4

236 31 2
                                    

LAMARIN GOBE....
......sai Allah.

_♡ The Love circle._

04
Lokaci zuwa lokaci Abubuwa dayawa suna gudana wasuna canxawa lokacin haifaffen Ɗan sarki Sujamal wanda haryau babu wanda ya san kamanninsa face mahaifyarsa da kuma nurse susan yana kkrin cika wata sha takwas a duniya gimbiya bahriyal Abeeda ta fara samun mafita ta hanyar turo boyayyar wasika izuwa ga ummu Abla(wasila) wato Amintacciyar kuyanga kuma yar uwa ga gimbiya fazeelat mahaifyar sarki wacce dama ita kadaice ta dauke ta tamkar ƴa acikin masarautar.

Ta gaya mata suna raye amma acikin wasikar bata iya fayyace mata inda suke ba sabida gudun abunda zai iya dawowa garesu duba da yadda duniyar ta dawo babu amanar sirri babu kuma yarda.

Cikin ikon Allah ummu Abla ta fara bincike mai tsauri akan zantukan Abeeda,komi ta gudanar dashi a boye batare da tay gigin sanarda mai martaba ba kamar yadda Hajja abeeda ta bukaceta tay shiru sakamakon yawan sharrin dake ciki, ahankli har itama ta samu nasaran soma fahimtar lamarinsu hajja shashe ta kuma samu gamsashun amsoshi da tabbaci akan mutanen da Abeeda take zargi.

Daga lkci xuwa lokci haka sukan rubuta boyayyr wasika wa juna acikin haka har suka shirya hanyar da zasubi su bayyana lamarin wa sarki abdlsamad Saidai kafun suyi hakan ranar da zasu hadu Allah ya hadasu da wata masifa ta yan daɓar wazeeri da suka gano mabuyarsu suka farmusu wanda sanadiyar gujewa don neman tsira hakan ya jawo aka kusan rasa rayuwar gimbiya bahriyal Abeeda, sister susan kuma ta rasa idanuwanta ta dawo bata gani kwata kwata, Sujamal ne kawai bai samu raunin komi kuma Alhamdullhi duk da hakan daya samesu ba'aci nasaran kamasu ba.

A wani tsauni da suka boye kansu na kankanin lkci bahriyal Abeeda ta cika sabida kakkaifar dafin wuƙa da aka cakka agefen cikinta, ta bar danta sujamal amana awajen nurse Susan kafin nan saida ta rubuta wasiƙa mai tsayi akan abawa mijinta king Abdlsamad wanda tasan ba lallai bane su kara ganin juna.

Wasikar ta ya kumshi abubuwa uku masu matukar muhimmaci
Na farko hakuri da qaddara,na biyu biyayya ga uwa,na karshe alkwari ne akan rayuwar dansu sujamal.

inda ta nemi alfarman cewa tana son dansun ya rayune a matsayin boyayyar mutum wanda babu wani mahalukin da zai san asalin kamannin shi face inshine dakansa ya bayarda dama.

Kodayake jariri Bayan mahaifinshi da doctor maheer,da nurses din da suka amshi haihuwarsa aka kashesu bayansu babu wanda yasan zak kamanninshi ayanzu sama da bayan ita da nurse susan.

Acikin wasikar sai tace  bata amince wani halitta na daban acikin masarautar hadejiya da kewaye yasan da asalin kamannin fuskarshi ba harsai ya girma yay aure.

Nurse susan batayi kasa a gwiwa ba duk da nakason idanu data samu saida tay iya kkri wajen tura sako wa ummu ablah ta hanyar aike dan tasan daga wnn rana bazasu iya tserewa duk wani masifar da zai biyo bayansu ba.

Faruwar hakan yasaka ummu ablah tay gaggawar sanar da doc maheer dukkan abunda ake ciki bata boye masa komi ba,daga nan babu bata lokci shikuma ya fahimtar da sarki Abdlsamad duk dama abubuwa masu wuyar daukace awajensa saidai kuma ya yarda da duk wani nazari,hikima da hukunci irinna matarsa Bahriyal Abeeda maiyuwa hakan da sukayita boyewa yanada matukar muhimmaci ga kare rayuwarsu dana dansu.

jarumta da karfin zuciya shine kadai ya bashi
gwarin gwiwa suka shirya zuwa wajensu har ya karance wasikar bahriya kafin nan aka suturta ta aka kaita makwancinta.

Tunda ya fice aranar sai Bai dawo cikin masarautar sa akan lokci ba har sai Bayan dayay makokin Hajja Abeeda ya kuma samu nitsuwa tare da danshi sujamal ya kuma amshi qaddarar rasa Abeedansa na har Abada.

Tsawon kwanaki bakwai babu wanda yasan inda suke boye face ummu Abla da kuma doc maheer sai kuma nurse Susan da abeeda ta bata amanar kulawa da lapyar sujamal,Dan hatta wayanda aka wakilta suyi kyakywan bincike bisaga labarin da bahriya da nurse susa suka bayar basu san inda suke ba.

LAMARIN GOBE.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang