FARKO

863 72 31
                                    

LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

♡ The Love circle

Bismillahirrahmanurreem
Dedicated to fatima isah muhammad.

FARKO...

Hadejiya emirates
4:pm Thursday evening.

Bayi da kuyangu ne bila Adadin a kowacce kusurwa ta cikin babbar masarautar,wasu na a tsatsaye suna gadin hanyoyin wucewa na kowace ƙofa ta shige da fice haka kuma kowanne Da kalar hidimar daya duƙufa yanayi.

Dukkaninsu awajen da irin kalar yadin suturar dake jikin sa na danyar Zaren auduga mai duhu da nauyi,mazansu sun saka kalar ja da blue dinkinsu ta  sasakken riga da wando buje,matansu kuma kalar dark blue ne riga da zani Wanda za'a iya kira da shine uniform dinsu.

Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana raɓewa gefe tareda sunkuyarda kai ƙasa cikin nuna girmamawa da biyayyarsu gamai kkrin shigowa msmn ma da suka tsinkayo sautin katoton kararrawar bango da ake bugawa domin isarda sakon tahowar mahaifiyar mai martaba sarkin hadejiya wato gimbiya fazilat ma'as sama, tare take da na hannun damarta wato Babban jakadiyar masarautar mai suna Sayyada Ateeqa wacce kusan kowa ke tsoronta acikin masarautar.Dan bayan sarki da mahaifyarsa daga gimbiyoyi sai ita awajen zantar da mulki da iko  acikin wann masarautar.

Wanda iya sautin gwalagwalan kafa da na hannu masu sheki ƙirar danyar zinaren dake sakale ƙafar uwar gijiyarta Gimbiya fazeelat ma'a sama shi yake sanar da kowa isowarsu tundaga can nesa.

Gimbiya fazeelat tsayayyar mace ce wanda tun zamanin mijinta king saiful islam khaleefa ta saba caɓa ado da kwalliya,duk inda take takawa toh sautin sarqar zinari ko gwal,ko wani muhimmin dutsi mai tsada dake sakale a tsintsiyar hannayenta da kafafuwanta shike sanarda isowarta cikin fada har izuwa yanzu da zamanin su ya shude ya zamto zamanin dansu mai martaba Abdlsamad saiful islam khaleefa.

Gimbiya fazeelat Ta manyanta sosai Sai dai haryau mulki da kasaita a jininta yake yawo,haka suka wuce ita da jakadiyarta sayyada Ateeqa Cikin bayi da kuyangu ba a samu wanda ya iya kuskuren dagowa kanshi sama ba.

Suna ƙarasowa hanyar dazai shigarda ita ɓangaren danta wato mai martaba sarki ABDULSAMAD SAIFUL ISLAM KHALEEFA ta tsaya cak batareda tace uffan ba ta juyo ahankali tadan kalli gefenta na dama inda jakadiyarta take atsaye,saurin matsowa kusa da ita jakadiya tay cikin girmamawa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su hudu, kallo daya sayyada ateeqa tayi musu suka ja nesa can ahankali suka tsatsaya tareda sunkuyarda kansu can kasa.

Boyayyar ajiyar zuciya mahaifyar sarki gimbiya fazeelat tasauke tareda shiga kofar da aka jima da wangale matashi jakadiya sayyada ateeka ce kawai tabita abaya snn aka rufe kofar.

Katafaren Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji Lumtsattsun kujeru na royal chairs golden and red colour. labulaye da chandelliers suma golden colour sai baza qyalli suke snn Duk wani abu daya ƙawata Falon ya zamto shima golden nd red colour dinne,manya manyan Airmores da incence burners kusan guda shida suna aikin bada Daddan Qamshin turarruka na alfarma da kuma iska mai sanyi wanda already sanyin ma yakama falon takoina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkashi acikin wnn falon.

Babu kowa acikin falon tasu ta farko wanda shine zai sadaka da babban falo na biyu wanda ya kasance falon sarauta daganan kuma harzuwa turakar sarki.

Ratsa dogon Falon tayi jakadiya sayyada na biye a bayanta ta nufi kofar da zai kaita ainihin falonsa na musamman tana isa dede wajen wanda ke tsaron kofar ya bude matashi,cikin takunta mai sanyi da aji ahankali tashige ciki jakadiya sayyada takoma gefe ta ta tsaya daga nan itama tana jiran fitowar uwar gijiyar tata.

Katafaren falone na alfarma an masa kwalliya da royal purple da wani irin cool golden colour,wanda shirun da wajen yay tamkar babu kowa aciki banda qamshi da ƙarar ac dake tashi ahankali.

LAMARIN GOBE.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang