6

228 31 2
                                    

LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

_♡ The Love circle._

06.
G.w.a.

Lokaci guda Masarautar hadejiya yay mummunan dauka da rubibin jin labarin dawowar yerima sujamal a garesu lungu da saƙo yau zancen kenan dake wakana tsakanin dumbin jama'ar dake cikin fadar masarautar hadejiya.

wasu a fassarar su cewa suke lokci ne yay da zasu kalli fuskar asalin magajin masarautar garinsu domin kuwa kusan burin kowane dan adam ne a hadejia daya san kamannin yerima sujamal wanda suka dade sunajin sunansa suke kuma kwana da mararin ganin kamnin fuskansa,dan bayan nan kuma basusan komi akanshi ba,wasu kuma aganinsu da wuyane sujamal ya mance da tsohon tarihin yadda aka salwantar da rayuwar mahaifyarshi bare har yaji sha'awar tako kafafunsa cikin wnn masarauta ta hadejia tareda sanin gimbiya hajja shashe wacce ita tayi sanadiyar faruwar komi tana atare dasu haryanzu,aganinsu gidansa da ake magana kawai shine "Beitul keiser",amma ba cikin masarautar hadejiya ba.

tunda mai martaba yay wann sanarwan ake ta muhawwara da harsashe kala kala tsakanin yuwar xaman sujamal acikin baitul keiser da yuwar dawowarsa cikin masarautar hadejiya wanda harynzu babu wani wanda yakeda masaniya akan dede.

Wannan muhawwara ce wanda kusan kowa yakeyi a fili wasu kuma acikin zukatan su domin neman gamsashun amsa da haske akan lamarin mulkin masarautarsu ta nan gaba.

Shekaru masu yawa sunja mai martaba sarki Abdlsamad saiful islam khaleefa yana shirin cika shekaru sittin da shida 66yrs a duniya wanda da wuyane aganinsu ya kara wasu shekaru masu yawa batare dayay murabus akan kujerarsa ba ya bawa dansa sujamal ragamar masarautar ba.

Kowadai makoman kujeran mulkin nan shine agabansa,shine kuma damuwarsa,sabda aynxu masarautar ta kasance cikin masarautu masu tsananin karfin mulki da hukunci babu bata wani lokci,sabida jinin iko da mulki dake yawo ajinin King abdlsamad saiful islam khaleefa kasancewar sa sarki mai zafi wanda baida sauki gurin daedeton kowani mahaluki akansa,duba da shikansa maimartaba king Abdlsamad saiful islam khaleefa tun yana da karancin shekaru ya soma mulkansu bayan mutuwar mahaifinsa saiful islam khaleefa wnda hakan ne yasa ake harsashen yuwar komawar mulkin izuwa kan dansa yerima sujamal acikin dan kankanin lokaci.

Daga lokcin da sarki yay sanarwan har ixuwa yanxu kusan dukkanin hankula da harsashen mutanen dake ciki da wajen masarautar duka naga kan lamarin dawowar sujamal ne.

A fannin hajja shashe kuwa yau tamkar wata ranar tashin hankaline wanda ba a sakamai rana dan kuwa zuciyarta bakaramin bugawa yay dajin labarin dawowar sujamal ba.

Cikin matsanancin tashin hankli da kaikawo mai tattare da bakinciki ta dafe zuciyarta datakeji yanai mata wani irin zogi da ciwo, kanta takeji naci da wuta kamar wanda zai kone tsabar tunani.

Itakanta harsashe take famanyi akan lamarin dawowar sujamal wanda tsawon shekarunan kusan da shi take kwana da shi kuma take tashi, babbann burinta akansa ayanxu bai wuce ta dau mummunan fansa akansa ba,domin kuwa ta jima tana rayuwa cikin bakinciki dominsu shida mahaifiyarsa Bahriyal Abeeda,wanda a silar mutuwartata ce yajawo ta cika karo da bakinjini da kuma karshen duk wani martaba da jin dadin rayuwarta a idon mijinta Mai martaba Abdlsamad khaleefa.

Juyowa tay ta sake tsayawa cak tareda sakin wata sihirtaccen ajiyar zuciya a karo na uku zuciyarta na matsanancin halbawa
Batare da ta dago kanta ba murya a karye tace
Tabbas! Wann sanarwan ya matukar girgiza zuciyata sabida saqone na bakinciki wanda da wani baiwace ta kawo matashi da abakacin farincikin rayuwarta ne.

Kanta bisa sama tanamai kure bango da wani irin nutsatsiyar kallo"tambayar kanta tayi cikin zuciyarta tana cewa shin ynzun wani sabuwar lokacine na bakinciki da kuncin rayuwa agareta da yazo wanda har za'ay zancen kawo musu dan kishiyarta sujamal cikin masarautar hadejia domin ya mulketa?mai martaba dakansa yay sanarwa Hakan yana nufin kenan har lokaci yay kusa da dan Abeeda zaizo yazama sarki kuma magajin masarautarsu.

LAMARIN GOBE.Where stories live. Discover now