LAMARIN GOBE....
......sai Allah._♡ The Love circle._
12.
ArroganceWashe gari da sassafe body gurds sukayi rakiya wa Haidar dan gidan gwamna har zuwa cikin masarautar gumal domin bawa gulnar hakuri.
jikinshi a matukar sanyaye yake sabida tun jiyan yakejin ransa babu dadi,ciwon kaine ke kaikawo dashi tsabar fushi.fuskar sa tun jiya harwa yau babu alamar fara'a ko sauki atattare da ita danji yake kamar an cakke zcyarshi da mashi musamman da yakasan ce mahaifinsa ne dakansa ya tursasa shi zuwa nan domin bawa fitsarriyar yarinyar nan hakuri.
Tun Ƙarfe takwas na safiya haidar ya iso yake tare da mai martaba sarkin gumal,har karfe goma kusan da rabi suna tare amma haryanzu gulnar bataji na farkawa a baccinta ba ma tukuna, bare kuma har ace tay wanka ta shirya ta sakko kasa.Kakan nata kuwa ya fi so ne tazo dakanta taganshi tasan yazo din koda shima ya samu sukuni a cikin zuciyarsa dan sosai yake Yaƙi da duk wani abunda zai iya jefa jikarsa gulnar acikin bakinciki da fushi wanda yakejin koma miye take bukata a fadin duniyar nan zai iya sadaukar da ransa domin ya sama matashi.
Tun haidar yana haɗe rai yanakin amsa hirar mai martaba haryazo ya hakura ya saki ranshi dan baiga alaman ansan yanayi ba.
Wajajen sha daya gulnar ta farka, as usual kuyangi goma ne zagaye da ita snn kowacce acikinsu da kalar aikin datakeyi mata tun daga lokcin data dire kafafunta kasa har izuwa wanka,kwalliya da saka suturarta bata tsinana wa kanta komi,komi bayine suke mata hatta brush,saka pants da bra, sakale agogo,wanda akalla daga yin wanka xuwa shiryawatan yakan dauki awa guda harda dan dori snn komin girmanka baka isa kayi kuskure agabanta ba.
Cikin awa guda cif cif aka kammala shiryata wai ahakn ma yau ta tsagaitane domin umarnin grand pa dinta datake matukar ji dashi a ilahirin duniya,tsoho mai tsananin dore mata gindi,mai ji da ita sama da uban kowa da komi mai yayinta.shikadaine a duk duniya take iya sadaukar mashi wani abu amma bayanshi hatta iyayen da suka haifeta bata sauke musu kanta cikin sauki.
Sai kusan bayan sallahn azahar kafin ta gama kwalemar mulkinta snn ta iso falon mai martaba
Cikin wani irin kasaitacciyar yanayi Qamshinta ya mamaye koina tanai ma haidar din wani irin kaskantaccen kallo.Shikuwa ganinta ma kawai saida yaji ranshi ya dada baci,As usual saida ta sakashi ya kusa walakanta kansa wajen bata hakuri wanda ahakan datakeyi kakan nata baiya ganin aibun halayyarta,haidar bai samu sarari ba saida gimbiya saudatu ta iso wajen ta dakatar mata snn ta sallameshi ya koma jigawa yana mai cikin tsananin fushi da wann ranar,dan rana ce wanda bazai taɓa mancewa arayuwansa ba tuna yadda ƙaramar yrinya kamar gulnar tayi fatali da girmansa da mutuncinsa a idon jama'an dake cikin fada ta hanyar gaggasa mai bakaken maganganu masu zafi.
Bayan tafiyarsa wani sabuwar rikicin ne ya kaure tsakaninsu da gimbiya,anan ma mai martaba yay fafur yace gulnar tay dede data walakanta wani don awajenshi jikarsa ce kadai a duniya wanda bata laifi.
Da yamma lis dandanzon motocin lemouzine royale daga masaurata tare da kakanta HRH Ahmadu gumal aka mata rakiya izuwa dutse intl airpot inda private plane din mahaifinta ke jira.anan sukayi ban kwana gulnar ta shirya tahowa asalin mansion din mahaifinta dake garin Abuja.
Basu fi wani 30 mint a sama ba suka iso outskirt na Anguwar Asokoro,her favrite car jam wato Bentayga shine yaxo daukarta tare da body guards din mahaifinta,Alexander mac queen jumpsuit nd long breasted jacket ne ajikinta kafafunta sanye da balenciaga espradile da golden chain side bag dinta na macqueen din mai tsada.
Idanuwanta ɗar suke acikin rectangular shades farare sol masu haske tafiya take bata kallon ko ina sai gabanta,direct wajen motar ta nufa aka bude mata gidan baya ta shiga ta kame a owners coner ta cigaba da latsa tsadadden apple phone dake hannunta.

YOU ARE READING
LAMARIN GOBE.
Fantasy"GULNAR assidique badaru Ta kasance yarinya mai tsananin jiji da kai da giggiwa wance bata ɗauki talaka abakin komi ba face abun takawarta,ita yar gata ce,tun tasowarta batada wani abar fargaba a duniya face yar uwarta HEER ALKALI wanda take ganin k...