PAGE TWENTY

170 11 3
                                    

                              🅿️2️⃣0️⃣

*FINALE* 🤸🤸🤸

🔚🔚🔚🔚🔚.

___________________________📖 Wanka tayi ta shirya cikin gajeran wandon da ya wuce cinya sedai be ƙarasa gwiwa ba se crazy top ta gyara fuskar ta tas tare da raba gashin ta gida huɗu ta kakkama da ribbons masu kyau da ado ta ɗebi abincin sa takai falon sa ta jera shi cikin tsari me kyau da ɗaukar hankali ta bayan ta gama gyara falo da bedroom ɗin komai yayi tsaf gwanin burgewa da ban sha'awa.

Tun a bakin ƙofar falo ta tare shi tare da amsar jakar hannun sa, duk yadda ta wuni da ƙwarin gwiwa yanzu se taji duk babu ya gudu ya bar ta tsurar ta sabida yadda fuskar sa take babu ko ɗigon fara'a.

Dake wa tayi ta raka shi har ɗaki tare da haɗa masa ruwan wanka, kayan da ze saka ta Fito masa dashi sannan ta fita, ɗaki ta koma da sauri tana kai kawo cikin shirya kalaman da zata yi amfani dasu wajen bashi haƙuri, se da taga dai lokaci na wuce wa ta maza ta koma.

Zaune kan carpet ta taddashi da laptop Yana aiki, be ɗago ya kalle ta ba har ta ƙarasa tayi serving ɗin sa abinci ta ajiye a gaban sa ta koma gefe ta zauna sannan ya ja abincin ya shiga ci at the same time yana danne dannen sa.

Se da ya gama aikin sa kafin ya tattara ya koma bedroom, gyara wajen da ya ɓata tayi ta kwashe kayan abincin ta wuce nata bedroom ɗin ta tayi wanka ta canja kaya zuwa na bacci sannan ta koma nashi abinda bata taɓa yi ba tsawon wata ɗaya da auren nasu.

Ɗagowa yayi ya ɗan kalle ta na ƴan mintuna a kau da kai ya cigaba da addu'ar baccin da yake yi dan yau be dawo da wuri ba se after 9 gashi Kuma gobe da wuri yake son fita saboda akwai inda zasu je da mai girma minister.

Tsaye tayi tana lanƙwasa yatsun hannunta dan ta rasa ta ina zata fara, hasken ɗakin da ya kashe yasa ta ankara ta shiga magana a hankali

"Tun kwana uku baya nake ta binka ina baka haƙuri duk da ban yi wani laifi ba amma kana share ni, meye laifi na fisabilillah akan abinda ya faru, duk dena cin abinci na da kayi na sati ɗaya da kwanaki ban ce komai ba se dan na samo mafita kuma kaji haushi na, ni dama tun farko abinda yasa na ƙi yarda da auren ka kenan dan nasan ba zaka iya adalci tsakanina da matar ka da kake matuƙar so ba, ita da tayi laifi kawai ɗakin ka ka hane ta shiga amma ni da ban yi komai ba kana fushi dani, tun farko abinda na hango na ke Kuma gudu kenan amma su Maah suka ƙi fahimta ta, shikenan kayi haƙuri kuma ba zan kuma zuwa kusa da kai ba dan na fahimci hakan ne baka so".

Ta faɗa tana share hawaye dan Allah ya sani ta ji haushi, juya tayi wajen ƙafa zata fita sedai dole ta tsaya jin yadda ya ruƙunƙume ta a jikin sa, zuciyar ta taji ya karya hawaye suka shiga tsere akan fuskar ta, bata ce komai ba har ya gaji da riƙon ya sake ta ya kuma yin gaba, hannun ta ya riƙo da sauri yana canja mata direction towards gadon sa, bakin gadon ta zauna ta cigaba da share hawayen ta tana jan hanci.

Haske ya kunna ya dawo ya zauna gefen ta tare da ruƙo hannun ta ta ƙwace ta shiga goge fuskar ta, gaba dayan ya janyo cikin jikin sa ya cire mata hannuwan ta ya shiga share mata hawayen da nasa hannun sedai kukan yaƙi tsayawa kamar wanda ake tunkuɗo hawayen, tsayin lokaci kafin ta samu ta tsayar da su sannan ta fara son janye wa daga jikin sa sedai ya Sa'a hannun sa ya zagaye ta

"Ka sake ni zan je in kwanta".

"A'ah anan zaki kwana".

"Nikam ɗaki na nake so".

"Ni kuma nace a nan zaki kwanta, period".

"Cikin nuna fifikon har da fin ƙarfi?".

Ɗan tsam yayi kafin ya sake ta ya sauka a gadon kafin ta ankara tuni ya ɗaga ta kamar wata ƙaramar yarinya har bedroom ɗin ta ya kwantar da ita kan bed Shima ya bita tare da danna switch ɗin da ke kan side drawer ya kashe hasken.

Has llegado al final de las partes publicadas.

⏰ Última actualización: Sep 26, 2022 ⏰

¡Añade esta historia a tu biblioteca para recibir notificaciones sobre nuevas partes!

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora