RUWAN DAFA KAI

4.2K 238 6
                                    

RUWAN DAFA KAI 16~20
Na SUMAYYA DANZABUWA

Haka Yusuf yacigaba da hakuri dazaman gloria agidan nasu,Farida ba abinda take sai karo wulakanci,wai ita matar so ganin yusuf yana kyaleta tana abinda taga dama,kasancewar cikin nata bata wani laulayi batashan wahala hakan  yasa ba abinda tafasa dangane da fitarta aiki dasauransu,tadai rage saka dogon takalmi sakamakon gargadi da likita tamata dataje awo,bataso hakan ba kwarai dagaske don sharudan daaka dinga kafa mata ba adadi,komai sai ace ta kiyaye ita kam wannan cikin fa yana neman ya hanata rawar gaban hantsi.
kullum kafin ta tashi gloria tagama mata girki tayi gyaran gida,daduk abinda ya kamata,haka zata dawo abinci yana jiranta,idan yan mutumcin suna kanta azauna ayi hira da yusuf inya dawo idan kuma ya kuskura yamata nasiha ko yafada mata gaskiya to fa komai zai sauya,haka dai ake rayuwar  kullum,shidai saidai yasha shayinshi,dama yakai komanshi daki,idan yatashi fita yasaka key yarufe kofarshi,donma kada gloria tace zatayi giggiwar shiga ta gyara mishi,abinci kuwa saidai yaje waje ko wajen Hajiya,don tun ranar dayaje wajen bash yadawo bai kara yiwa farida zancen gloria ba,harkarshi kawai yake,yana nuna shi baima san da ita ba,ita kuwa gloria tanata bangaren kullum da tunanin yusuf take kwana tske tashi,hakan nema yasa kullum idan zai fita ko ya dawo saita dan labe a kitchen inyazo wucewa tadan kalleshi taji dadi,amma  itama lamarin farida yafara isarta,saboda agaskiya duk gidajen datayi aiki a baya bata taba ganin kazamar matar gida masifaffiya irin farida ba,hakan nema yasa take tausayin yusuf don adan zaman nan datayi ta fuskanci hakurin zama da faridan yake kawai.
"Wai lafiyarka kalau kuwa?kullum idan kazo sainaga rama a tattare dakai na tambayeka kacemin komai lafiya,meyake damunka ne?"Hajiya ta watso mishi tambayoyi,bayan yagama cin abinci rana,"babu komai lafiyata kalau,"ansarshi kamar kullum dai"karya kakeyi,lafiyar taka kalau shine kullum kake tsomarewa?"yaufa saifa ka fadamin abinda kasa aranka?"Hajiya ta titsiyeshi,nan ya kwashe komai yagaya mata tas,tun daga zuwan gloria gidan har yau amma fa har yanzu bai taba mata zancen bakin halin farida ba,"yanzu fisabilillahi da wannan dalilin ne yasa duk kabi ka fita hayyaci?yau ni naga ikon Allah?"cewar Hajiya,anya kuwa yaron nan lafiyarka kalau bawata matsala bace dakai?"matsala kuma Hajiya"yace cikeda rashin fahimta,"toh matsala mana,inba haka ba menene hadin zaman mai aiki da ramar ka?kawai saboda tsananin tsabta saika nemi ka susuce?dama nasan zaa rina ai tunda kanuna baka kaunar zuwan mai aikin nan tun farko,h..."wallahi hajiya bahaka bane,kamar yadda nafadamiki dinne,ni inda ace musulma ce wallahi bazan damu ba amma kasancewarta k....."wannan duk ba dalili bane"ta katseshi,kamin zancen bazata iya girki kaci ba,wato shiyasa ashe kake sintiri kullum agidannan ashe abinci kake zuwa ci?"Hajiya abinnan duk ba yadda kike t...."yusuf"hajiya ta katseshi,"naam"yabata ansa,"Don Allah don Annabi kadaina saka abinda baikai yakawo ba aranka ni ina jiyemaka ne kar wani ciwon yazo yakamaka,meyasa bazakaji tausayin matarka bane?yarinyar nan ciki ne da ita ga aiki datake zuwa dame zataji?don kawai ta bukaci mai taimako shikenan masifa taki karewa?kasawa ranka ruwan sanyi mana,kayi hakuri,"Hakane,zan cigaba  da hakuri,"kawai yace ganin cewar fa Hajiya bazata taba gane lamarin nan ba,shiyasa ma take ganin laifinshi a kullum,amma bakomai yasan komai daran dadewa gaskiya zatayi halinta.

"Ni kuwa inataso in tambayeki yaya yarinyar nan kuwa(gloria)dafatan dai komai kalau,uhm ko da yake ma nasan hali inda bakwa zaman lafiya datuni kin kawo kara,"sammy tace da farida gamida tabe baki,"komai kalau fa ai yarinyar nan akwai iya aiki nikam nasami machine kema tunda kikaji nayi shiru ai kinsan komai zanzan"tace tareda yar dariya,"au haba kinajin dadin zama dai da ita kenan?"eh gaskiya balaifi don ma dai rannan taso ta zakemin amma tunda na taka mata birki shikenan,"nan farida ta kwashe duk yadda akayi ranar  da gloria ta tashi karbar kayan yusuf,dariya sammy ta dingayi,"birgeta yayi kenan "kawai tace,"hmm haukanta dai,ai a lokacin naci mata  mutumci na mata tatas  ina gaya miki"uhm saiki kula dai karta kwace miki miji"cewar sammy tareda cigaba da rubuce rubucenta,"tab wane mijin?indai wannan ne ai gata gashi,da tasan tsanarta dake cikin ranshi hm"tace tana dariya sanin halin  gogan nata don tasan komeye zai faru babu abinda zaiyi dawata gloria.
"Hmmm kidai kula karkisha mamaki,saunawa anayin hakan?"sammy tasake cewa,"uhmm abu mai yiwuwa shi ake sawa arai har ace zaa kula"farida tabata ansa,"Nace ba?"uhm inajinki",mai zai hana ki chanja yarinyar nan ki kawo irin wadda mijinki yakeso farida,bawan Allahn nan yanada hakuri fa yadda kike gayamin halayenshi nasan tabbas yana tsaka mai wuya irin mutane haka masu  jarabar tsabta sai ahankali bakya ganin kina shiga hakkinshi?"ke kyaleshi  dallah bawani damuwa dayayi,sufa mazan nan haka suke  kullum burinsu su dai  ayi abinda sukeso,su kuwa  basu damu da abinda mace takeso ba toh ni kuwa idona yariga yabude nasan ciwon kaina  nasan me duniya take ciki don hakane ma nasha  alwashin babu namijin dazan taba bari yarainani aduniyar nan h...."Nidai kinsan bazan daina fada miki gaskiya ba,namijin dakike magana fa bawani bane,illa mijinki,mijine fa ba saurayi ba,farida Allah yasa kinyi saar miji  mai hakuri mai sonki,amma duk baki gode ba kenan,wasu matan fa hakan suke fata basu samu ba suna cen gidan miji anacin ubansu kuma dole suyi biyayya,su zauna don su rufawa kansu asiri,amma ke don kinga gata yamiki ya...."tuntsirewa tayi dawata muguwar dariya hakanne ma yasa samira kasa karasa zancen ta tsaya kallonta,"hmm abin dariya yake baki kenan?to ki kula  dakyau dai ki lura ki kiyaye  kidaina zalumtarshi,"mtsww zancenki kenan kullum,wai don Allah ta yaya nake zalumtarshi? ke in tambayeki ke in kece a matsayin danake yanzu mexakiyi?cewar farida,"kinfi kowa sanin  abinda Zanyi ai,nimai kaunar  abinda mijina yake kaunace  mai kuma kiyaye abinda yace bayaso,"mtsww banza sai kiyi tayi ai,ke kikaga zaki iya gashinan kinsa miji ya rainaki,haka zaki gama shan aiki anan kidinga rawar jiki zakije kiyi girki saboda karki bata ran  miji kamar baiwar daaka siyo,ni har namiji  ma ya isa,?tab"eh naji,kada Allah yasa ke ki gyara idan bakiyi ba zai samo wadda zatayi mai ai"tab yusuf ai inbani ba sai rijiya,ke shifa ba irin wayannan mazan bane dakike tunani,bazai iya rayuwa babu ni ba ni nasani h...,"kina bakanta mai ran?sammy ta katseta,"to bari kiji ingayamiki inma baki sani ba kisani wayannan abubuwan dakikeyi na nuna bai isa dake ba kina rasshin mutumci kina  rashin kunya wallahi dasannu zaiji kina fita aranshi,saboda kuwa kowane danadam yanason kyautatawa,h...."saidai ke ki fita daga ran naki mijin nikam nida yusuf ai mutu karaba, tace hadeda dan murmushi"hmm Zamu gani dai  cewar sammy.
"Am tellling u oh?if u see dis guy chaaiiii"!gloria take cewa kawarta Naomi a waya yayinda take bata labarin yusuf,naomi tanata son tazo wajen kawartata amma farida tariga ta gargadi gloria akan babu zancen kawo kowa,itama kuma inda ba Sundays ba datake zuwa church bata yarda da yawo ba,"me kike jirane just steal d man,where are those sexy dresses of yours?kifara sakasu mana"cewar Naomi,"hmmm i wish,but this wicked woman is making me dress like a reverend sister all the time,i no fit show boobs and ass again oo,hmm"chaii,ya zakiyi kenan,zaki zaunna ne bakiyi komai ba akai,?"inji naomi,"to ya zanyi naomi,i dont even know what todo again"tace cikeda muryar tausayi,"and what annoys me the most is that she cannot even cook,shes very dirty,and evil,inkinga yadda take treating guy dinann,you wont believe your eyes,"to ke ga opportunity ma,mtsw what are you waiting for again"inji naomi,"hmm i dont want to start misbehaving oo"gloria tace,"idiot stay there"inji naomi,"to yazanyi,kinsan i need dis job dat is why i dont want to..."I know,please save me the explanations,just try and seduce d man"cewar naomi,"hm u wont understand but i know am seriously inlov with dis guy aswear,"i laugh in pidgin,"inji naomi tareda kyalkyala dariya,"then  snatch d man"its not dat easy abeg,he dosent like me,kona mai magana baya ansani baya kallona,and worst of it all idan nayi girki baya taba ci he hates me"tace cikin wata murya mai ban tausayi hakika naomi  ta fara tausayawa kawar tata matuka domin kuwa bata taba son wani namiji ba sai yusuf gashi dai daga yadda take ganin lamura babu abinda zai yiwu,amma dai zata kokarta wajen ganin ta taimaki kawar tata wajen cinma burinta don a yadda ta fuskanci abin farida dosent deserve him he deserves better.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now