*📲TYPING 📲 TYPING 📲 TYPING📲*
💤A MAFARKI NASANTA💤
I know her in my dreams
By
Faizah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔
🙌First lady🙌
-------------------------------------------------------------------
_Yar lelen Taskira _ --------------------------------------------------------------------
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
____________________________________________*بسم الله الرحمن الرحيم*...
*فيدك، ابي وامي يارسول الله (صل الله عليه وسلم)* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*Paid*📙*EPISODE*2️⃣
*PAGE*5️⃣📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
*@Arewabooks*
*@Faizatou**Wattpad*
*@Fai'zaMurai*
_________________________________________*Dan Allah kar ki fitar min da littafi,ni bazance Allah ya Isa ba,Amma Ina rok'on ku da Allah🙏wannan itace k'aunar da zaku nuna mini Yan uwa*_🥰🥰🥰
_*Ki biya ki karanta Yar uwa,ki Sha karatu anatse cikin natsuwar ki da k'ima da darajarki ta asali*_.🤩🤩
*Ki/ka Siya akan Farashi Mai sauk'i*
# N500 kachal
Sai ki tura ta wannan Account number d'in
*8069059746*
*Opay*
*Faiza Almustapha*
Sai ki tura shaidar payment dinki ta wannan lambar
*08069059746*_Na Facebook masu k'aramin waya zaku iya biyan kud'inku akwai PAID GROUP na Facebook,in ki/ka biya za,a Saka ki/ka aciki_..
DM.✍️Mutanen NIGER DA k'etare Kuna iya turo mini katin waya ta AIRTEL Numbata +234 808 750 4734 sai ki tura shaidar biyan ki ta numban.
🥀🥀🥀🥀❤️🥀🥀🥀🥀
A hankali ya yak'ara Furta musu na mance ban sanar daku ba anan ma nasamu aiki har nakai matakin ministan (C B I) na India na zamo shugaba a offishin.Cikin farin ciki da Al ajabi suka had'a Baki wurin Furta Masa congratulations uncle,murmushi yasaki Yana Furta " thanks you guys na Karb'a " murmushi Suma sukayi Jin yadda ya Kira guys d'in.
Fitowar su Lubna ne da Ziyad lokaci d'aya ya katse musu firar da sukeyi ta yaushar bo wadda ta Had'a da tambayoyin da yake musu akan masarautar da yadda kowa yake.gaba d'aya rankaya sukayi sai kan dining d'in da Aunty ta shirya musu shi.Lubna tsakiyar su Dr.Aj ta zauna shida Dr.Ammar Appah Kuma ya zauna agefe guda da Matar sa,su ziyad Kuma ajere suka zauna kujerun su na facing nasu Aunty Laila.Aunty Laila ce tayi saving d'insu,inda ta zuba wa kowa had'add'en girkin na shinkafa da Miyar kifi Wanda duka Rabin stew din manyan kifi ne tsage acikinta,sai Kuma pani puri da ta Had'a shaf shaf dansu Dr Ammar da Kuma dosa.
Ahankali kowannen su yake cin abincin sa cikin natsuwa,....
Dr.Ammar da Aunty Laila ta cika ma filet da shinkafa da Kuma wani filet d'in Mai d'auke da su pani puri ne ya Furta
" Aunty k'aramun ''yayi maganar cikin Rashin nuna damuwar sa Wanda shi zai tabbatar Maka da yadda yasaba da mutanen gidan tun asali.
D'an saurin kallon filet d'in sa tayi sai dai wayam d'an Abunda ke ciki Bai wuce spoon biyu ba murmushi tayi Dan batayi mamaki ba tun da tasan halin sa tun suna Yara,haka yake in anzuba musu Abinci bayan sun Chanye kowa Zai ce ya k'oshi Amma shi Banda shi,k'ara Masa tayi tana Furtawa aranta duk halin uncle d'in su ne ya kwaso na Rashin ragawa abinci.cigaba da cin Abincin sa yayi hankali kwance su Lubna kuwa har sun gama sun koma falo suda Dr.Aj,suna fira dashi, A hankali ya Ture fillet d'in daga gabansa Wanda iyaka Rabin da tasaka Masa yacinye Jin cikin sa ya cika yinwar da yakwaso a Asibiti Babu ta da wadda yake ta fama da ita tun kafin barowarsu Nigeria,Wanda sai alokacin ma yaji yunwar ta harzuk'o Masa,inda sallar Azahar kad'ai sukayi a Asibitin tun bayan Fitowar su operation d'in duk da anyo musu ordern Abincin k'in tsayawa sukayi su ci Dan suna son suje gida suci Abincin kukunsu da sukayi Marmari akwana biyu,Lemu ya tsiyaya na had'in kwakwa da Abarba da su kankana da Aunty ta Had'a musu Mai k'amshin dad'i,hamdala yayi tare da mik'ewa Yana barin kan dinning d'in bayan yasha lemun,Wanda ya rage daga Appah sai Aunty Laila ne a gurin.Bayan wucewar sa ne Appah yayi Murmushi Yana Furta " har yanzu babu Abunda ya chanza daga halayen sa,k'ara fad'ad'a murmushin sa yayi Yana Furta na matsu naga yadda Mai sunan Umma ta koma ayanzu Nasan tak'ara zama kyakkyawar zan kad'ed'iya kamar zuk'ek'iyar mata ta yakai k'arshen maganar Yana kashewa Aunty Laila ido d'aya,idanu tazaro ganin Abunda tayi tare da kallon falon ganin hankalin su Baya kansu sai ta samu kanta da sakar Masa murmushin ta Mai kyau Wanda yak'arawa fuskar ta kyau Wanda ya K'ara fito da Asalin kamar ta da da Halee dasu Unni,sai dai banbancin ta da Halee yarintar da ke ajikin Halee,mik'ewa tayi A hankali cikin Jin kunyar zancen sa Wanda Dama tagama Abunda takeyi shi kad'ai take Jira yagama ta kwashe komai ta gyara sa.yar k'aramar dariya yayi Yana kurb'a lemun data zuba masa sannan yabar dinning d'in Shima cikin murmushi da farin ciki.
YOU ARE READING
💤A MAFARKI NASANTA💤( I know her in my dream )
Художественная прозаHaka take ta faman Lilo da k'afafun ta tare da sakin k'ayataccen murmushinta,tana cigaba da binsa da kyawawan idanunta masu haske kamar wata k'aramar yarinya cikin Rashin damuwa tana k'ara fad'ad'a murmushin ta Wanda ke nuna Babu abun da ke damunta...