https://chat.whatsapp.com/L42Op0Ya7YPDsMhkJtVRbI
https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y
💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
🙌First lady🙌
-------------------------------------------------------------------
_Yar lelen Taskira _ --------------------------------------------------------------------
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_________________________________________🌹بسم الله الرحمن الرحيم.🌹
فيدك، ابي وامي يارسول الله (صل الله عليه وسلم ) 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Free* 📙EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣9️⃣TYPING📲📲📲
_In Sha Allah nadawo kenan da yardar Ubangiji na dawo ne ta dalilin matsin da nake samu daga gareku fans💋💋 duk da Abunda ke gabana,wannan shi kad'ai zai nuna muku irin k'aunar da nake muku,Ina godiyaah,_
_Da kulawarku agare ni Allah yabar k'auna_follow me please on
@Arewabooks @Faizatou
Wattpad @Fai'zaMurai
Facebook&instagram.
@Pha'eezah Almustapha♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️
Tun bayan da suka dawo gida yagabatar da sallar isha'i A d'akin sanadin Rashin samun jam'i da baiyi ba,wanka kad'ai yad'auro tare da alwallar kwanciya bacci yau ko yen shafe shafensa baiyi ba ya leme akan had'add'en gadonsa na Alfarma.
Kwance yake akan gadon yayi d'ai d'ai daga shi sai tattausan towel Wanda iyakar sa K'ugunsa,baccin sa yake shara hankali kwance, sanyin A.c da yanayin sanyin da aka fara yana shigarsa hankali kwance,Jikinsa sai shek'i takeyi na Hutu da tsabar kyau.
'Murmushi yake ta faman saki shi kad'ai acikin baccin nasa,chan Kuma A hankali ya fara ware manyan idanunsa har yabud'e su tar akan pop d'in d'akin,mik'ewa zaune yayi akan gadon tare da jinginawa akan head din gadon Yana Jin wani yanayin farinciki nasake shigarsa fiye da Wanda ya tsinci kansa aciki d'azu da yafara tunano Abunda yafaru acikin mafarkin nasa da yagama ayanzu......
Zaune yake akan had'add'en gab'ar ruwan swimming pool din k'afafunsa na Lilo aciki shiyana awaje iskar wurin yake shak'a cikin wani yanayi Mai sanyi da yatsinci kansa aciki,takon tafiyar da yaji ne abayansa yasanya sa A hankali bud'e kyawawan idanuwansa Yana waigawa dasauri Dan Jin muryar da baiyi tsammanin ji ba ayanzu tayi sallama....
Kyakkyawar fuskarta Mai cike da annuri yaci karo da ita tana ta sakar Masa kyakkaywan murmushinta Mai narkar da zuciyar 'yan maza.
Kallonta yakeyi da kyawawan idanunsa cikin wani yanayi na farinciki ko akasinsa,har ta iso inda yake zaune, zaman ta akusa da shine yasanyasa sauke nannauyiyar ajiyar zuciya wadda Bai shirya ma fitowarta ba,idanunsa Yada'uke Ahankali daga kallonta cikin wani yanayi."Assalamu Alaikum"
Ta Furta cikin zazzak'ar muryarta
"Wa aiaiki Assalam" ya Amsa mata cikin sakin fuska da wani yanayi na farin cikin ganinta Kuma araye.
K'ara Furta masa tayi
"D'an uwa na nadawo gareka,k'ara ware manyan idanunsa Dake Lumshe yayi akanta Yana mata wani irin kallo Jin furucinta, k'ayataccen murmushi ta Masa Wanda yasanya sa Shima sakin wani had'add'en smile nasa Mai k'ara wa fuskarsa kyau na musamman.
YOU ARE READING
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
Narrativa generaleHaka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta...