LAMARIN GOBE....
......sai Allah._♡ The Love circle._
03.
G.W.ATake Mai martaɓa ya dago kai sama fuskansa dauƙe da wata iriyar lafiyayyr murmushin da bai taɓayin ma wani irinsa a duniya ba,ahankli ya lumshe idanunsa snn ya budesu cikin wata nitsutsayar sigar kamewa,ahnkli snn ya furta "Alhamdullhi" kasancewar shi kamammen mutum wanda bai cika nuna zaucuwarsa da abu a fili ba..wnn murmushin dayay kurum ya isa ya isar ma dukkan mai kallonshi saƙon sanin cewa lallai yana cikin matsanaicin farinciki a daidai wann lokcin.
Aikuwa babu bata lokaci labari ya xaga koina ya kuma fara shiga kunnuwan manyan manyan Sashuna dake cikin masaurautar lungu da saƙo anata sambarka da jin labarin samun sabon magajin masarautar hadejiya.
Kusan dare ne wanda ba a taɓayin irinsa ba,kowa na farincikin samun hakan domin kuwa mafi yawan alummar cikin masarautar na kaunar gimbiya bahriyal Abeeda bana kadan ba.
Babu wani abun da ake ciki gameda haihuwar wanda doc maheer bai sanar masa ba,Sun dade suna tare su biyu inda daga can asibiti har an turomusu video da hoton ɗan da aka haifa sarki Abdlsamad ya saka agabansa yana kalla.
Allah ne kadai ya san iya Abunda yakeji acikin zuciyarsa musmmn dayaga lapyayyen yaron
Wanda atake yaji duk duniya kamar bai taba jin yanason wani abu kamar wann jaririn ba,how he wish he can be with him right now,saidai Doc maher ya riga ya bashi tabbacin dawowa da su cikin masarautar zuwa gobe da sassafe lkcin hajja Abeeda ta samu farfadowa daga sumewar datayi.A Asibiti kuwa anriga an ninka tsaro a maternity babu shigewa babu ficewa hatta nurse susan datake nan aka haifi Ɗan sarki ba a kyaleta ta fito waje ba domin umarnin sarkine bai amincewa kowada yasan cikakken labari ko kamannin dan nashi ba.
Iya su da sukenan aka haifeshi su sukasan da kamanninshi amma bayan nan daga sarki sai likitarshi doc maheer suka sani.
Koda Labari ya riske kunnuwan gimbiya fazeelat cikin zuciyarta ne kawai tay matukar farincikin samun jika kuma magajin sarki amma a zahiri bazata taɓa iya nuna farincikin ta ba sabida tausayi da kuma bakincikin jin cewa ba hajja shashe datake jininsu jinin sarauta bace ta haifi da namiji,hajja Abeeda datake barece ta haifa.
Lokaci guda ilahirin cikin masarautar ya sukurkuce anata kai kawo da kananan maganganu musanman ganin yadda gimbiya fazeelat ta basar da lamarin bata wani nuna farin cikinta a bayayyane ba itadae damuwarta yadda gimbiya shashe zatajine shiyasa batakoyi yunkurin zuwa barka wa danta ba,ana fadar sakon basuyi wata wata ba ita da jakadiyarta sayyada Atika suka wuce direct suka nufi sashen hajja Shashe domin duba yanayin da zata shige ciki sunakaiwa kuwa suka samu harta sallame kowa ta bada umarni mai tsauri akan arufe mata kofofin da suke sashenta
Bata bukatar ganawa da kowa yau haka gimbiya fazeelat din itama ta hakura ta koma sashenta sam hanklinta bai kwanta baUmma Abla,datake tamkar yar uwa gareta itake kwantar mata da hankli tanai mata nasiha amma sam bajinta takeyi ba sabida sam batason abunda zai batawa hajja shashe rai duk dama jikarta ne aka haifa kuma haihuwar abun Alfahari da farincikine agareta sosai.
Amma dake ba shakira bace ta samar mata da hakan Har dare ya raba bataje tay wa Ɗanta san barka ba barema ta nuna farincikinta akan haihuwar a fili.
2:30pm can cikin tsakiyar dare bayan komi ya lafa wani farin kyalle ne mai tsayi aka zagaye gadon da gimbiya bahriyal abeeda da danta suke kwance,tsakiyar dare Bahriyal Abeeda ta farka a doguwar suman datayi bayan ta dauki jinjirin ta ta shayar dashi ruwan nono saita maisheshi wajen baccinsa ta sauko kasa tanajin fitsarin da ya cika mata mararta kamar zai fasa mata marar nata..Lokacin dukan masu kulawa da ita na tare da ita,ta daga ido can ta hango nurse Susan na zaune agefe ta kan karanta bible dinta
har tay fitsarinta ta dawo ta kwanta bata tanka kowa ba,saidai bata iya samun wani baccin ba har can gabanin asubahi idanunta a bude suke tanajin wani irin niimtaccen sanyin asubahi mai tsananin niima da dadi na bugarsu duka ayayin da ilahirin tawagar nata suka lula cikin duniyar baccin daya kwashesu a bazata.
YOU ARE READING
LAMARIN GOBE.
Fantasy"GULNAR assidique badaru Ta kasance yarinya mai tsananin jiji da kai da giggiwa wance bata ɗauki talaka abakin komi ba face abun takawarta,ita yar gata ce,tun tasowarta batada wani abar fargaba a duniya face yar uwarta HEER ALKALI wanda take ganin k...