💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
🙌First lady🙌
------------------------------------------------------------------
_Yar lelen Taskira _ --------------------------------------------------------------------
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
____________________________________________* بسم الله الرحمن الرحيم*...
*فيدك، ابي وامي يارسول الله (صل الله عليه وسلم)* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Free* 📙EPISODE1️⃣
PAGE5️⃣5️⃣TYPING📲📲📲
Idan Baki karanta ba ki fara karantawa kar abarki Baya atafiyar nan,domin LITTAFIN AMAFARKI NASANTA 📚 daban yake,labari ne da ya had'a komai Dake faruwa awannan duniyar tamu musamman abun da ke faruwa a wannan k'asar tamu,labari ne da ya d'auki dogon lokaci Ina tsara shi,littafin ya wahalar Dani sosai yadda Baku tsammani,zan iya ce muku yayi shekara biyu wannan littafin atare da ni sai dai akwai dalilin da yasa nakasa wallafasa atake,Ina Baki shawara ki karanta domin na goge Alkalami na nayi rubutu da basira ta Babu kissa Babu munafunci bare shakkar wani,domin Babu Wanda nake tsoro face Allah na.
Shiyasa nabar muku shi a free domin Alumma su Amfana dashi sosai,saboda darasin da ke acikin book d'in.
Allah Ina rok'on ka kabani Ikon kammala wannann book lafiya🤲🤲🤲🤲🤲🤲-----------------''''''''''---------------------''"""""-------------
follow me please on
*@Arewabooks*
@Faizatou*@Wattpad*
@Fai'zaMurai*@Facebook&instagram*
@Pha'eezah Almustapha♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️
💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋
____________________________________________
'Da innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Aunty Laila ta mik'e daga kan carpet din da suke kwance itada sarki Umar,wayen da bacci ya kwashe,bayan gama mugun mafarkin ta da Norah,wasu zakuna ne biyu sun biyo ta zasu cinyeta tana ta kuka tana neman agaji gashi bata ma iya gudun.zufar Dake saukar mata take sharewa tana cigaba da Neman Agajin ubangiji,A hankali ta ida mik'ewa daga kan sallayar bayan Jin kiraye kirayen sallah sama sama,hasken fitilar wayarta ta kunna sai dai wayam tagani bayan haska kan gadon inda ta kwantar da Norah cikin tashin hankali ta tada sarki Umar tana Ambaton sunan NORAH cikin tashin hankali da yanayin kukan da ya b'alle mata tunano mafarkin da ta gama yanzu,A Ahankali cikin shesshekar kuka take sanar dashi Rashin ganin Norah akan gadon.Cikin tashin hankali dukkaninsu suja fara binciken d'akin har toilet da sauran Spare rooms din sun duba,sai dai Babu ko Mai kama da itane,sun tsinci kansu cikin tashin Marar misaltuwa bayan da suka tambayi Mai gadin gidan in yagan ta,ko yaji kukanta, ko yaga fitar ta gidan ko yaga alamar wani ya shigo gidan,sai dai dai Ina Babu Amsa cikin tashin hankalin da yatsinci kansa Shima yashaida musu bacci yaci k'arfinsa ya bar k'ofar gate Abud'e jikin su yayi mugun sanyi fahimtar cewa ta bar gidan kenan ba dauke ta akayi ba,Aunty Laila Dake tsaye kawai suka ga ta zube cikin tashin hankali aka Nemo ruwa aka yayyafa mata,Koda ta bud'e idanunta da sunan NORAH ta fara magana tana cigaba da kukan ta,A hankali uncle Dake rungume da Aunty Laila yake nazartar yadda tabar gidan inda take yagano cewa tabar gidan ne tana halin Neman su bayan ta farka atsakar Daren taci karo da fitilar wayar sa da ya kunna ta mutu inda ta dunduna acikin duhu,har ta fice sanadiyyar wayarsa da tadauke Babu isasshen chaji wadda ya kunna mata hasken ta.
YOU ARE READING
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
General FictionHaka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta...