9

188 26 0
                                    

LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

_♡ The Love circle._

09.

Ranar jumu'a da misalin karfe bakwai na safe yerima sujamal ya samu fitowa inda babu ɓata lokaci aka hau kammala shauran shirye shirye da suka rage snn aka fiddo daa wasu kosasshun dawakai na iya mutanen da zasuyi rakiya wa sarki da dansa sujamal fadar hadejiya.

Kamar yadda aka shirya zuwan sujamal a sirrince yau fadar keiser tunda asubahin fari suka soma shiryawa yiyuwar hakan domin bawani daɗewa zasuyi ba ana gabatar da sallahn jumu'a acan za'a dawo dashi gida bisa umarnin mahaifinshi sarki.

Ayayinda ake kan shirin kai ma fadar hadeijiya ziyaran bazata daga cikin beitul kesier,a cikin fadar hadejiyan kuwa babu wani mahalukin dayake da masaniya gameda faruwar hakan dan haka tuni jama'ar cikin fadar hadejiyar suka tashi kowa ya kama harkokin gabansa nayau da kullum batare da sanin cewa sujamal zai shigo fadar tasu yau ba.

Kasancewa yau rana ce ta daban Daddadan sautin algaita,kakaki,
ganga da sauran nau'o in traditonal drums and trumpet su suka cike babban filin beitul keiser

Da safe da misalin karfe 10 daidai lkcin Kusan kowani mahaluki ya fito kwansa da kwartan sa duk ana tsaye ana kallon wucewar dawakansu da suka sha lafiyayyun ado da kwalliya suna wani walkiya kamar ranar hawan daba.

Kosashiyar dokin Mai martaba Sarki Abdul samad saiful islam khaleefa shine a tsakiya tare dana dansa yerima sujamal agefe da kuma na hakimansa daya zaɓa zai yi tafiyar dasu,duk sun sha kwalliya da manyan kaya da kuma alkyabbai na alfarma wanda yawancinsu kalar blue da farine,sai kuma rawanin kansu farare masu tsananin haske wanda suka killace kisan rabi daga kamannin fuskokin su,mai martaba sarki da dansa sujamal ne kawai kayansu ya bambanta da kowa sabida tsadarsu da kuma tsananin kyaunsu.

Tafiya sukeyi a convoy na dawakai da kyafaffun motocin Rolce royce dake binsu a baya ahankli,can Saida suka kusa isowa daf da fadar hadejiya sann sarki ya bada umarnin a sanar dasu,wanda atake labarin yuwar isowarsun cikin dan kankanin lokcin tayi bala'in gigitar da hankulan jama'ar gari kusan kowa saida ya gigice da jin mamaki
musammn ma jama'ar dake zama cikin fadar hadejiya da suka ruɗe gabaki daya,nan da nan gidan sarauta ya kacame da kai kawo babu bata lkci aka hau gyara kimtsi cikin dan kankanin lokci suka shirya wajajensu Tsaf,duk dama zuciyoyin su harynzu cike take da tsantsar mamaki da fargaban irin bazatan da mai martaba yayi musu a wnn rana.

Bayan kamar awa guda
Cikin wata kasaitacciyar royal canopy fari kar na hango mahaifiyar sarki watoh Gimbiya fazeelat ayayinda ta hakimce cikin sigar burgewa da takama akan kujerarta na mulki golden colour mai  sheki jikin ta a kawace yake da wani irin cool
maroon colour french lace wanda aka sakaya shi da handwoven golden alkyabba issashe kuma bajajje har yana bin sawun kafarta,Sayyada ateeka da ummu ablah ne zaune akasa kusa daf da inda take zaune.

Daga su kuma sai kujerar da gimbiya hajja shakira shehu zata zauna tare da diyarta princess sa'adah wanda har iyanzu ba aga fitowarsu izuwa wajen ba tukuna.

Kuyangi da bayine bila adadin a gefe da gefen su dukan su sanye da shudiyar dogayen riguna kowacce dauke da bouyant welcoming flower palates an rubuta kalmar maraba yerima sujamal khaleefa da harufan larabci.

A Dayan canopyn kuma fadawan hadejiyane da hakimai magada arziki da sauran representative din gwamna,with some few ministers,senators and many other business men nd distinguished  guest da suka samu daman isowa wajen cikin kankanin lkci.

Within one hour kusan komai ya kammala tamkar da shirin tarban su ake kwana, zuciyoyin jama'ar masarautar hadejiya kuma acike yau yakeda fargaba da zumudi mai tsananin gaske dan ko a mafarki basuyi zaton hakan zai faru ba.

LAMARIN GOBE.Where stories live. Discover now