PAGE SIX

73 5 0
                                    

                               🅿️6️⃣


inkinsan bazaki dingayin sharhi/comment me ma'ana ba kada kimin magana👌 ba sticker da godiya nakeso ba✖ addu'a da sharhi/comments masu ma'ana nakeso✔ inkin shirya shiga group dina ki min magana ta wannan number, 09013101854





_________________________📖 Yau kam se da su mama gaji suka gaji da jin labarin gidan su yaya friends kamar yadda ta raɗa masa, seda ta gama labarin ta kafin Mama gaji ta shiga yi mata faɗa cikin taushi murya kan tafiyar da tayi wani waje batare da sanin su ko Maah ba, haƙuri ta basu dan tuni ta aminta tayi kuskure tun lokacin da umma ta ankarar da ita.

Weekend gaba ɗaya haka tayi spending ɗin su wajen kallon fina finan ɗan Ibro tana cin dariya tun bare ma ƙarangiya, sosai kuma suka zaga gari zuwa wajen shaƙatawa tare da su mama gaji bayan ta sanar da Maah da Papi, kuɗi Papi ya turo musu  purposely sabida su siya abinda suke so a fitar, ranar se da suka ci dinner Sannan suka waiwayi gida bayan an yi wa maigadi na shi takeaway ɗin shima.

Ran Monday kuwa har Allah Allah take taje makaranta dan taga in ya karɓi wayar, ranar da kanta ta tashi batare da mama tayi fama ba kamar kullum.

Ƙarfe bakwai da mintuna ta bar gida dan lecture ƙarfe takwas ce da su, har gaban hall ɗin da zasu yi lecture ya kai ta dan da ɗan nisa kuma ba sanin wajen tayi ba.

Gaba ɗaya ta tattara hankalin ta ta maida kan malamar dake musu bayani kan software managing sedai tun ba'a kai ko ina ba hankalin ta ya bar kan karatun da malamar take yi ya koma kan irin shigar da ke jikin ta.

Fuskar malamar kamar an yi ɓarin mai se maiƙo take yi gata kuma haƙa, kayan jikin ta kuwa atamfa ce me ruwan bula da ruwan ɗorawa mayafin ta kuma Ash color ne, takalmin ta baƙi jakar ta dake ajiye gefe kuma ruwan bula.

Duk yadda takai ga so ta danne dariyar ta seda ta fito kuma uncontrollably, tsit ajin yayi kamar ba kowa acikin se ita kaɗai suna binta da kallo, jin yawon idanun ta yasa ta tsayar da dariyar da ƙyar tana bin kowa da kallo cikin zare ido, se lokacin ta lura da hankalin kowa ya dawo kanta ne hatta ko da malamar dan ta bar bayanin da take ta koma gefe tareda zuba mata ido.

Sunkuyar da kai tayi ƙirjin ta na duka cikin fatan Allah yasa kar malamar ta dake ta dan taji ance makarantun Nigeria duka ake yi in ɗalibi yayi ba daidai ba.

Gyaran murya malamar tayi kafin ta shiga tambayar ta abinda take wa dariya, rasa me zata ce mata yasa kawai ta shiga Binta da kallo kafin ta fara bata haƙuri, tsaki kawai malamar tayi ta juya ta cigaba da abinda take yi, tun daga lokacin kuwa tayi duk yadda zata yi ta maida hankali kan karatun duk da ba wani fahimta take ba dan an yi bayanai sosai lokacin da take aikin ƙare wa shigar Malama kallo.

Ana gama wa ta ja jakar ta tayi waje inda da yawa ƴan class ɗin suka bita da kallo, wasu na yaba kyan ta wasu kuwa tsarin shigar ta ne yayi musu wasu kuma mamakin dariyar da tayi ne be bar su ba.

Guri ta zauna tare da nutsuwa ta shiga bin karatun a hankali a hankali, cikin ikon Allah se gashi tana fahimta dan fa dama ba wai bata da ƙoƙari bane, kawai dai karatun ne bata so.

Se da lokacin shiga next class yahi ta tashi tana rufe littafin ta maida jakar ta ta shiga tafiya hankalin ta kwance dan tasan theatre ɗin kasancewar tun ranar farko suka yi lecture a can, twins theatre ce, a wannan karon kam malamin kasa daurewa yayi seda ya kori Deeyerh saboda yadda bata maida hankali haka kuma se uban surutu take yi da besan da wa take yi ba dan ba kowa a kusa da ita, abinda be sani ba da Papi take waya kuma Bluetooth ne a kunne ta, gaba ɗaya malamin be iya koyar wa ba dan kansa kawai yake wa bayani, tun da yasa board a gaba ya shiga rubutu yana karantawa wai haka bayani yake yi shiyasa kawai ta kira Papin ga suka shiga hira a bin su.

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now