RUWAN DAFA KAI

3.9K 233 25
                                    

RUWAN DAFA KAI 116~120
Na SUMAYYA DANZABUWA

Koda kaya suka isa gidansu Farida,jaraba da masifar datayi Allah kadai yasan yawansu,bawanda ya kulata don lokacin babu kowa ma agidan,sai sauda haka tasha bakinciki ita kadai,"wato haka yusuf ya kagu yayi aure ya rabu da ita kenan?,dama ashe ya dade da tsanarta zaman gulma da munafurci kawai yake da ita yaki gaya mata har saida tagano don kanta,to inba haka ba wane irin abune wannan da bama zai iya jira tazo dakanta ba,daga yin abin jiya,shine zai kwashe mata komai ya aiko mata?wannan fa yana nuni dacewar ya tsaneta iya tsana kenan,da har baya kaunar yaga wani abu nata,hmm,to idan ma wai yana tunanin shikenan tadawo gida kenan dazama to kuwa zaisha mamaki,don itama nan bada dadewa ba zatayi aure ko ta halin kaka,don dolene ta muzguna mishi yafasan cewa bazatayi kwantai ba idan ya gaji da ita ya daina sonta akwai wayanda zasu karbeta hannu bibbiyu,ita har agaya mata farin jini ma,itada tun tana budurwa ake rububinta har tayi aure baa daina yayinta ba,aikin banza ma kenan,tacigaba da mita.

Batareda wani bata sauran lokaci ba yusuf ya tada ginin daya fara da yabari,don so yake ayi komai agama cikin kankanin lokaci babu wani amfanin ayi jinkiri Allah ya rufa mishi asiri.
Soyayyarsu shida Abu kullum karuwa take,tabbas ta tabbatar yanzu tana sonshi kwarai da gaske,don tana zaune saitayita tunaninshi,musamman idan yadanyi jinkiri bai kirata ba ko ta kirashi bai dauka ba tayita damuwa kenan,idan hakan tafaru takan saka hotunanshi gaba tayita kallo( wayanda yasako mata awayar dawayanda yake tura mata a watsapp don basuda aiki sai turawa juna hotuna tun tana jin kunya harta saba)tabbas sai yanzu ta kara jin tausayin farida don ba karamin rashi tayiba,samun namiji irin yusuf abin sai an tona,don adan kwanakin nan da yusuf yake nuna mata tsantsar soyayya ta fuskanci wane irin mutum ne shi ,zata iya cewa irin namijin nanne buri ko mafarkin kowace ya mace amma farida duk ta watsar da hakan saboda tsananin yi wa kai da rashin rabo tabbas zatayi danasani.

Kafin kuce meye wannan gini yayi nisa to harkace ta kudi,kuma duk step din daaka dauka saiya tura mata (Abu) tagani ko ya mata,dukda dai bata taba cewa wani abu bai mata ba don ita aganinta bata isa ba,amma hakan baisa yayi kasa agwiwa ba don ko tiles da penti saida ya tura mata hotuna akan tazaba taki kamar koda yaushe ganin ya nuna mata bacin ranshi ne yasa ta daure tazaba a karo na farko don ta faranta mishi,saboda yusuf ya mata komai bai cancanci bakantawa ba daga gareta ko da wasa,kuma duk abubuwan dake faruwa ganinsu take kamar a mafarki wai yau ita Abu ce har ake nunawa ginin katafaren gida mai bene,ana cewa in ya mata,abinda yamata shi zaayi wanda bai mata ba a chanja,kai lallai rayuwa abin mamaki ce, yadda Allah yaso haka zaayi duk saurin mutum,dabara ko dagewar mutum akan abu sai Allah ya nufa zai faru ita dai babu abinda take a kullum sai godewa Allah da wannan baiwa daya mata babu zato babu tsammani.

Cikin kankanin lokaci aka hada lefe,na gani na fada,akwatuna goma sha shida yayi ganin yayi goma sha biyu lokacin farida kuma ya yasha alwashin saiya ninka mata komai fiyeda wanda yayi lokacin farida,don lokaci yariga yadade dayi da mutanen duniya yakamata su gane cewar wani kayan lefe dawani kyautatawa badole sai yayan masu kudi ba kawai,aa yayan talakawa ma zasu iya samun irin hakan,su samu sauyin rayuwa,duba da yadda lamuran duniyar nan suka zama na kwarya tabi kwarya,yayan masu kudi su auri junansu su kara wadata da daukaka, yayan talaka suma su auri junansu su kara talauci su dawwama a ciki,ayita rayuwa babu sirki tayaya zaayi mu taba cigaba idan mukace zamu cigaba ahaka?.wannan dalilin ne ya karawa yusuf kaimi,don shi Allahn dayayi shi mutum ne maison kyautatawa baya kyamar talaka,yakuma kijinin yaga ana wulakantashi,tunda shima mutum ne dan Adam.

Kafin kuce meye wannan,an gama shirya komai da komai,Tafiya kai kaya ma an shirya dayake ma dai duk mazaa ne a harkar babu mata,gudun gutsiri tsoma don babu abinda zai hana mutane yin magana,na farko dai anhada wannan uban kayan,na biyu,maiaiki wai zaa kaiwa kuma yar kauye,kunga kuwa ai abin magana ne dole,saidai idan anki gaskiya,to gudun hakan ne yasa Hajiya tace maza ne zasu kai asaka rana ayi komai a wuce wajen.
motoci sukayi kusan nawa,shida bash ne agaba Amin yana bayan seat,suna tafe ana hira har aka karasa.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now