15

631 31 21
                                    

LAMARIN GOBE

SURAYYAHMS

15.

Abuja,Asokoro.

Karfe takwas saura jirginsu Heer ya iso garin Abuja,bayan sun dawo gida Kafin heer ta yi komai wanka ta faɗa don ji ta ke jikinta har wani danko-danko yake mata.
Ga ta da son wanka dama kamar agwagwa komai sanyin da akeyi sai tay wanka kamar sau uku arana,balle kuma a lokacin zafi. yau Hatta gashin kanta ji ta yi yana mata wani kaikayi kaikayi duk da ma yau baifi kwana biyu da wanke shi datayiba.

Mikewa zaune tayi Ta warware gashinta data dunkuleshi ta shiga toilet din da ke cikin lapiyayyen dakin nata mai wani irin kyau da tsari saidai bamai yawan tarkace ba
Kominta sky blue nd white colour ne.

tsaye tayi na dan lokaci kamr wata mai nazarin bandakin nata wanda ke dauke da lafiyayyen babban bathtube na hollow cup jacuzzi,
kalarsa white komai da ke cikin bandakin kalarsa kenan.Ahankli Ta mika hannu ta zare ribbon din da ta daure tulin gashinta da ya riga ya wargaje ya zubo a kafadunta,baki sidik mai wani irin tsayi da tsantsi shampoos da
conditioners kala-kala masu tsada dake a jere ta dauka inda kusan babu kalar da babu awajen wannan na da nasaba ne da yadda take bala'in son tsaftace komi nata.a lokacin ta manta da komai ta shiga tara ruwan dumi cikin bahon wanka snn ta shiga ta soma abin da ta fi so a rayuwarta wato wanka.

Ta jima tana kalkale sassalkar fatar jikinta kafin ta soma wanke  sumar kanta bayan tayi conditioning dinsa da mint hair masque tana cudawa da kumfar bayan Ta kammala komi ta dauro alwala ta fito snn ta bushar dashi a handryer.

Doguwar rigar baccinta na mickey mouse ta saka ta dauko hijabin sallarta ta tada sallah Sai da ta rama sallolin da ake binta sannan ta samu nutsuwa tazauna ta soma cin abincinta acikin nitsuwa,brown spaghteti jollof da meat balls,A gefe kuma wani gasasshiyar meal din hanta ce a cikin bowl na tangaran ta sanya fork tana cin hantar a hankali bayan ta gama da jolof din.Da ta gama, ta kora da ruwa mai sanyi, sannan ta kishingida a sofa tana hutawa bazata bacci mai nauyi ya sunkuce ta.

Can cikin baccinta mai nauyi taji wani irin sautin Ƙida na tashi daga sashen yar uwan tata gulnar,ahankli ta daga ido ta kalle agogon bango lokacin karfe sha biyu da rabine na dare.

Ajiyar zuciya heer ta sauke thinking of ko mafarki take kanyi can cikin lumshe idanuwanta datayi takuma bude idon ta kara tsinkayo sautin wakar sean paul dayake duka akan speakers.
Dim dim dim kamar zai balla bango.

Da kyar ta watsake idanuwanta ta sauko akan kujeran data kishingide ahankli snn ta saka bedroom sleepers din ta na fenty ta fice tanufi sashen gulnar din duk jikinta a muce sabida baccin datayi..

Tundaga kan corridor ta toshe kunnuwanta sabida kara kamar gidan yan party kuma kamar ba tsakar dare ba.

Tasan dolene wann karar ya hana ma'aikatan gidan  samun bacci,kai koma badon hakan ba ai baidace tsakar dare a kunna ƙida acikin gida ba.Jin yadda ko ina ya dau wani iri shiru yasa tajin wani iri ajikinta.
Da alaman kowa tsoron magana kawai yake yay ma gulnar din dan ansan yau alhaj assidique dazai iya tsawatar mata baya kasar princess sanah kuma bata daukar yarta matsayin mai laifi akan komi.

Tsaki Heer taja kafin ta isa bakin kofar dakin gulnar din dake nan a budê,kai tsaye ta shiga ganinta zaune agaban fankacecen mirrornta tana kan rabza kwalliya jikinta sanye da wani irin damammen crazy jeans blue colour da wani tsinannen white crop top wanda ko brazier bata saka masa ba daga inda take kana ganin motsin dukiyar fulaninta.

Batayi la'akari da shigowar heer ba har saida taji music dinta ya dauke cak alaman an kasheshi,ta cikin madubi ta Dago kai ta kalleta cike da harɗe fuska taja wani irin doguyar tsaki mai sauti batace mata uffan ba.

LAMARIN GOBE.Where stories live. Discover now