RUWAN DAFA KAI

4K 201 8
                                    

RUWAN DAFA KAI 71~75
Na SUMAYYA DANZABUWA

"Hajiya kamar fa akwai abinda yake faruwa agidnnan?yusuf dai bayason fada ne kawai"cewar Asmau bayan sun kama hanya?"wane gidan?"Hajiya tace cikeda rashin fahimtar zancen don sun biya gidan wani kawunta dasuka baro gidansu yusuf din,"Haba ashe dai ba ni kadai na lura ba,yusuf fa akwai abinda yake boyewa yaron nan,kullum naganshi a firgice yake duk yabi ya ufita hayyaci,tunda yayi aure duk yabi ya chanja kamanni ana ganinshi ansan yana cikin damuwa amma yayita musawa"Aisha ta kara, "Au sai yanzu nagano inda zancen naku ya dosa ai,Amma meyasa kuka ce haka?"hajiya ta katsesu,"Nifa inaga matar nan tashice take gana mishi azaba Hajiya,don idan kika lura dashi zaki gane baa nutse yake ba"hmmm da gaskiyarku to amma ya zanyi dashi na tambaya na tambaya yacemin babu komai komai lafiya,saima matarshi datake yawan kawomin kararshi,akai akai kwana biyu dai banganta ba bansani ba ko lamuran haihuwar ne suka sha mata kai,"ta kara,"kunsan Halin yusuf da hakuri da kau dakai,ga dauriya tun yana dan karaminshi ba mutum bane dazaizo yace muku ana mai badaidai ba ko wane da wance sun mai kaza,mutumin dayake ansa laifikan wasu bayan bashi ya aikata ba wai don azauna lafiya ko kun manta?banda na saitashi ai da tuni ya dade da tsunduma kanshi cikin matsala,ban fiya damun kaina bane da lamarinshi da matarshi saboda nasan halin maza,zai iya yiwuwa abinda take fadamin din gaskiya ne tunda dan adam ne shi,zai iya chanjawa akoda yaushe,amma koma dai menene Allah ya kawo sauki yakuma bayyana gaskiya"Amin sukace dukansu suka cigaba da yan hirarrakinsu.

Tunanin Aunty ne yafado mishi,farida tace ta tafi,to amma kuma ai ba yau sukayi da ita zata tafi ba,hasalima baa saka ranar tafiyar ba,dama shine yaketa matsawa saita kara kwanaki don tun wajen sati biyu dasuka wuce tace zata tafi ya hanata ya roketa,ita kuma gani take kamar tana takura musu kuma ga faridan ta warware,tana kuma gudun kada tazo wani abu yashiga tsakaninsu tunda ta lura da take takenta."Anyankuwa?"yadinga nanatawa aranshi don yasan Aunty mutum ce mai faranfaran ga mutumci da kirki baa cewa komai,idan da tafiyarta yau ta lafiya ce ai koba komai dai zata mishi sallama,shima yakara mata godiya,tunda ga abubuwan daya sissiyo nan zai bata.
kasa nutsuwa yayi yanata fatan dai Allah yasa ba abinda yake tunani bane aranshi na cewar farida tamata hali(saboda yadda yaga faridan dazu yasha jinin jikinshi)wayarshi ya dauko yafara lalubar lambar Auntyn amma shiru,bama ta shiga,shidai yanata fatan Allah yasa lafiya gashi dare yanayi kuma ko gidanta baisani ba don basu taba zuwa ba dama iyakarsu da ita waya.

Haka rayuwa tacigaba da kasancewa agidan kullum yusuf dai yanata hakuri farida tana cigaba da iskanci,saukin daaka samu ma shine Amin din yafison madara nonon bai dameshi ba,kuma itama hakan yamata dadi don dama tadade da yanke hukunci idan ta haihu wata shida zata shayar kawai don bazai yiwuwa nononta yazama kamar slippers,da iliminta dakomai tazama jagwal,hakan ne yasa idan tanajin haushi shiga daki take ta kullo kanta batareda ta muna damuwarta ga yaron ba nako yana jin yunwa ko bayaji saboda tasan zaisha madara,dama zancen wankanshi da duk wani abu nashi Abu ce,saidai dan abinda baa rasa ba don kusan rabin kayan shi ma suna dakin Abun,tunda ita take wankesu,ita take mishi komai yusuf yana matukar jin takaicin hakan,don ya tsani yaga uwa nanuwa dan data haifa rashin kulawa,lamarin farida kuwa har yau yakasa gane mata yau zata nuna babu abinda takeso sama da danta gobe ta nuna bata damu dashi ba,ga yaro kullum wayo yake karayi.

Ba yadda yusuf baiyi ba akan farida tagaya mishi abinda yafaru Aunty ta tafi kememe taki fada daya matsa sai cewa tayi rufeta tayi da duka haka kawai,"duka kuma ita Auntyn dakanta?"ya nanata,tareda jinjina zancen"ita din fa to meye na mamakin kai fa don bakasan halin matar nan bane shiyasa har kake wano damuwa da ita,ai ba abanza kaga naki sakin jiki da ita ba tun farko ai saboda gudun irin haka ne tunda ni nasan hali,duk hakurin danayi da ita,duk juriyar danayi,kuwa ashe saita bani mamaki" tace,"to amma meya hadaku da har zaa kai ga duka,ni shine abinda bangane ba"meye kuwa ya hadamu ni nama manta meya faru,kasanta dai da nuna isa dason mulki,"ita Auntyn yaushe?ban taba lura ba ni"ya katseta "bazaka lura ba dama,kaga ni bama nason mudinga maganar nan abinda yafaru yariga ya faru kawai amanta a wuce wajen"tace tareda tashi tabar palon"hmm wanda baisan farida ba wallahi tagama dashi,ni har me zaki fada in yarda dake?nima fa ba kyaleni kikayi ba,wai macen dazataje ta hadani da uwata tamin sharri akan abinda bansan hawa ba bansan sauka,nasan karya take itama tasan nasan karya take,wai kuma itace zata fadi wannan shashancin tayi tsammanin zan yarda da ita,tabdi ada kenan"yace aranshi tareda murmushi afili,lokacin yayi daidai dajin karar shigowar sako wayarshi daukowa yayi ya duba,yaga Aunty ce ya bude"Sallama yagani,sannan yan gaishe gaishe,yusuf inata kira bana samunka ya kuke dafatan kowa kalau"a take yatura mata ansa"Duk muna nan kalau Alhamdulillah kituro min address dinki don Allah"ya tura don zancen ba na waya bane,ko minti biyar baayi ba kuwa ta turo mishi da ansa.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now