RUWAN DAFA KAI

3.6K 238 15
                                    

RUWAN DAFA KAI 126~130
Na SUMAYYA DANZABUWA

Koda suka shiga basu zame ko ina ba sai dining table,inda aka shishirya abinciccikan da Hajiya tasa a aiko musu,tabbas dayawa dukda dai su Gwaggo ma sunci.
zaunar da ita yayi kan daya daga cikin kujerun, dinnig table din,sannan yashiga kitchen ya dauko musu  plate,abinciccika ne kala kala kowanne da flask dinshi,tambayarta abinda zai zuba mata yafarayi bayan ya lissafo mata komai,ta girgiza kai alamun ta koshi,rabuwa yayi da ita yacigaba da zube zubenshi,ya hada mata tea,saida duk yagama sannan yaja kujerar dake kusa da ita  yazauna yajuyo da ita yadda suke fuskantar  juna har lokacin batabar hawayen ba "kiyi hakuri kibar kukan nan haka kinji muci Abinci don nasan yunwa kikeji"yace bayan yadebo soup din naman a cokali zai kai mata baki,kallonshi tayi taga yadda  yayi narai narai da ido saikuma suk yabata  tausayi itama,haka ta bude bakin yadinga  ciyar  da ita don batason tayi mishi musu,"kai bazaka ci ba"tace dakyar ganin sai bata yake shi baya ci,"zanci amma nafiso yar amaryata  tafara koshi tukun"yadda yayi maganar ne  yasata dan murmusawa,"ko kefa gashi dakikayi dariya  harkin kara kyau"yace cikeda zolaya itadai shiru tayi saida takoshi tukunna ya dakata sannan yace  tazuba mishi nashi,ba musu ta tashi ta zuba ta ajiye mishi ya bita da kallo,"like seriously?"kallonshi tafara cikeda rashin fahimta,"banganeba"tace cikin sassanyat muryarta,"hmm dole kiki ganewa ai tunda kinci kin koshi,wato ni ba dangatanki bane kenan,"sunkuyi dakai tayi don tagane abinda yake nufi,"shikenan dama baso kike inci ba indai hakane"cikin sanda ta  dauki cokalin tana debowa kamar mara jini ajiki,"hmmm ina jira fa"yasake cewa tareda nade hannunshi a kirjinshi donma wai tasan cewar fa  bashida niyar ci din dakanshi don ya fuskanci dasauranta sosai dole ya dorata akan hanya shi dan soyayya ne,ita kuma komai kunya yake bata amma dai ahankali zaisan yadda zaisata tadinga sakin jiki dashi,yar dariya tayi cikeda jin kunya sannan tafara bashin cikeda nutsuwa,yanata janta da hira wai don duk ta wartsake don baya kaunar ganinta cikin damuwa,saida yakoshi shima sannan ta dakata,tareda tashi  don fara gyara wajen saboda bata kaunar ganin waje a hargitse kwata kwata,riko hannunta yayi,hakan ne yasa ta juyo takalleshi,"wai gyarawa zanyi naga duk m..."bakyson hutu baby na kefa amaryace ko kina mantawa da  alqawarin dana miki nacewar zan shagwabaki? dagaske  nake fa,kiyi zamanki ki huta ni zan gyara tunda nima ai na iya yafara hada kan kwanukan,"da dai k..."saifa na gyara  komai duk abinki naki wayon kije ki zauna ki huta"yamata nuni da kukerun dake palon dama tv a kunne take,ganindai da gaske yake bazai barta tayi aikin bane yasata hakura ta nufi kujerar ta zauna,juyowa tayi tasake kallonshi ya mata gwalo hakan ne yasata yar dariya,remote tadauka tafara chanja channel tana neman abin kallo don tanason kallo abinta,"kai anya kuwa abinda  tayi yakamata?ace tabar mijinta da gyare gyare shi kadai ai aikinta ne,ita datake fatan kasancewa mace tagari"wata zuciyar tace da ita,hakan ne yasata binshi kitchen din da ragowar kwanukan dazai dawo ya dauka,"ni ban taba ganin mutum mai gudun hutu d....."aa wallahi"ta tari numfashinhi tun kafin ya karasa"zan tayaka,sai muyi tare"tace bayan ta ajiye kwanukan cikin sink din,"dats my baby inye ashe dai yarinyar badaga nan ba,irin soyayyar nan,irin dinnan,haka akeso"yace cikeda sonta yacigaba da tsokanarta don yusuf mutum ne mai son wasa da tsokana amma farida dole tasashi yazama wani iri don batason duk abinda yayi da wasa ganinshi take gaske ita ta chanja maana dole ya hakura,don  bakomai yake gaya mata ba saboda azauna lafiya shes too serious.

Haka kuwa akayi yana wankewa tana kifewa tana goge wajen ana yar hita,harsuka  gama suka fito,inda aka ajiye mata kayan turare ta nufa ta dauko coal tashiga ta kunno tasako a wata hadaddiyar burner ta turaren wuta,hakan ne yasa yusuf jin dadi don tabbas Abu itace abokiyar rayuwarshi saboda abubuwansu dayawa sunzo daya,zama sukayi 3 seater suka fara kallon wani American movie the equallizer,ganin tadan takure gefe ne yasa shi janyota jikinshi ya kankameta,tayi luf abinta.

Masu karatu lamarin farida fa yazama abin mamaki  duk inda tasan sun taba haduwa da mayenta take bi wai ko zata samu wanda yasanshi ko inda zata sameshi don wallahi ita yanzu shi kawai takeso dukda dai bata wani ji irin muguwar soyayyar nan tashi aranta ba amma dai koba komai yanada kyau yanada  tsaho kuma daga ganinshi mai kudine haka  takeson namiji yakasance,shiyasa zuwan yusuf wajenta karon farko ta aminta  dashi saboda duk qualities  din datake bukata a namiji,yana dasu.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now