LAMARIN GOBE...
.....sai Allah_The Love circle._
02
Har Wajajen ƙarfe shida da rabi na yammacin ranar gimbiya fazeelat bata samu wani wabi cikakkiyar nitsuwa acikin zuciyarta ba.A Cikin sashenta na masarautar daga ita sai amintacciyar kuyangarta datake kamar matsayin yar uwa agareta mai suna wasila wacce akafi sani da umma Ablah sai babban jakadiyarta da kullum ke tare da ita wato sayyada Ateeqa,bayansu yau kowa ma bata amince mai shigowa nan falon ta ba,iyakacinta nan cikin kai kawo da fargaban labarin da zai biyo baya daga can asibiti wajen surukuwanta hajja abeeda da tuntuni take tsammanin jin labarin wani irin jinsin halitta zata haifarwa sarki.
Tun ficewarta a sashen hajja shashe hanklinta bai dawo jikintaba,sai dai duk tashin hankli da fargaban datake ji a zcyarta baikai rabin adadin abunda hajja shashen takeji a zuciyarta na bakincikin haifar ma mijinta ƴa mace datayi ba.
Abune wanda haryanxu kwakwalwarta ya kasa dauka zuciyarta kuma ya kasa samun nitsuwa dashi,wani kakkarfan iska mai zafi mai kuma nunnuke da barazanar rasa komi nata take shaƙa a kowani kiftawar lokci na rayuwarta.
Tun ficewar gimbiya fazeelat a sashen nata ta saka hannu ta share hawayenta amma bata iya motsawa awajen datake dinba zugum tayi wani irin tsabar bakin cikin dayake mamayarta wanda har ayanxu batajin kafafuwarta ma zasu iya daukarta izuwa sama bisa kan gadonta.
Durkushe a tsakiyar lafiyayyen bedroom dinta tay jikinta na wani irin tsuma da hucin takaici, zuciyarta kuwa ta nitse cikin kogon tunani dan tasan kuka ko jimami bazai ficceta ba,kuma shiru bai taba kawo sauki ko magani ba,Kowani giftawar lokaci fargaba ne mai tsanani ke barazanr haukatar da ita,ta riga ta san waye King Abdul samad shidin ƙwankwason jimina ne mai wuyar shafawa,shi namiji ne wanda ba'a iyar mishi cikin dabara,ba a kuma gane gabarsa bare kuma agane bayansa.
tasan ba lallai bane alkwawuran da mahaifiyarsa Gimbiya fazeelaat tay mata ayau yay tasiri akansa musamman ma inhar yau akace uwar gidansa hajja Abeeda ce ta haifar masa magajin masarautarsa.tana da yaqinin in hakan ya faru toh komi ma zai iya faruwa da ita,samun ɗa namiji wajen hajja Abeeda ba zallan bala'i bane daya sauko ma duniyar soyayyarta,
haihuwar tata tamkar babban barazana ce ga rayuwarta mai gaba daya."toh shin ina mafita?...me zatayi..?
Kuma Ta yaya zata tunkare Abun,lallai bazata sake ta bar rayuwarta ya hallaka a sanadiyar Abeeda ba,bazaitaba yuwa hakan ya faru da ita ba,soyayyar datakyi wa mijinta mai martaba ta mutuwace wanda duk sanda aka raba wnn soyayyr to tabbas tamkar an rabata ne da rayuwarta,batajin zata iya shakar wani kyakwan numfashi awani wajen na daban face a gangan dashi,king abdulsamad shine rayuwarta,yau koda wani zai mutu acikinsu toh saidai ita ko shi amma ba aurensu ba,ba kuma soyayyarta agareshi ba.Ayau tay dana sanin sawa datayi aka raba musu likita mai kula da lafiyarsu duka acikin masauratar,badon hakan ba yau tasan dakomi sai zo mata da sauki wajen kau da abunda Abeeda zata haifa muddin abun ya kasance ɗa namiji ne
Tsaki taja tareda kife kai da ƙarfi a kasa sanin ayanzu kam ko Doc maher,wato babban likitar mijinsu king Abdalsamad ya isheta bare ajega Likitar Hajja Abeedar wato doctor surayya mahmud wacce suke takun saƙa da ita.
Koda shike taji labarin cewa mijin doc surayyar ya rasu jiya,da wuyane in itace yau akan batun nakudar hajja Abeedar murmushi tay cikin ranta dan hakan awajenta labari mai kyau ne wanda shine zai iya bata isasshiyar dama da kuma lokci akan lamarin Cimma burikanta akan Abeeda cikin sauƙi batare da fargaban komi ba.
Dan haka dolene yau din nan ta dauki dukkan wani babban mataki da zai kiyaye faruwar haihuwar Abeeda Domin kuwa tay imani mutuwace kadai yake da ikon da zai rabata da mijinta kuma ya sha abanza amma ba Abeeda ba.Abeeda ko Abunda zata haifa basu isa ba,jikinta da zuciyarta gaba daya bakaramin tsumuwa sukeyi ba,ta dade anan durkushe cikin shirya hanyar da zata amshi saƙon mutuwarta dan tabbas jin labarin samun ɗa namiji wajen hajja Abeeda dede yake da jin sakon malakal maut a cikin kunnuwanta.

YOU ARE READING
LAMARIN GOBE.
Fantasy"GULNAR assidique badaru Ta kasance yarinya mai tsananin jiji da kai da giggiwa wance bata ɗauki talaka abakin komi ba face abun takawarta,ita yar gata ce,tun tasowarta batada wani abar fargaba a duniya face yar uwarta HEER ALKALI wanda take ganin k...