PAGE TWO

82 7 0
                                    

                               🅿️2️⃣












_________________________📖 "wane irin wulaƙanci ne ana ji mutum na sallama amma an kasa amsa shi se kace ba musulmi ne yayi receiving call ɗin ba, even if ba Musulmin bane ya kamata yayi magana ai".

Wata irin dariya ce ke cin ran Deeyerh, irin yadda mutumin ya taƙarƙare yana zuba faɗa ka ɗauka da ɗan sa ko ƙannen sa yake, gyaran murya ta ɗan yi dan Allah ya sani ba zata bada wayar nan ba se ta tsokani koma waye

"Haba mana Malam, wannan faɗa haka kamar wani babana, ya zaka kira ni kace dole se na kula ka, ni fa wallahi bana son takura".

Takaici da baƙin ciki ne ya cika zuciyar sa, daga Muryar ta yasan yarinya ce haka kuma ko rantsuwa yayi baze kaffara ba ya girme mata

"Will you shot up ko se ranki ya ɓaci, baki san takura me nake nema a wajen ki, if not because of my phone kin isa in kalle ki balle har in Kira ki ne".

"A'ah kaga dakata kar ka nemi ka zage ni, fisabilillahi yaushe kaga na ɗaukar maka waya da zaka ce saboda ita ka kira, wannan wayar tawa ce wallahi dan baba na ne ya siya min, kuma se Allah ya saka min da kake neman laƙa min sata".

Ta ƙarashe tana toshe bakin ta dan kar dariya ta suɓuce mata, wani shegen tsaki aka ja daga can ɓangaren kana aka kashe wayar, dariya ta shiga yi kamar wata sabon kamun hauka har su mama suka fito, tambayar ta suka shiga lafiya take dariya aikuwa take ta sanar da su abinda ke faruwa, girgiza kai Mama tayi dan wannan kaɗan ne cikin shika shikan tsokanar Deeyerh.

Compound ɗin su ta fita ta bawa Sale wayar da ta tsinta tare da 50k tace ya siyo mata irin ta, ba ɓata lokaci sale ya karɓa ya fita ita kuma ta koma.

Jira take a kuma kiran wayar dan har ta tsara me zata kuma yi sedai shiru an ƙi kiran, ajiye wayar tayi ta wuce dining inda su Harira ke jiran ta su ci abincin dare, tana zama Mama gaji da tafi Harira sanin favorite na Deeyerh ta shiga serving ɗin ta Chicken Mandi rice sai hadin salad a gefe sai shredded Beef hade da vegetable soup, bismilla tayi ta shiga cin abincin a nutse sedai kamar ko yaushe ba wani me yawa taci ba ta ture tare da kallon Mama gaji

"Mama abawa sale ragowar abincin nan maimakon jallof sphagetti ɗin ku kiji me zece, kai bakin sale yasan ta kan daɗi".

Dariya Mama da Harira suka yi dan gaskiya ta faɗa, sale akwai son daɗi shiyasa da suna Abuja yafi kowa sanin manya manyan suya spot da restaurants, hatta da icecream yasan wane flavor ne yafi daɗi da ƙamshi.

Suna cikin maganar kuwa se gashi, dariya Deeyerh tayi tana kallon shi

"Abincina na rage maka sale shine Mama tace a'a zaka fi son dai jallof taliyar da tayi muku shine nace to Harira ta cinye kawai".

Zaro ido yayi yana kallon Mama nan da nan fuskar sa ta marairaice Muryar sa ta fara rawa

"Haba gaji, haba dan Allah, fisabilillahi yaushe na taɓa ce miki ina son taliya, ke Kuma Harira banda halin ɗan Adam ai kin san ni ba ma abincin da bana so kamar taliya kawai dai ina daure wa ina ci ne amma shine kika buɗe baki kika cinye abincin, ai shikenan se ki tashi ki miƙo min taliyar".

Dariya suka fashe da ita su duka ukun ganin yadda sale ya koma wani kalar tausayi har idon sa na neman kawo ƙwalla, sale ba dai son daɗi ba.

Tashi Harira tayi ta wuce kitchen ta ɗauko foodflask ɗin sa ta miƙa masa, warcewa yayi a zafafe dan fa yaji haushin cinye kayan daɗin da tayi ga kuma dariyar da suke masa, har ya juya ze fita Deeyerh ta dakatar dashi

"Ina saƙo na, ko kuwa nima halin ɗan Adam ɗin zaka min kamar yadda Harira tayi maka".

Itama se da ta sami rabon harara a kaikaice wajen sale ganin har da ita a tsokanar sa, ciki ciki ya bata amsa yana fita

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now