RUWAN DAFA KAI

3.8K 219 22
                                    

RUWAN DAFA KAI 96~100
Na SUMAYYA DANZABUWA

"Kinsan Allah saina nunawa yarinyar nan batada wayo,batasan nafita hauka ba,wai harni zata cewa idonta idona saitamin tsinannaen duka" farida take bawa sammy labari tanata hucin bakinciki da takaici,dariya ce taso kufcewa sammy tadan dake,don yadda farida take lamarin sai wanda yagani tabbas abin nata abin dariya ne,"nagaya miki abu amma kinmin shiru ko kice wan...."mekikeso ince,kinfi kowa sanin halinki farida abinda fa kikeso a koda yaushe shi kikeyi babu wanda ya isa yasaki ko ya hanaki,akan yarinyar nan babu yadda  banyi dake ba,amma kika ji,babu irin labaran daban baki ba akan ire irensu,saboda nasha ji tunda nidai ban taba maiaiki bama kinsani ai,saboda kin dauki aniyar kuntatawa  mijinki kememe kika kijin zancena kika dage sai ita,yau me gari yawaya?,alhakinshi  nefa"tacigaba da rubuce rubucenta,shiru faridan tadanyi nawani lokaci ko nazarin metake oho,"kina nufin dai kice laifina ne kenan?kawai don na dauketa aiki sh..."kinsandai bazan miki karya bako?to duk abinda ya faru ko ince yake kan faruwa laifinki ne,"cewar sammy  tareda dagowa ta kalleta,"ai ko hakkin mijinki ya isa yasa k....."mtsw bawannan fa nakeson ji daga gareki ba,wannan zancen ma ni ya isheni,"tabe baki sammy tayi"wanne kenan kikesonji kenan?"tacigaba da abinda take,"cewa nayi kimin kwatancen gidan da  daya shegiyar (naomi)take aiki tunda kince kinsani,"ikon Allah to sai kije kiyi me?"cikeda mamaki sammyn tayi maganar"kedai kiyimin babu ruwanki da abinda zanyi in naje tunda ke bazaki iya goyon bayana ba bankumace ki rakani ba"ta share hawayen daya zubo mata,don indai ta tuna zancen gloria sai ranta ya sosu,"to babu kwatancen  dazan miki kuwa,don bazan goyi baya ba inaji ina gani  kije ki aikata abinda zakizo kina danasani,so nake kibar maganar nan ki raba kanki da yaran nan,idan bakisani ba kisani  wannan(naomi)naji labarin ta ba karamar tantiriyar yariskar yarinya bace mara mutumci,duk gidan dataje sai an koreta saboda hada husuma,muguwar yarduniya ce na tabbata ita take zugo wannan din(gloria)take miki iskanci tunda naji ance aminan juna ne h...."nima yar iskar kaina ce ai"ta hayayyako,"idan sunayi sunacin bilis to wallahi bazasuyi akaina ba in kyale,kawai ki binciko min duk inda takoma ni bance ki rakani ba, don wallahi bazan kyalesu  s...."wai don Allah mexakyi musu?"don tana nema kuma ta kular da sammyn,"haba farida ya zaki dinga abu kamar wata irinsu? So kike kenan ma suga kina biye musu suji dadi duk ku zama daya kenan? suga sunata tunzuraki kina kara haukacewa kina biyemusu,"tafara maganar cikin rarrashi,"don Allah ki rabudasu don duk haukansu  da iskancinsu dai iyakarsu waya ai,wata shegiya ta isa tace zata tako tazo cikin gidanki tace zata miki ne?, ki bar maganar nan,idan kinga ansake kiranki da numbar dabaki  sani ba karki dauka,idan kuma kin dauka kinji sune ki kashe shikenan duk abinsu  ai dole  su daina"sammy harta gaji da rarrashin faridan yau kwana wajen nawa ana abu daya,zance yaki karewa,,"baa taba cimin mutumci ba kmar yadda yaran nan sukamin,har ni n....."nace kiyi hakuri haba,"sammy tayi kwafa,dakyar dai aka samu farida tabar zancen ganin abokiyar tata tadaina sauraronta amma fa ta kuduri niyyar duk ranar dataga yarinyar saita bata mamaki.

"Hajiya Gashi wancen mutumin  ne yace inyiwa girman Allah da Annabi muhammadurrasulillahi in baki"maigadin shagon data fito ya miko mata kati irin complimentary card dinnan,"waye shi?"wancen mai shaddar ruwan kasa"yamata nuni dawani mutum a jikin mota,kodata kalleshi mayen nata tagani,hakan ne yasata jan tsaki  kamar koda yaushe "jahili kawai mahaukaci"tayi tafiyarta,"Hajiya,Ha...."maigadin ya biyota kafin ya karaso tashige mota taja,shikuma mayen yana jingine ajikin tashi motar,yana kalon duk abinda yake gudana,"Yallabai  gashi wallahi taki karba"yace tareda mika mishi,ya karba yasa a aljihu yashiga mota yabar wajen,duk abubuwan datake mishi bai taba sawa ranshi ya baci ba bare yace wai zai hakura da ita,hasalima akullum soyayyarta kara karfibtake acikin zuciyarshi,shiyasa ya gwammace yadinga jurewa duk wani wulakanci nata anashi  tunanin wata rana zata saurareshi har ta soshi itama.

Yusuf da Abu kullum sabonsu kara gaba yakeyi,dukda dai Abun na kaffa kaffa,a kullum tsoronta kada farida ta isketa tana mata magana da miji,don idan yana gida har zama suke sudan taba hira don ahalin daake ciki yasan labarin garinsu,gidansu,iyayenta da dan abinda baa rasa ba,malam kuma yana nan yana zuwa sunata karatu abindai gwanin ban shaawa,a irin sakonnin daya saba tura mata kowane dare yau yayi shahada  harda I lov you don yana ganin  lokaci yayi dazai fito mata da kudirinshi game da ita karara,boye boyen ya isa haka tunda dai shine mai gida bawai tsoron kowa yake ba.
Koda Abu taga sakon saida zuciyarta tabada wani daram don ta dade tana shan jinin jikinta akan hakan amma kuma bataso ta tabbatar ita ya zatayi yanzu?,"mamaki ne yahanaki turomin ansa ko kinyi bacci?"yasake tura mata,"to yazaayi ma yace yana sontawai,?wannan wane irin so ne?yusuf yafi karfinta nesa ba kusa ba,shiyasa kenan duk wanda zaizo neman aurenta, saiya koreshi ashe yanada nashi  kudirin,ya ilahi,wayyo Baban Amin meyasa yafara sonta alhalin ita tasan bazata taba sonshi ba,ita da ahalin daake ciki ma batasan metake  ji ba game dashi don bata taba doyayya ba baretasani  ko tafara sonshi ne itama  ko  kuwa akasin haka,kuma ma duk abar ta wannan tayaya zasuyi zaman kishiyoyi itada farida?farida fa?idan aka cire masifarta da bakin halinta,macece iyaka macece,don Abu rabonda taga mace mai kyau haka tamanta,indai ba yanada wata manufa ba tashi takanshi me zaiyi da ita?me matarshi ta rasa da ita zata iya bashi?wasu hawayene masu zafi suka fara zubo mata don hakika tana cikin tsaka mai wuya,wannan wane irin abu ne?ya zaayi tana yar aikin gida maigida yace yanasonta?me mutane zasu  dinga tunani akanta kenan?taci amana?daga zuwa aiki ta kwace mijin matar gida?labarin datakeji yau kanta ya fado kenan?agaskiya bazata iya ba gwara ma idan barin gidan ne tayi.
Ganin shirun yayi yawane yasa yusuf dan shiga damuwa amma shima dama yasan  dole zaayi haka ai don abune dabata taba zata ba,kasa nutsuwa yayi dole yasauke kan farida dake kirjinshi tana ta minshari harda yawun bacci yafita palon saman don  kiran Abu,saida ya kira sau uku tana tsinkewa ana hudun tadauka  yanajin muryarta yasan sanaar  tata take ta kuka,"don Allah kiyi hakuri zainab nasan abinnan yazo miki bazata amma wallahi dagaske nake tsakanina da Allah nake son ki kasnce matata wallahi ban fada miki abinnan ba don in bata miki rai"kuka tafashe dashi,wanda harsaida tadan ruufe bakinta donkarta  tashi Amin,"kiyi hakuri kidaina kukan  nan kinsan banaso yana damuna kicemin wani abu ko naji dadi"yace a marairaice,dakyar ta iya  hadiye kukan tafara magana,"nagode da kulawarka da soyayyar dakace kana  min amma bazan iya aurenka ba baban Amin"kafin yayi magana takashe wayargabaki daya kiran duniyar nan wayar akashe, dole ya hakura yakoma daki yakwanta cikeda damuwa yanata fatan  Allah yasa dai ta aminta dashi  don shi yanzu idan tace bazata aureshi  ba baisan yazaiyi ba tabbas yariga yagama macewa da sonta hakika zai shiga wani hali.
Cigaba da kukan tayi mai kunshe  da dalilai  iri iri.
Ganindai baccin bazuwa zaiyi ba tana cikin tsananin  damuwa dole ta tashi tashiga ta dauro alwala tazo tafara salloli,tareda rokon Allah yakawo  mata mafita don tasan wannan wata masifa ce take shirin samunta.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now