PAGE ELEVEN

52 5 0
                                    

                             🅿️1️⃣1️⃣








_______________________📖 Kwanan ta biyu tana hutawa a gida kafin ta koma school, ranar kam purposely sabida ita ya shiga makarantar dan ba abinda ze shiga yi dan tun da aka koma yaje ya karɓi project topic ɗin shi.

Ranar wuni guda bata shiga lectures ba saboda ba wani kankama tayi ba kasancewar ba kowa ne ya koma hutu ba daga malaman har ɗaliban.

Hira suka sha kamar basa waya kullum wanda a ƙa'ida ne basa waya ƙasa da so huɗu each day banda kuma watsapp da yanzu ƙarfi da yaji ta zama regular saboda chat dashi da kuma vedio call.

Se fice sale ya dawo ya ɗauke ta suka tafi, kwanan kam su Mama gaji kasa gane kanta suke dan ta auri zaman ɗaki kamar wata sabuwar amarya sedai ko da suka faɗawa Maah ta kira ta tayi mata magana se tace karatu take zama yi dan in tana cikin su bata samun daman concentrating yadda ya kamata saboda hira.

Da wannan ta rufe bakin Maah ta bar maganar, eh tana karatu sosai amma mafi yawan lokutan da take zaman ɗakin tana spending ne wajen waya da Haydar da ta gama yarda ta aminta ta sallama wa ranta da zuciyar ta tana matuƙar so haka shima yana mata so kwatankwacin wanda take masa ko ma fiye.

A sati na uku da komawar ta school ne baya samun dama sosai da ita saboda research da ya sa gaba sedai waya kam ba abinda ya ragu se ma ƙaruwa da tayi, duk ya sami space ko ita ta sami interval to cikin waya suke.

Cikin wannan yanayin rayuwa ta cigaba da tafiya har suka cinye wata biyu a second semester dan har sun fara tests sabida exam dake approaching, a lokacin haka yake squeezing time ya shigo school su yi karatu duk da kam alhamdulillah tana ganewa da kanta haka kuma da result na first semester ya fito tana da 3.59 Cgpa, ba ƙaramin murna Maah tayi ba a lokacin, Papi kuwa ba'a magana dan latest motar da ta fito ya siya mata yace as gift amma se ta dawo gida zata yi amfani dashi.

Haydar kam Papi takanas Shima ya karɓi number sa ya kira shi yayi masa godiya har abin ya dinga bashi mamaki ganin yadda iyayen ta ke murna kan nasarar da ta samu as if Basu da wani ɗan bayan ita.

San da bashi da lokacin zuwa school kuwa har gidan umma take zuwa ta jira shi in ya dawo suka gama se ya rakata gida, wani sa'in kuma shi yake zuwa can gidan su.

A kwana a tashi ba wuya wajen ubangiji, cikin nasara da taimakon Ubangiji suka kammala second semester cike da fata da burin samun result ɗin da yafi na farko dan ta san karatu da mai da hankalin da tayi a wannan karon ko kusa ko alama ba za'a a haɗa shi dana baya ba dan ya ninka previous effort ɗin ta kusan da ninki uku, satin su ɗaya da gama exam Haydar yayi submitting project ɗin shi cikin fatan samun Nasara dan in har komai ya tafi yadda ake fata daga wannan matakin se kuma tafiya service.

A ɓangaren shaƙuwa kam abin nasu har ya fara bawa Umma tsoro dan ko da suka gama exam haka kawai se yi wanka yayi wa Umma sallama yace ya tafi wajen Deeyerh in Kuma shi be je ba ita zata ɗauko ƙafa ta taho gidan, bata sami sauƙi ba seda Deeyerh ta tafi Abuja, sosai Papi da Maah har ma da yaya Aliyu suka tare ta cike da farin ciki, kwanan ta biyu da komawa suka tafi Umrah gaba ɗayan su, ko da ta kira Haydar da number ɗin ta ta can Saudiyya sosai yayi mamaki dan shi be da wani da se Kira shi daga ƙasar Saudiyya amma dai ya daure ya ɗauka.

Ba ƙaramin kiɗimewa yayi ba jin Muryar ta, cikin dukan tara tara da ƙirjin sa ke masa ya shiga tambayar ta ya akayi taje Saudiyya, kamar baya wannan karon ma bata faɗa masa gaskiya ba dan gudun kar yace za bar ta,

"Tare da mamy da Papa muka tafi".

That was the reply she gave him, a lokacin yadda tayi sounding se yaji kamar akwai abinda take ɓoye masa, ya daɗe shiru kafin ya mata fatan alkhairi ya kashe wayar ya bar ta riƙe da waya a kunne baki buɗe saboda mamaki, from that very day ya fara behaving mata somehow da ta kasa ganewa, bashi yake kiran ta ba dan ta san akwai tsada sosai calling from Nigeria to an international countries so bata taɓa damuwa ba dan be kira ta ba sedai kuma nata kiran ma se yayi ta bada excuses din da ze kashe wayar da sun gama gaisawa, tun abin baya samun ta har ya fara, daga ƙarshe dai da ta lura in ta biye masa ba zata samu damar gabatar da ibadar ta yadda ya kamata ba se ta ƙyale shi kawai ta dena kira ta maida hankali kan abinda ya kawo su.

ABOTA CE KO SOYAYYA??? ✅Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora