CHAPTER 56

13 2 0
                                    


💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

🙌First lady🙌
------------------------------------------------------------------
_Yar lelen Taskira _ --------------------------------------------------------------------
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________

*بسم الله الرحمن الرحيم*...

*فيدك، ابي وامي يارسول الله (صل الله عليه وسلم) *🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE5️⃣6️⃣

TYPING📲📲📲

follow me please on

*@Arewabooks*
@Faizatou

*Wattpad*
@Fai'zaMurai

*Facebook&instagram*
@Pha'eezah Almustapha

♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️♠️

***
______________________Halee ce kwance yau tun safe bata da lafiya sai Kuma ciwon ya K'aru akan Abunda Baba Asabe ta Yi mata akan ta zubar da garin Koko ba da gangan ba,ta zazzage ta tare da mari, Mari har biyu,tare da kalamai marassa dad'i, A yau ta na Jin bazata iya hakuri ba tanason sanin itadin Wacece,Ayau ta d'au Alwashin duk da yadda take Jin Rashin lafiyar na damunta ta matsanancin ciwon kan da take fama dashi sai ta Rok'i Baba Adee Da yasanar da ita d'in Yar tsintuwa dince Yar gaba da fatiha kamar yadda Baba Asabe ke yawan Furta mata...
Ahankali hawaye masu zafi suka silalo mata masu zafi da rad'adin Rashin makama,gwanin ban tausayi gefen hijab d'inta tasanya tashafe,Khady Dake kallon kyakkyawar fuskar ta da yan yatsun Baba Asabe suka kwanta rad'am akan kyakkyawar fuskar ta kamar an Dora su abu ga farar fata,Kai ta girgiza kawai na tausayin Yar uwarta ta,Dake cikin rad'adin Rashin gata na Mahaifiya, Addu,a tayi Allah ya bayyanar da iyayen
Halee idan har suna Raye da ahalinta,tunda dukkaninsu yanzu sun San ba yar Baba Adee bace.

Sallamar Baba Adee ce ke katse ma Khady maganar zucin da takeyi,Dan dama yaune yasanar zai dawo Dan yak'ara Duba jikin Halee da yatashi Kwanakkiin baya ,fitowa Khady tayi ta tarbesa cikin farin ciki,ruwa takawo Masa da Abinci bayan karb'ar jakarsa takaimasa da'ki,A hankali ya Furta Khadija Ina shalele,cikin Yar damuwa Khady ta Furta tana d'aki batada lafiya tun safe A hankali cikin dattako da kulawa ya Furta shine ba,a kirani aka sanar Dani ba,ina ita Lauren take ne,Khady cikin Jin haushin Mahaifiyar ta ta tafurta cikin gayya ta tafi gidan indo,Dan sai da ta kwabe ta akan kar tace Masa gidan indo taje,shiyasa tace mata tace wai tace gidan Baba mudi taje,Mahaifin Baba Adee"wurin ganin iyah,Dan tasan ya Hana ta zuwa gidan Indo domin yasan harda chan ake k'ara b'ata Masa mata ake hure mata kunne tadawo tana wulakanci guda guda ga Halee,shanye b'acin ransa yayi Yana Furta kiramun ita inganta in tana iya fitowa..da touhKhady ta Amsa Masa tare da juyawa tana dosar d'akin su Dan Kiran Halee,Zaune ta iskota ta tsurawa gefe guda ido tana ta faman tsiyayar da hawaye gwanin tausayi hannunta dafe da kanta Dake mugun sara mata,Khady bata ce mata k'ala ba sai hawayen da ta share mata tana riko hannunta d'aya,ko ba,a fad'a mata ba tasan gurin da Khady zata kaita Dan taji Muryar sa,A hankali suke takawa har suka iso inda yake har yafara cin abincinsa,kallon Halee yakeyi cikin tausayi da soda kaunarta da yakeji har cikin ransa fiye da Yar cikin sa Khady.
" Sannu ya Furta mata cikin tausaya wa, bayan Karb'a mata barka da zuwan da take Masa,
"Meya samu fuskar ki ne naga kamar kwanciyar yatsu ajiki ga Kuma kwanciyar Jini acikin idanunki gefe da gefe, yakara tambayar ta bayan ta d'aga Masa kanta alamar yawwa.

💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )Where stories live. Discover now