PAGE THREE

87 6 0
                                    

                              🅿️3️⃣














                                 3️⃣











_________________________📖 Duk yadda gaban ta yake faɗuwa saboda fargaba da tsoro bata nuna ba a kan fuskar ta ta dake sosai.

Takowa suka yi zuwa inda take tare da mata sallama bayan sun kashe wayar, kannewa tayi ta amsa a nutse kamar ba ita ba ta cigaba da kallon su dan jin me zasu ce.

"Mune wanda kika yi waya dasu zasu karɓi waya".

Ɗan kaɗa kai tayi kafin tace "oh nagane". Tare da kallon su kaɗan

"Amma dai kun san ba zan baku wayar nan haka kawai ba se kun tabbatar mun da taku ce".

Ɗan murmushi me kaftin ɗin yayi saboda abinda ta faɗa

"Haba ƙanwa ta, yanzu ke kin ga mun yi kama da marasa gaskiya?".

Kau da kai gefe Deeyerh tayi

"Kayi haƙuri yayana amma ba'a goshi ake rubuta gaskiya ko akasin ta ba bare na gane".

Zuwa wannan lokacin tuni ransa ya daɗe da ɓaci dan har wani ɗaci ɗaci yake ji a bakin sa

"Ke ki shiga hankalin ki fa, ya zaki tsaya kina ɓatawa mutane lokaci da wani raunin hankalin ki, in ba wayar mu bace ina muka samu number har muka kira".

Duk da ta tsorata da yanayin sa amma ba hakan ya hana ta bashi amsa ba

"Fisabilillah me ye laifina, ai dai ba ƙarya nayi ba ana irin haka, ni ba ruwana da wani kyan ka ehe kawai ka faɗi shedar waya taku ce se in baku in ba haka ba se dai ku haƙura".

Ba ƙaramin dariya ce ta ciyo Jameel ba ganij yadda mutumin nasa ke faman ƙanƙance ido da alama yau ya samu daidai dashi, da sauri ya haɗiye dariyar sa ganin yadda Haydar ya zabura yayi kan ƴar mutane, cikin firgicin yanayin mutumin ta ja baya da sauri tare da miƙa musu wayar baki na rawa tana faɗin

"Ga wayar ku nan Allah ya sani tsokanar ku nake, amma kuyi haƙuri dan Allah kar ka dake ni".

Warce wayar Haydar yayi fuuy yayi gaba kamar wanda ze tashi sama yayinda Jameel ya duƙe wajen yana dariya biyu, dariyar yadda yarinyar ta ƙular da Haydar da dariyar yadda lokaci ɗaya ta firgice dan har yanzu da ya bar wajen hannun ta na dafe da ƙirjin ta tana numfarfashi tare da zare ido kamar shege a rabon gado, seda yayi ta ishe shi kafin ta miƙe tsaye yana murmushi

"Amma ƙanwar mu kin iya tsokana sedai ashe matsoraciya ce".

Harara Deeyerh ta maka masa ta figi jakar ta tayi gaba a ranta tana godewa Allah da yasa mutumin be dake ta ba.

Gefe ta samu ta tsaya tare da kiran Sale, ba'a daɗe ba ya ƙaraso har cikin makaranta ta shige suka tafi gida, duk yadda yake mata hira bata maida hankali kan shi ba, ba abinda take tunawa se irin yadda ya zaburo kamar ze dake ta ko se haɗiye ta.

Suna shiga gida ta manta da abinda ya faru ta shiga bawa su gaji labarin malamin su me what da what.

"Ina faɗa miki Harira mutumin nan se ya faɗi what a sentence fiyeda so goma, ji kike yana okay class our topic for today is what, input system, so the in input system is what, but what is input system, so who can tell us what is what, input system......, Ire iren haka fa wallahi se yayi fiye da nawa dan ma ni ban iya ba, yau nidai se da yasa cikina ya kusa ƙullewa".

Daga mama har Harira dariya suke dan yadda take kwatanta abinda malamin keyi dole ya baka dariya, ranar har ta kwanta bata da hira kamar ta malam me but what.

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now