RUWAN DAFA KAI

3.6K 297 24
                                    

RUWAN DAFA KAI 141~145
Na SUMAYYA DANZABUWA

Suna zaune bayan sallar ishai,Ya kira Hajiya donsu gaisa,bayan sungaisa dinne take shaida mishi cewar fa ga dansu nan yatadawa jamaar gida hankali tun dazu yake rigima,da har zata sa akawoshi dazun to kuma sai yayi barci,yar dariya yayi,"to ai yamayi kokari Hajiya,don tun jiya ma ni nake sa ran kiran naku ai,bakomai idan Allah yakaimu gobe inshaalah zamuzo sai mu tafi dashi"yace yana yar dariya,haka dai suka cigaba da taba hira inda Hajiyar tadinga jaddada mishi hakuri da kai zuciya nesa azauna lafiya kar taji karta gani,itama Abun baa barta a baya ba don saida Hajiya tace abata wayar itama don mata tata nasihar.

"Kinaji fa danki yanacen ya tubure"yace bayan ya kashe wayar,yar dariya kawai tayi,don batasan mezatace ba,tunda dama itama a kage take ta ganshi don ba yadda zatayi ne kawai,bataso tayi magana aga rashin kunyarta ko rashin kara amma dan kwanakin nan datayi bata ganshi ba Allah kadai yasan halinda ta shiga ita ba abin tace akawoshi ba ko aje a dauko mata shi,tunda dole da nauyi wajen Hajiya yake,kuma ma zaa iya cewa ta zake shiyasa tayi shiru ta hakura har sai sanda aka dawo dashi din ko shi yusuf din ya daukoshi,tunda ita Hajiya gata tamusu saboda su samu su sake shiyasa tace abarmata shi acen.
Cigaba sukayi da kallo, abinsu cikeda so da kauna suna dan taba hira kafin daga bisani su tafi bacci.

Abubuwa dai nata tafiya yadda farida takeso,don a halin daake ciki ma Su Abdallah har sun kawo kudin aure an saka rana nan da wata biyu dukda dai taso taga wata biyun kamar shekara biyu,taso tayi magana sai dai tabawa zuciyarta hakuri tadaure kar yace tafiya mita ya fasa.
Kuma yace ba lefe,shima bidia ne amma yayi alkawarin idan ya aureta sutura sai irin wadda takeso.

Tabbas farin cikin datake ciki bazai misaltu ba wane aurenta na fari,?tunda lokacin aurensu da yusuf zuciyarta bata kai haka lalacewa ba kuma batada wata mummunar niyar bakantawa wasu amma yanzu inaa abubuwan sun chanja sun shallake hankali tazama tantiriyar mai bakin hali,kafin kuce kwabo tafara duk wasu gyare gyare da shirye shirye irin na amare,Abba kuma yayi order kayan daki da sauran tarkace gida wayanda ta zaba kamar dai wancen lokacin(aurensu da yusuf).
"Yanzu shikenan saboda baason gaskiya daga haduwarki da mutum sai a saka rana?shin hakan ya dace?har yaushe ma kuka gama sanin juna?ke bakya ganin wani laifi a tattare da abin ida shi (Abban)ya biye miki ne don ya faranta miki?wannan wace irin rayuwace kuka zabarwa kanku?"cewar mama cikin wata murya mai dauke da tsantsan nasiha"mama ni so nake kicire duk wasu tunanika daga ranki donAllah,kiyi fatan alkhairi kawai,wallahi Abdallan nan dakike gani mutumin kirki ne,don dai baki zauna das....."duk kirkinshi shikenan k......"wayyo Allah na,"ta katse manan,"wai meyasa duk abinda nakeso shi kike tsana?nifa yanzu ba kamar da bane mama ni bazawarace nafa taba auren nan nasan yadda abubuwa suke,na girma,idanuna sun riga sun bude shiyasa ma nasan wane irin miji ne yadace dani don Allah kibar irin wannan zancen"tace cikeda kaguwa don ta gaji dajin wannan nasihar kullum abu daya,"ni bawani abu nace ba,rayuwa tariga ta chanja mutane babu wanda zaka yarda dashi rashin gaskiya y......"kasa kai aya maman tayi sakamakon matsanancin kukan karyan da faridan ta fashe dashi"to Allah ya sawwake,kije kiyi duk abinda kikeso"ta tashi ta barta.
"Hmm wai wannan wane irin zancene da maman nan zata wani matsanta sai an zurfafa bincike? wayake wannan a zamaninan?tab"ta tabe baki" gashinan yanzu da baa matsa ba anyi abinda zaayi amma da ance zaa biye ta tata datuni baa kaiga haka ba,irin wannan ne ma zaa takura ayita bin kwakwafi har mutum yaga takurar tayi yawa ya gudu nikuwa bawannan nake fata ba atoh "tayi zancenta afili,tareda daukan waya takira rabin ran nata,abin mamaki tunda aka saka musu ranar daga ta kira yake dauka yadaina jan ajin hakan ma ba karamin dadi ya mata ba.

Tun bayan Dawowar Amin yusuf yaso ya daukowa Abu mai aiki koda dattijuwa ce tunda har wajen ajiye maiaikin ya tanada just in case,amma taki kememe,saboda aganinta idan ta yarda da hakan kamar zata kasance mace mara godiyar Allah ne ita kam metake nema yanzu a rayuwarta?duk wani rufin asiri da gata Allah ya bata to mezatayi dawata mai aiki,wacece ita?tayi ma ada wanda bai zama wajibinta ba bare yanzu dazata samu lada?kuma ma da yaushe tagama yiwa wasu dazaace itama zaa kawo mata,babu yadda baiyi da ita ba akan ta manta da baya komai ya wuce amma kememe taki,harda kuka,dole ya hakura ya kyaleta don tace babu abinda zai gagareta a gidan zata iya komai kula dai da Amin dama tasaba ai.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now