10

236 28 4
                                    


LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

_♡ The Love circle._

10.

Kwance tashe babu wuya yau kusan sati guda kenan bayan ziyarsu cikin fadar hadejiya,a fannin yerima sujamal kullum acikin shiri yake dangane da ayayyukansa dake tunkarosa mussamn ma meeting din dayake dashi mai matikar muhimmanci da zai halarta acan garin lagos nan da wasu yn satikai.

Yau yakasance ranar Alhamis kuma ranace da yerima sujamal yay ban kwana da mahaifinsa dake kkrin halartan wani taro na energy resouces world summit a kasar russia tare da wasu daga cikin hakimansa.

Tun bayan rakiyar daya musu ya dawo sai bai fita koina ba,Hakama yaki amincewa da kowa ya dameshi asashen sa dan hatta abincin shi sister susan ce kawai ta kawo masa dakanta ta kuma tursashi ya danci.

He is being alone for queit long har zuwa wani dan lokci,washe gari da sassafe ya farka yay dukkanin ababen dake gabansa ciki harda bada kulawa ga harkokin fadar  mahaifinsa ayayin da baya nan.

Shauran manyan hakiman da suke rage kaf suna lura dashi ganin yadda yake gudanar da kominsa atsanake batare da wani fargaba ba, kusan salonsa babu wani bambamci dana mahaifinsa,hakama da kalar jarumta da tsantsar iya mulki dake bin jinin jikinsa duk irin na mahaifinsa ne.

Tun anan yafara burge wasu dake cikin fadar domin kuwa duk wani abun da ake nema a iya wynn lokutan yana tsaye akai a matsayin jagoran su kuma ana samun gamsuwa dashi sosai.

Yau ya kasance ranar laraba yawan mutanen dake kai kawo cikin fadar keiser yay bala'in baiwa marida mamaki,wani irin shirye shirye taga anayi mai daukar hankli,an sassaka kujerun zama acan filin da ake horar da daƙaru da mayaƙan masarauta an hura gagarumin dutsin wuta da karare,wann shi ake kira taron zaratan mazaje da sojojin yaki, dan haka dayawansu sun firfito da mataimakansu domin gabatar da gasar koyan riƙe ƙwari da baka,takobi da mashi a filin daga.
Abune wanda aka dade ba ayishi acikin masarautar ba.
musammn ma a gargajiyance,wanda akalla sabida samun cigaba ne da akayi na civilisation da sauran su yasa ake mancewa da al'ada na asali,jiya bayan sallahn isha'i sarkin yaƙi da kuma comanding officer wajeer suka samu daman cusawa sujamal wnn ra'ayi akan cewa yakamata adawo da filin gasar horaswa ma sojoji da dakaren yakin su na hadejiya domin samun cigaba da inganta kaifin basirarsu ta yaƙi.

Sujamal bai amince musu kai tsaye ba harsai washe gari bayan yay kyakkwan nazari.
anshirya za'ayi hidiman ne zuwa yamma lokcin da kowani daƙare zai fito da makamin sa filin daga dan a kwabza wasa.

Yau kusan zuciyar kowa a wanke yake saboda kusan yau ranar hutune ga a ma'aikatar fada, wani irin farinciki da nishadi ne yake tattare da wnn ranar saboda murnan ganin irin wann gasar tasu ta al'ada dake yawan sakasu zumudi da nishadi musammn wajen ganin fafatawa da fierce competition na karfi da karfi tsakanin zaratan maza kuma manyan mayaƙa inda kowa yake kokri wajen baje iya basirarsa wajen nuna kwarewaesa da salon sa na iya yaki da rike takobi.

Wasu basirar su a iya harba kwari da baka ne, wasu kuma amfani da wuƙa,wasu kuma da mashi..kan kace wani abu barden yaki ya tsara yadda gasar zai kasance.

Wajajen Karfe hudu na yamma kowani mahaluki dake masarautar ya fito wajen kwansa da kwarkwatansa kowa ya shirya ne domin kashe kwarkwatan idanu an samu waje duk an zazzauna.

Hakama Zaratan mayaƙa duk suka fito sanye da kayansu na yaki bakake ajikinsu kowa na rike da kalar nashi takobin.

Jim kadan saiga yerima sujamal ya fito shima yana tafiyarsa mai daukar hankli ayayinda duka bayi da kuyangu suka durkusar da kai kasa suna masu raɓewa tareda koma can gefe, ma'n da marida sune kusa dashi suna take masa baya,sai kuma masu tsaron sa wanda suka kai su biyar dake binsu yuuu abaya baya,

LAMARIN GOBE.Where stories live. Discover now