PAGE SEVENTEEN

64 7 0
                                    

                            🅿️1️⃣7️⃣





__________________________📖 Kuka ta saki uncontrollably har nunfashin ta na ɗauke wa saboda tashin hankali, shikenan yanzu ta zama mallakin Ashraf bashi ba, shikenan sun haramta ga juna duk ɗumbin son da take masa, se yanzu ta sake tabbatar da har ila yau ba kowa a zuciya da ruhin ta face Haydar, shi ta fara so, akan sa ta soma ɗanɗana raɗaɗin so haka kuma har yanzu ba wai ta dena son nasa bane sedai bata san me yasa zuciyar ta tunzura ta aikata abinda ta fara nadama tun yanzu ba wato auren Ashraf sedai aikin gama ya riga da ya gama se dai haƙuri.

Ƙwanƙwasa ƙofar mamy ta shiga yi tare da kiran sunan ta dan ta fito ayi hotuna sedai tayi fumfurunfus dan ko san ganin angon bata yi, da a san ranta ne da tace komai da ya faru ya zama mafarki sedai bata da wannan ikon.

Haka dole mamy ta ƙyale ta ta koma wajen su Maah aka cigaba da sha'ani, ƙarfe bakwai bayan an sakko daga sallar magrib ƴan ɗaukan amarya suka zo, mota uku ne sedai lafiyayyu ne masu kyau da tsada, a lokacin ne kuma Maah ta tursasa ta buɗe ƙofar ɗakin, sosai hankalin Maah ya so tashi ganin yadda idanun ta suka koma saboda kuka se kuma ta bar shi as kukan da kowace ƴa mace ke yi ne na fargabar sabuwar rayuwa da kuma barin gida, wanka ta sata ta sake yi sannan ta taya ta shiryawa cikin wani shaking materials tare da naɗe ta cikin lafaya me matuƙar kyau da walwali sannan ta riƙe hannun ta zuwa side ɗin Papi.

Su uku suka tadda a ɗakin, Papi, mamy se yaya Aliyu, zaunar da ita Maah tayi gefen ƙafar Papi kafin itama ta kai zaune kusa da mamy.

Nasiha sosai Papi yayi mata da ta sata sake sabunta kukan ta, mamy na haka ta daure tayi mata tata nasihar se yaya Aliyu, Maah kuwa ta wa mamy kara bata ce komai ba tun bare ma da ta ji duk sun faɗi duk abinda ya kamata.

Yaya Aliyu ne ya riƙo hannun ta har cikin mota sedai kuma ta kafe ba zata shiga ba se an kawo nata Akash, seda Umma tayi mata jan ido kan za'a kawo shi a week after yanzu sannan ta haƙura ta shiga, share hawaye Maah tayi cike da kewar ƴar ta ta shige gida da sauri.

Gaban motar da ya saka ta ya buɗe ya shiga dan shine ze Kai ta har ɗakin ta ragowar motoci suka rufa masa baya.

Flat ne me matuƙar kyau kamar a Turai, tsarin ginin gidan ba ƙaramin tafiya yayi da mutanen da suka je kai ta ba, kowa se santi yake da kuran ta side ɗin nata dan side uku ne, ƙaramin side daga can gefe kaɗan se biyun daf da juna inda babban falo ya haɗa su a tsakiya yayinda gaban su ma wani ƙaramin flat ne me one bedroom da ƙaramin falo shima a haɗe yake da ragowar biyun ta babban falo.

Sabuwar nasiha yaya Aliyu ya sake mata tare da ajiye mata medium bag me ɗauke da pray mat, tasbaha da Alkur'ani inji Papi se wasu littattafai masu ɗan yawa a cikin wrapper inji Maah, rungume shi tayi tana kukan kar ya tafi dan seda ƙyar ya zame jikin sa ya fita yana sharar hawaye, ƙarfe tara mamy ta tattara kan jama'a aka tafi aka bar amarya bayan an sake gyara mata part ɗin ya ɗau ƙamshi sosai.

Kwanciya tayi da kayan jikin ta bayan ta cire lafayar dan bata jin ƙarfin jikin da zata iya yin wanka, ta daɗe kwance a ɗakin tana bitar rayuwar ta tun daga tasowar ta kawo yanzu kafin bacci ya sace ta batare da taji ɗuriyar ango Ashraf ba.

Kiran sallah da aka kira ya sa ta farka dan masallacin a bayan gidan yake, alwala tayi ta gabatar da sallah bayan tayi wanka sannan ta ɗora da karatun Alkur'ani har gari yayi haske kafin ta sake komawa bacci.

Se ƙarfe goma ta farka ta tashi ta sake wanka ta ɗan yi kwalliya dan tasan zuwa anjima kaɗan zata fara yin baƙi, bedroom ɗin ta gyara tare da wanke bathroom ta Fito ta ɗaya bedroom ɗin , addu'a ta shiga yiwa Papi ganin irin uwar dukiyar da ya narka mata, fita tayi ta shiga next dan bedroom uku ne a each side, nan kam falo aka maida mata shi tun da babu se na haɗa ka shine aka yi mata jeren falo a nan, royal seat ne ƴan uban su masu matuƙar kyau da kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da tsadar su, milk and coffee haka ma set ɗin curtains ɗin se Centre table mahaɗin kujerun se dining a can gefe da kuma glasses ɗin turarukan ta, hatta wallpaper ɗakin seda aka canja mata zuwa kalar kayan ta, bata san tana hawaye ba se da taji ɗumin su kan kuncin ta, ba hawayen komai bane se na so da ƙaunar iyayen ta nan ta shiga yi musu addu'a a ranta kan Allah ya saka musu da alkhairi.

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Where stories live. Discover now