RUWAN DAFA KAI

18.5K 591 32
                                    

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

RUWAN DAFA KAI 1~5

Na SUMAYYA DANZABUWA

Agajiye tashigo palon nata kamar dai kullum,tana tafiya dakyar,takalmanta tacire masu uban tsini,ta watsar,sannan ta jefar da jakar kan kujera,ta cire mayafin dake jikinta ta rage kayanta,Ac ta kunna sannan tanemi waje ta kwanta duk da kuwa lokacin an fara kiran sallar laasar kuma tana ji.

Bata san sanda bacci mai nauyi ya dauketa ba,Horn din motar dataji anayi shiya farkar da ita,a zabure ta farka ta kalli agogon dake makale abangon palon taga karfe 7:30 na dare,"na shiga uku banyi laasar ba,(kamar koda yaushe)gashi isha tayi,"tace arikice tareda mikewa tashige bandakin dake palon donyin alwala.
Ko da ya shigo ranshi ne yabaci matuka kamar dai kullum,ganin ko ina kaca kaca ga kura kamar mutane basa rayuwa agidan,kamar ba satin daya gabata ba ya gyara gidan tsaf kafin yayi tafiya,bayan nasiha daya mata mai ratsa jiki akan tsabta,amma tasake haukata ko ina,ga kwanuka nan kan table Allah kadai yasan tun sanda suke,ga kayan ita kanta matar gida sunfi aqirga Allah kadai yasan tun sanda suke,dangin takalma mayafai da jaka ko ina,hardasu sarka,awarwaro da agoguna akan table din tsakiyar palon,bakin ciki ne da takaici suka kara turnikeshi kasancewarshi maaboncin tsabta wanda kuwa duk duniya ta shaida da hakan amma saidai kash matarshi kazama ce ta innaniha abin nata sai wanda ya gani.

Lekawa kitchen yayi yaga ko ta dora wani abu saboda yasan yafada mata yau zai dawo,duk da kuwa in ya kirata ma bata dauka tun kafin yayi tafiya takejin haushinshi,don haka ya tura mata text message kuma yasan tagani, ganin babu wasu alamun girki ko shirin yin hakan ne yasashi girgiza kai,tareda fadin"Allah ya kyauta"duk da dai girkin nata bawani damuwa yayi dashi ba daman kasancewar ba iyawa tayi ba,kawai dai yana ci ne saboda ba yadda zaiyi azauna lafiya,dakuma gujewa masifarta,yace taje wajen koyar girki shi ko nawane zai biya tace ya rainata yana gaya mata magana ita tafi karfin akoya mata girki,don haka ma tadaina mishi girki inya ga dama yayiwa kanshi tunda bata birgewa,anyi wannan lamarin ana sauran kwana biyu zaiyi tafiya,"wato tana kan bakanta kenan?"yasake cewa aranshi,domin kuwa ko shi yasan yafita iya abinci,yarasa gane wane irin girman kai ne wannan ace wai mutum bai iya abu ba kuma bazai yarda bai iya ba bare har ya yarda ya karu.

cikeda hanzari tafito daga bandakin,tazo ta wuceshi ta haye sama batareda ta nuna ma wai da mutum ba awajen,baki bude ya bita da kallo,shi dayayi sati daya baya gari amma irin tarbar dazai samu kenan?tunda ya tafi bata kirashi ba hasali ma idan yakirata bata dauka,anya kuwa yarinyarnan lafiyarta kalau?,ta kuwa san darajar aure bare tasan darajar miji?ya tambayi kanshi,dan karamin tsaki yaja gamida nufar nashi dakin ya shige cikeda takaici ya fada wanka.

Ba abinda yake bashi mamaki kamar wannan sauyi na Farida,tabi ta chanja gabaki daya kamar ba ita ba,du du du watansu shida da aure amma gida sai kace na mahaukata,uban kazanta,ya rasa wannan wace irin macece ace bazaka iya gyara inda kake zaune ba jikin ka ma sai ahankali agaskiya abin yafara isarshi kuma,tunda tadanyi tsabtar amarci shikenan kuma komai ya zama tarihi,ga girki bata iya ba hakuri kawai yake yana ci,kuma bai isa yamata nasiha ba,ita baacin gyaranta abinda takeso shi zatayi,babu abinda tasaka gaba sai neman kudi kamar wadda tarasa wani abu,iyayenta Allah ya rufa musu asiri,gashi shi mijinta shima babu abinda ya nema ya rasa,shikam dai yana cikin wani hali.

Yunwa tafara ji bayan ta idar da sallar hakane yasata saukowa tanufi kitchen batareda tabi takan mijin nata ba,kiciniyar dafa indomie tashiga yi don itace abarda tafikwarewa akai,farkon aurensu ba abinda take dafawa sai ita tun yana shiru har ya gaji yace indomin nan fa tafara isarshi shi duk lokacin baisan ita kadai ta iya ba,tunda yayi maganar nan kuwa tafara dafa shirme saidai ya faki idonta ya waske yaje waje yaci saboda abincin bazai ciwu ba ita kadai take iyacin kayanta,ganin hakan nema yasa yakasa kawo abokanshi cin girkin nata duk nacinsu kuwa,saboda shi yasan meke wakana.
Motsinta yajiyo yafito ya karasa kitchen din,tareda hadiye duk bacin ranshi,kamar koda yaushe,saboda bayason ya biye mata daga dawowarshi abubuwa suki dadi,zuwa yayi ya rungumota ta baya"my angel nayi missing dinki,ya kike"yace,banza tamishi,"shine kuma ko ki kirani kiji ya naje,naje lafiya ko ba lafiya ba shiru,babu ko dan text message,na kikkira kika ki dauka k...."nace komai lafiya haan"tabashi ansa atakaice,yar dariya yayi,wai don dai karya biye mata,"haba habibiya ta meye hakan kamar muna fada?menayi ne idan nayi laifi afadamin mana in bada hakuri"yace,"tsaki taja,"da Allah kasakeni malam,yunwa nakeji tun safe babu abinda naci,banida lokacin wayannan abubuwan"tace tareda kwace jikinta ta dauko tukunya,"to idanma nayi wani abin ne bansani ba Allah ya huci zuciyarki yabaki hakuri,me zaki dafa manane?"yace cikeda tsokana,"au yau kuma?mezan dafa muku?"tace cikeda fada "nazata cewa kayi ban iya girki ba?abincin nawa daba dadine dashiba meye amfanin indinga bata lokacina inayin abinda bazaa godemin ba,mtswww"taja dogon tsaki tareda bude ledar indominta,wannan halayya tata ya tsana domin kwata kwata bata iya magana ba kamar tana mantawa shi mijinta ne tsaki baya mata wuya,"Ni bance baki iya girki ba kawai gyara naso namiki s...."kaga kar kanemi ka rainamin hankali,wane irin gyara zakace zakamin saboda ka rainani?har ni za...."yanzu dai bazaki dafa abincin daniba kike nufi ko me?"ya ktseta,"ga abinda zan dafa nan daidai cikina idan zakaci ka dafa taka ai ka iya"tace bayan tamishi nuni da indomin,baki bude ya tsaya kallonta,ganin bata wani damuba da hakan yasashi girgiza kai cikeda takaici,kamar koda yaushe cikeda  hakuri da sonta ya fito ya dauki key din motarshi ya fita neman abinda zaici.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now