PAGE NINE

67 5 0
                                    

                              🅿️9️⃣









_________________________📖 Waje suka samu suka zauna ta koya musu, suna gama wa samarin suka tafi ya rage ita da Farah, transfer tayi wa farahn sannan ta shiga kiran sunayya, ringing biyu kuwa ta ɗauka, da suari Deeyerh ta fara magana batare da ta jira ita tayi magana ba

"Haba yaya, haba yaya, ina ce tun da safe muka gama magana zaka turo min 10k in siya wannan gown ɗin amma shine har yanzu shiru baka min transfer ɗin ba".

Toshe bakin Farah tayi dan yadda Deeyerh ke magana zaka zata da gaske yayan ta kira, shiru sunayya tayi kamar ba zata ce komai ba kafin ta kashe wayar, dariya suka saka ganin ta kashe, da alama wannan ba za'a ci kuɗin ta ba.

Deeyerh bata bar ta haka ba ta sake danna mata kira, wannan karan kam se da ta kusa tsinkewa ta ɗauka da sallama, haƙuri Deeyerh ta shiga bata kan bata san ita ta kira ba yayan ta take ƙoƙarin kira,cikin yaƙe sunayya ta yi ƙuru

"Bakomai nima ai yar ki ce yanzu dai turo account number in tura miki 5k se ƴaƴan ya cika miki, am sorry nayi broke ne da duka zan baki".

"Kai haba dai Aunty sumayya ayi haka, to shikenan dai angode Allah ya saka da alkhairi bari na turo".

"Bakomai". Kawai sumayya ta iya cewa ta kashe wayar,

"Wallahi wannan ta san kanta ba kamar sauran ba".

"Oho ko dai yayane se ta turo ai bance ta so yayana ba, in tana da hankali daga yau ba zata kuma min maganar yaya ba".

"Ke kam Deeyerh ban san me yasa ba kya san haɗa su da yayan ki ba".

Wani kallo tayi Farah

"In haɗa su akan me, beside ahi baya ma San maganar su kuma nima ba zan so yi auri as low class and cheap ladies as wadannan ba wanda zasu ce suna san samari ba samari ne zasu ce suna son su ba, ke nifa.........".

Ringing ɗin wayar ta ne ya katse mata maganar da take yi, kyakkyawan murmushi ya wadaci fuskar ta ta dubi Farah

"Kin ga ɗan halal gashi nan ma yana kira, na tafi byee".

Ta faɗa tana miƙewa ta shiga tafiya batare da ta jira jin me Farah zata ce ba tana living call ɗin, ita ma Farah miƙe wa tayi ta tafi dan ta saba da halin Deeyerh in dai akan yayan ta ne tofa da ya kira bata wani jira.

"Ni nayi fushi".

"Haydar dake zaune cikin garden ya murmusa

"Am so sorry my Lilly though ban san laifi na ba".

"Bayan ma yau throughout ko kirana ba kayi ba".

"Oopps, wani assignment ne yasha kaina wallahi, bamu daɗe da yin submission ba".

"Shine ka manta da ƙanwar ka, kenan ma assignment ya fini".

"Haba ni na isa in ce, kina raina wunin yau ɗin gaba ɗaya, ban kira ba ne dan nasan kema zaki ce inje inyi kar in faɗi ko".

"Uhm".

Ta faɗa a hankali

"Am sorry to, ayi min afuwa Please ma".

Ɗan dariya kaɗan tayi shima ya ƙara murmusawa jin dariyar ta

"Are we good now?".

"Sure big b, kana ina?".

"Guess".

Shiru tayi ta shiga lissafa wa da hannun ta kafin ta canka

"Garden".

"Inye ta canka daidai".

"Will be there in a jiffy".

Ta faɗa tana kashe wayar ta shiga takawa heading to the garden, Zaune ta same shi shi kaɗai ba kamar kwana biyu ba da mutane ke yawan zama ba, idanun sa a lumshe yayi resting bayan shi jikin kujerar cement ɗin da alama yana jin daɗin yanayin iskar wajen.

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now