💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫Firstlady🙌🙌
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*
*💫P.E.W.A💫**Home of perfect essential writer's together we stand🤝*
*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*
*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*
*Free* 📙
EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣3️⃣TYPING📲📲📲
Bayan rigunann sun ciye da wuta ne ogan yace su rubuta sak'o su turawa duniya cewa sun kashe 'yan sandan nan da ake ta Nema ruwa ajallo wayenda ake Nema tun watanni uku da suka wuce,take Anan kuwa suka watsa hotunan Yan sandan nan da yadda suka kashe su har yadda Namun Daji suka lamushe su suka musu cin gilla Wanda Dama sun Riga da sun Yi d'auka.
Hasbunallu wa ni'imal wakil..
Ogane yaciro wayarsa k'irar iphone 14promax yayi dialing numban din da akayi saving da MY TEAM yakira,Senator Jamil Babuga ne yafara yin magana bayan receiving call din cikin yanayin kamar na maye ya furta "yane oga",Shima Captain Anas Lemu Dake cikin Taron Dan dazon manyan Sojoji ne ya mik'e tsulum ya fice daga d'akin Taron bayan Bada uzurin sa na k'arya,A b'angaren Emir Kabir Saraki ne yad'aga Kiran yanayin sallama bayan tashi da yayi daga cikin iyalan sa,sai Kuma minister Isyaka Muradi da yad'aga nasa Kiran Bayan korar 'yan matan Dake a dakin nasa wayenda ya gayyato agidan shak'atawarsa..Bayan gama gaisawar su ne mutumen da ake Kira da oga ya sanar musu da hukuncin da ya Yanke kaitsaye Bada shawarar su ba,Dukkaninsu sunji Dadin hukuncin kashe wayen nan matasan polisawan domin gudun tonuwar asirin su,Emir Kabir Saraki ne cikin Jin dad'i ya furta Dama ni oga tuntuni naso akashe su karsu kub'uce muna Asirin mu ya K'ara Shirin ban kad'uwa,kunga ita wacchan matsalar tuntuni mun kawar da ita duk da bamu mukayi aikin ba,Kuma namu nakanmu muka so muyi da hannun mu yadda zamu Fi samun kwanciyar hankali,Hakane cewar senator Jamil Babuga sannan yakara furta Nima wallahi tuntuni hankali na yake a tashe,Captain Anas Lemu ne ya furta nifa haryanzu hankalina atashe yake akan mutuwar tsohon ministan tsaro da binciken laifukka Gani nake kamar zai dawo daga mutuwarsa...
Minister Isyaka Muradi ne cikin D'an faduwar gaba da yar damuwa ya furta nidai abar maganar minister of security and investigation crimes (S.I.C) domin tana d'aga mun hankali cikin Jin haushinsu oga ya furta ku wayen na irin mutune ne mutumen da ya k'one k'urmus kuce ya dawo nida kaina naga gawarwakinsu shida matar sa babu kyan gani 'yar su ce kad'ai ba 'asamu tata gawar ba domin ita gaba d'ayanta ta k'one..shine har kuke wani banzan tunani chan yakai karshen maganar cikin wani haushin tuno maganar Captain Anas Lemu mugun tsaki yaja Mtssw sanann ya cigaba da magana "Naji mission din da kuka samo muna Mai kyau domin akwai tsoka aciki,tabbas Yana buk'atar manyan makamai masu kyau irin wayenda bamu dasu a Nigeria wayenda sojan Nigeria Bai tab'a rik'a suba domin munsan masu tsaron gidan sa basu da wasa ko mu Banda sun sanmu da bazasu rik'a bari mugansa ba Dan basu cika yadda da mutane ba..
Emir Kabir ne ya furta ai shiyasa mukasa akawo odern wasu tak'arkashin k'asa Shekaranjiya,munyi Kiran layinka bamu samu ba,sai muka aiwatar domin munsan dama anyi maganar makaman awanchan zaman,oga ne ya furta "na cire layin ne akan k'aramar wayar kasan bamu shiga mutane da kowanne kalar sim card musamman irin wannan harkar ta sirri ..dariya dukkaninsu suka Sanya cikin annashuwa,Anan ya umurcesu da su shirya su shigo dukkaninsu su had'u anan dabar farko Ranar wani sati Mai zuwa,Amsawa dukkaninsu sukayi da Tau sannan sukayi sallam,wayar ya mayar Acikin aljihunsa,sannan suka d'auke sa suka Mai dasa dabar farko inda suka d'auko sa sannan yayi sallama dasu ya bar dajin...
YOU ARE READING
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
Genel KurguHaka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta...