🅿️🔟
_________________________📖 Tun da aka yi hutu shikenan bata da wajen zuwa da ya wuce gidan Umma wadda take zuwa bisa yarjewar Maah bayan ta kira Umman ta faɗa mata zata dinga zuwa dan su dinga karatu da Haydar na wajen da aka wuwwuce ta dan seda aka fara lectures da sati Uku ta fara zuwa.
Wannan ya daɗa ƙara musu shaƙuwa sosai, sati ɗaya da yin hutu suka tattara suka tafi Abuja main house hutu ita dasu Mama gaji, mai gadi kaɗai aka bari.
Babban gida ne da tunda ga gate ɗin sa zaka san me gidan ba ƙaramin attajiri bane, Alh Sulaiman sanannen ɗan kasuwa ne a Nigeria haka kuma shine ministan noma na yanzu wanda tsabar yadda ya Companies ɗin shi suka ƙware a noman zamani yasa aka bashi wannan muƙamin.
Gidan Alh Sulaiman babban gida ne me ɗauke da ɓangarori har biyar, ɓangaren farko na me gidan ne wato shi Alh Sulaiman ɗin, na gefen sa kuma na Maah ne se na bayan sa dake da ɗan tazara na ma'aikata mata, ɓangaren ma'aikata maza dake can kusan ƙarshen katanga se ɓangaren Haydar dake gefe daban wanda Maah ta sa a ka kulle tace se yayi aure ze shiga dan ba zata lamunci yana wani waje daban ita ma na wani waje ba dan sa ido akan tarbiyyar sa.
Ɗakin ta da yake next to na Maah a upstairs ta sauka, tas yake a gyare se tashin ƙamshi yake dan Maah da kanta ta zage ta gyara ko ina saboda gudar ƴar tata taji daɗi.
Bacci tasha wanda se da ta tashi sannan ta ƙarasa wajen Papi dan baya nan da suka ƙara so, abinci Maah ta tsara ta se da taci sosai kafin ta bar ta ta koma ɗaki dan ta ce bata gama huce gajiya ba.
Wayar ta ta jawo cikin duba ko Haydar ya kirata sedai ƙwalam though sun yi waya so uku da suna hanya na ƙarshe shine yace ze Kira yaji ya suka sauka.
Tura baki tayi gaba ta shiga ƙunƙuni ƙasa ƙasa tare da tasa wayar a gaba dan kar ya kira bata kusa sedai fiye da mintuna talatin tana zaune be kira ba.
Agogo ta duba cikin son ganin lokaci, awa biyar da saukar su amma ace be kira ba ai fisabilillah be mata adalci ba.
Ringing ɗin da wayar ta fara yasa ta duban ta da suari cikin sauke ajiyar zuciya sedai maimakon sunan sa sunan mamy ta gani, wani dam taji a ranta amma ta daure ta ɗauka.
Ban gajiya da ya hanya tayi mata suka ɗan taɓa hira ta kashe, almost an hour suka yi spending on the phone Amma duk da haka bata ga kiran sa ba, ƙwafa tayi kana ta kira Umma ta sanar mata sun sauka lafiya, fatan huce gajiya ta mata suka yi sallama.
Ajiye wayar tayi kan mirror ta wuce ta sake wanka tare da saka kaya marasa nauyi ta sauka wajen su Maah dan zaman nan ɗin ba abinda yake ƙara mata ban da takaici da damuwa.
Yau hirar ma sama sama akayi da ita yawanci sedai tayi ta yaƙe, duk labaran da ta ƙunso dan bawa Maah se ta neme su ta rasa se zallar damuwa da ta cika mata rai, tuni Maah ta gano akwai abinda ke damun ƴar tata sedai ko da ta tambaya se ta e mata ba komai gajiya ce kawai gashi kuma ta kasa bacci.
Bata ja ba ta bar shi a hakan duk da ranta na bata ba haka bane, seda tayi sallar magrib sannan ta koma ɗaki dan gujewa idanun Maah da ta sa mata take Binta dasu duk inda ta yi.
Kamar wadda ake jira ta shiga wayar ta dake ajiye kan mirror ta ɗau ringing, a hankali ta taka zuwa wajen tare da duban wayar, ganin sunan sa kan screen yasa ɓacin ranta ya ƙaru, wato ma se yanzu ya tuna da ita kenan.
Tana riƙe da ita a hannun ta har ta ƙaraci ringing ɗin ta ta ɗauke amma bata iya ta ɗauka ba, miss call huɗu sannan ya haƙura da kiran, karatun Alkur'ani ta kunna ta saka Bluetooth tana saurare har taji ranta ya ɗan yi mata sanyi ta shiga bi a hankali, kiran sallar isha da ta wayar ta shiga yi saboda ta saita al-moazin dake kiran sallah duk in lokaci yayi yana ata miƙe ta zura hijab ɗin ta dan tana da alwala.
YOU ARE READING
ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅
RomanceA friendship-love story..........kudai ku biyo Ouummey through the journey, promise you'll enjoy it to the fullest!!!