💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
🙌First lady🙌
------------------------------------------------------------------
_Yar lelen Taskira _ --------------------------------------------------------------------
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________بسم الله الرحمن الرحيم...
فيدك، ابي وامي يارسول الله (صل الله عليه وسلم) 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Free* 📙EPISODE1️⃣
PAGE5️⃣1️⃣TYPING📲📲📲
YAN KASUWA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU K'OFA ABUD'E MU NA TALLATA KO WACE IRIN HAJACE AKAN FARASHI MAI SAUK'i
Zaku iya mun magana ta wannan
Layin +2348069059746
___________________________________________
follow me please
On
@Arewabooks
@FaizatouWattpad
@Fai'zaMuraiFacebook&instagram
@Pha'eezah Almustapha
___________________________________________♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️
Cikin mintina da basu wuce talatin ba Unni tasa ank'ara gyarawa Ammie sasashenta Dake kusa Dana Fulani Wanda Dama ba,a barshi haka ba,ana gyaran Sa duk sati duk da kasancewar ba kowa aciki.
Sarki Ali ne da Unni ta aika Masa da sak'on zuwan Ammie yashigo cikin farin ciki tare da sallama abakin sa yasha rawani da wata had'add'iyar Alkyabba Dake nuna irin kud'in da ke tattare da ita har k'asa ya durk'usa yagaida surukarta tasa Kuma Mahaifiyar sa,cikin farin cikin ganinsa Ammie ke Karb'a gaisuwar tasa, Sallamar Hajiya ce itada Mama Dije da suma sak'on ya Isar musu na zuwan Ammie, rungume Ammie hajiya tayi harda Yan hawayenta tana Furta Ashe Rai kan ga Rai Fatima cikin farin ciki Ammie take Furta Allah ya Nufa Gimbiya Halimatu itama tana sharar nata hawayen yanayin da suka shiga duk sai da suka bawa duk Wanda ke gurin tausayi,Dan su Unni sun San irin shak'uwar Dake tsakanin su na k'awance a chan lokuttan Baya da suka shud'e,Sallamar su Nisa ce da K'arar da suka Saka ce ta farin ciki wadda gaba d'aya Muryar Nisa tafi d'agawa da tasanya kowa duban k'ofar shigowa da gudu suka fad'a kan Ammie da suke tsaye itada hajiya suka rungumeta suna mata sannu da zuwa cikin farin ciki harda Saka mata kuka lallashin su take Yi cikin murmushi da farinciki,tare da Karb'a musu barka da zuwan da Suke mata, congratulations ta k'ara furtawa Nisa Ashe an girma har angama makaranta Yan matan Su Hassana ,murmushi Nisa tayi kawai tana k'ara lafewa kan jikin Ammie,Ammie ce tak'ara Furta Amma dai za,ayi muna walima Koh?Kai Nisa ta d'aga mata,Unni ce cikin d'an wasa ta Furta Ammie su d'aga Miki Ajiki kar su iyar muna Dake cikin murmushi da dattako Ammie da har ta zauna a inda ta tashi zuwan hajiya ta Furta k'yalesu Hassana in basu zauna ba a Ina zasu zauna Abunda zan musu Kenan naji dad'i Dan nasan irin yadda sukayi kewata,d'an hawaye ta share afakaice tare k'ara k'awata fuskarta da murmushi.
Dr.Ammar da Dr Aj Dake a falon zaune ne suna tab'a fira sama sama wadda Aj ne Mai kokarin Yinta shi uban gayyar uhm ne sai Aah yan misklillancin sun motsa,k'arar da Nisa ta saka ce tasanya Dr Aj Furta subhanallah tare da Jin gabansa ya fad'i domin shi har ga Allah ta Nisa kad'ai yaji,Dr.Ammar da Shima yaji sautin ne nata itada Inayah tare da Jin surutun mutane ak'asa yayi kamar baiji ba,Cikin yar damuwa Dr.Aj ya Furta Dude muje muga Abunda ke faruwa inba jikin Yuhanis ne ya tashi ba,kallon k'asa k'asa Dr Ammar yayi Masa tare da Furta sai kadawo mugun kallo Dr Aj yayi Masa Yana ficewa daga d'akin tunda ya doso falon yagane Ammie ce ta hanyar Muryar ta yaji da bata chanza ba,duk da yanayin tsufa cikin farin ciki Dr.Aj ya Furta marhababiki ya Ammie,ya hanya yamata,sannu A hankali take ka'bawa cikin farin ciki tare da K'ara tayasu murnar bud'e Asibiti da Kuma k'ara yimusu barka da dawowa gida duk da ta musu A waya,tambayar sa take Ina D'ayan Bokon turan ....
YOU ARE READING
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
Aktuelle LiteraturHaka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta...