8

234 29 0
                                    

LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

_♡ The Love circle._

#SURAYYAHMS

08.

Babban masallaci ne mai dauƙe da kayatattacun daddumai masu kyau da tsafta golden nd red in colour na sarauta,masjid ne wanda aka tanadar acikin tsakiyar beitul keiser wanda sarki tareda jama'arsa ta cikin wajen ke sauke duk wata sallolin farillai,sallolin jumu'a da kuma sallahn idi.

yau daya kasance musu tamkar wata rana ta musamman makil aka cike cikin masallacin da jama'ar dake cikin fadan beitul keiser,duk wani hakimin sarki da nakusa dashi duk sun hallara ayau domin su taya sarki farincikin kasancewarsa tareda dansa sujamal bayan shekaru 18 da tafiyansa yawon neman ilimi a kasashen waje.

Yau Bakaramin shiru masallacin ya dauka ba.

Daɗɗadar sautin muryan babban limaminsu wato waiz,sheik mubarak ibn Azad shiya karade ilahirin cikin masallacin da zazzkar sautin kira'arsa ayayin da yake karanta suratul taubah acikin nitsuwa.

Sujamal na tsaye agefe kusa da mahaifinsa a sahun farko suna sallahn tare har aka kammala sallahn magrib akayi na ishai inda kusan kowa ya xauna wajen zamansa a nitse ana faman addu'oi.

Kusan dokace ta cikin masarautar babu wani mahaluki da ya isa yay surutu ko wani magana na daban acikin kwaryan masallaci musamman ma in maganar tashi bata shafi addini ba.

Duk son jama'ar sa da su gaisa da dansa sujamal yau haka suka hakura harsaida aka kammala duk abunda za'ayi acikin masjid aka samu fitowa
zuwa ainihin cikin fadar sarki aka xazzauna.

Nan ma gaisuwar da yay aka kumayi masa bai wani dade ba mahaifin sa ya bada umarnin a kyaleshi yaje sashen domin ya ci abincinshi ya kuma huta sabida gajiyar hanya daya debo ajikinsa.

****

Zaune yake a lafiyyan falonsa dake sashensa idanuwansa a lumshe kwata kwata bayan hot coffee dayasha da zu har lokacin baici komaiba duk dama har ankawo masa abinci kala kala daga kicin din sashen aslinsa anjere masa shi agabansa wanda dama an shaidesa,inhar yana cikin baitul keiser toh bayacin abincin kowane kicin saina sashen sister suzan.

Yau tare da marida suka shigo,sister susan ta saka kaya masu kyau da tuni ya bayyana farin cikin dake gudana acikin zuciyarta na ganin dawowar sujamal lpya wanda already tamkar ɗan cikinta haka takejinshi acikin ranta da zuciyarta,tun safiyar yau din fuskarta yake dauke da murmushi masu sanyi,tun kafin ya iso ta sa aka shirya masa girki kala kala,cikin murna da farinciki tay masa tarba mai kyau,saidai tana gama taya marida jera masa abincin nashi basu ko zauna ba tace mishi ita zata tafi,sam sujamal baiji dadin haka ba duk dama ya lura kmr aranta tana matsanancin son kasancewa tare dashi din amma haka ta danne bukatun nata zuwa gobe domin ya samu ya huta, ta kuma ki mishi sam ta amince ta zauna atare dashi a sashensa burinta a kyalesa shi ya samu cikakken hutu wanda hakan yasa Bai wani iya cin abincinshi sosai ba ya tashi da niyyar zuwa yin bacci.

Da kyarma ya samu ya runtsa yau din duba da yadda mahaifinshi ya bada dokar kada wani yaje kusa dashi bare a damesa,iya wann kalmar kadai yasan ta isa ta hana duk wani mahalukin mutum jin zimman zuwa inda yake hatta Aslinshi.

Haka rayuwanshi ya kasance cikin hutu in yagaji yaje dakin motsa jiki,yau kusan satinshi guda kenan amma babu inda yake takawa face sashen mahaifinshi da kuma masallaci.

Mother susan kuwa kullum itace take rako marida wajen kawo masa abincin data dafa masa domin yaci.

Inda haryau itama bata zauna tay wani nisan hira tare dashi ba saboda tsantsar kiyaye dokan mahaifinshi dayace a kyaleshi ya dan huta.

tasan samun isashen hutu yana da matukar muhimmanci ga sujamal ayanxu musmn in tay la'akari da tarin ayyuka da kuma responsibity na masarautar dake jibge a gabansa yana jiranshi son samu ne sujamal ya dan huta din,snn ya warware gajiyar jikinshi duka kafin ya soma daukan duk wata nauyi dake rataye a wuyansa anan gaba.

LAMARIN GOBE.Where stories live. Discover now