RUWAN DAFA KAI

4K 233 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 21-25
Na SUMAYYA DANZABUWA

Tunda Naomi takarfafawa gloria gwiwa akan jan hankalin yusuf gloria ta dage wajen ganin tacimma burinta,dama idan Farida ta fita dasafe su biyu take bari agidan,kuma hakan bai taba damunta ba don batada wata fargaba,ga yusuf sai wajen sha daya yake fita, hakane yabawa gloria damar saka matsatstsun kayanta datazo dasu,wayanda tafara sawa tun farkon zuwanta kafin farida ta hanata a tunaninta ko zata birge yusuf har ya kamu da sonta amma ina kamar kullum idanunshi kara dakushewa suke suna makancewa in tana guri.
A kullum takan matse jiki gata dama ba laifi a dire take,tanada duk wasu abubuwa/surori na jikin mace dazasu iya jan hankalin namiji fuskartata cedai sai ahankali don tubarakallah Allah yamata muni,daba don muninta ba Allah kadai yasan mazan dazasu mace akanta,a koda yaushe Farida tana barin gidan zata shige daki ta shiryo taci uwar kwalliya saita daidaici lokacin fitowar yusuf saita zo ta zauna a palon bayan zaman palon ma farida ta hanata,amma matukar bata gidan abinda taga daama takeyi,ko sau daya yusuf bai taba nuna wa ma wai yana ganinta ba bare yasan wai metake sakawa ajikinta,ko metaje nufi,tunda shidai bawai abinci zai tsaya ci ba idan ya sauko zai fita bakuma zama yake ba a palon,kama hanyarshi kawai yake ya fita,duk da kuwa a kullum bata gajiya saita gaisheshi ta mishi adawo lafiya amma ko ansata bayayi tunda ya lura da taketakenta amma hakan bai taba sawa ta gajiya ba,sannu dazuwa ne dai bata samuwa domin matar gida tana nan kuma tasha ja mata kunne indai mijinta yana gida karta dinga ganin ko gifcinta indai ba ita ta kirata ba.
Duk abinnan daa ake shima yusuf din ko sau daya bai taba yiwa farida zancen ba na cewar wai gashi gashi abinda gloria takeyi idan ta fita saboda bashida wannan lokacin ba abu bane daya shafeshi,tunda ai bashi ya kawota ba,bakuma zamanshi take ba,zaman farida takeyu, harkar ta ita ta shafa shi babu ruwanshi dukda sai shiyake bada kudin aikinta,baima zama lallai ma ta yarda ba idan ya fada mata halin daake ciki,yasan hakinta zata iya cewa saboda bayason zamanta ne zai mata sharri,shikuwa yanzu akan gloria dai yariga yagama magana don babu abinda zaisa ya sake tada wani zance kuma,kansu akeji daga ita har uwar dakin nata.

"Anya kuwa ba fitowa zanyi fili ba nafadawa guy dinnan abinda nakeji araina game dashi?idan nacigaba da shiru fa soyayyarshi zata iya kasheni!"gloria take zancen zuci,bayan ta yiwa yusuf adawo lafiya yakama hanya ya fice batareda ya kalle taba kamar dai kullum,"hmmm ki fada mishi kawai,to ma meye aciki just confess your love for him,"tasake cewa afili,wayarta ta dauko suka fara chatting da Kawarta Naomi,sannan take tambayarta yaya labari ya ake ciki,nan take gloria tafada mata halinda ake cikin take kuma neman shawararta akan abindatake shirin aikatawa,"hmm gloria gaskiya nayi supporting hakan karki wani wasting time,I know your courage I trust you,gobe idan ta fita dasafe ki samu ki fada mishi duk feelings dinki game dashi kinji,baki sani ba ko shima yana feeling same,"naomi tace da ita,"inata tunani ne naomi wannan wani irin namiji ne duk abinda nakeyi don in dau hankalinshi baya gani kuma ni nasan nafi wannan stupid matar tashi komai,(banda dai kyau gloria)kawai dai ignoring dina yake saboda yana tsoronta"tace,"karkiji komai ni banaso ki rasashi ne,don ya hadu da ina blaming dinki dakikayi falling for him but after kinmin sending wannan pic din sai nadaina saboda naga abinda kika gani(hoton su shida farida faridan tasaka a dpn watsapp dinta hakan ne yabawa gloria damar saving tareda yanke faridan yazamana akoda yaushe idan tana tunanin yusuf saita dauko wayarta tadinga kallon hoton don dai tasan inbanda ta wannan hanyar babu yadda zaayi tace tasamu hotonshi),dahaka dai suka gama hirar akan cewar washe gari gloria zata aiwatar daduk abinda suka yanke shawara akai saidai kuwa duk abinda zai faru yafaru don ita ba tsoron farida take ba,kuma besides she is not even a good wife.
"Yusuf nakeso nadan leka kwana biyu,kuma dazu inata kiran wayarshi shiru,"Bash yake cewa Amina,"oh Allah sarki ai kuwa dai kwana biyu baizo ba watakila baya kusa da wayar ne in kaje kace ina gaidasu dukda ma dai fushi nake da farida,na gayyaceta biki batazo ba kuma ko kirana ma batayi ba"cewar Amina,"kinsan dai harkokinku na mata sai ahanakali watakila itama bikin ne da ita,ko aiki yamata yawa,kinsan dai ba irinki bace da kullum kina gida"yace cikeda tsokana don yayi yayi da Amina tacigaba da karatu tace wanda tayi ya isheta,meye amfanin tadinga barin mijinta cikin damuwa,bata so tashiga hakkinshi ko kadan kuma sau dayawa mace tanayin aiki ne don ta kula da kanta yanuwanta dasauransu ita kuwa Alhamdulillah ta gode Allah babu abinda ta rasa ladan aurenta ya fiye mata komai,"hmm kaima kasan yadda na damu dakai ai a kullum cikin godewa Allah nake daya bani miji irinka babu abinda ka rageni dashi to meyasa zan takurawa kaina bayan kana kyautatamin? kaga ai nima yakamata ace kullum cikin faranta maka nake ko?"eh hakane kam Allah yabarmu tare shiyasa nake kara sonki wallahi kinsan yakamata Allah yamiki albarka"murmushi tayi cikeda kaunarshi sanan ta rungumeshi,"nace mai zai hana ki shirya muje tare"ina din?"ta tambaya,"gidan yusuf",hmm honey kasan dai nayiwa farida kokari ko tunda sukayi aure fa sau daya ta taba zuwar min nayi mitar harna gaji,kuma naga sai nunamin alamu take kamar batason kawancen nan dani kaduba fa kaga tunda akayi auren su Allah kadai yasan sau nawa naje mata nice kiranta a waya tura mata text message amma sau dayawa bazata dauki wayar ba kuma bazata kira ba text dinma bata reply,ni ina ganin kawai ayi nesa nesa zaifi a hakura kawai,"tace dashi cikeda nutsuwa ba wani tashin hankali,akoda yaushe hankali da nutsuwar amina su suke kara sawa tana birgeshi yanakara sonta har yake ganin ma babu namiji yashi aduniya domin kuwa yasan yayi saar mace,"bakomai baby kiyi hakuri kar kice saboda bata nemanki ko bata zuwa inda kike shikenan kema bazaki nemeta ba baa haka,kiyi hakuri kinji hakuri ake"yace tareda murmushi itama murmushin tayi "toh shikenan mijina bari inshiga sai in shirya" tace ta tashi.

Ko da yusuf yafito daga wanka ya dauki wayarshi yaga bash ya kikkirashi a take ya kirashi shima,"ina kashige ne"cewar bash din bayan sun gaisa,"ina wanka ne wallah ya akayi ne?"ya ce,"najika ne shiru kwana biyu gamunan ma ahanya nida madam zamu lekoku"yace,saida gaban yusuf yadan fadi saboda tsoron kada suzo farida tayi wani rashin mutumcin don ba kara bace ta isheta tunda tariga tace batason harka da Amina to fa babu abinda zaisa ta chanja hakan,"hello kajini kuwa"bash din yace jin yusuf bai bashi ansa ba,"eh najifa netwrk ne sai kunzo"yawwa bash din yace ya kashe waya.
Yana cikin shiri tashigo dakin,zata dauki computer,
"Yanzu bashir ya kirani suna hanya z..."shida wa?ta katseshi tun kafin ya kai aya"shida matarshi mana"ya bata rai,don yaga yan balain na kanta shikuwa yau daidai yake da ita"hmm wajenka zatazo kenan?don inda wajena zatazo ai yakamata ace ni zata kira,(kamar inta kira tan zata ansa ne)"narasa gane natsalar mutane wallahi ,wai yaushe zaa wayene?mtswww matsalar rashin ilimi kenan komai ..."yarinyar nan fa babu abinda ta miki meyasa ne bazataci koda arziki na bane?wai ke ko kara baki sani bane?amma dai koba komai ai kinsan yadda nake da bash ko?ko kuwa angaya miki idan kina zagin ta ko sauran matan frnds dina inajin dadi ne?t.....ai dama kullum nice nakeyin ba daidai ba,ban isa infadi laifin wasu ba kullum nidin dai nice,ita yanzu datayi jahilci baka gani ba kenan?tace tareda daukan computer tayi hanyar fita,"tunda wajenka zasuzo sai suyita zuwa,tunda kai suka shafa kuma wallahi karka kuskura ma kace ina nan don idan kace zaka matsa dawani zancen sai an gaisa wallahi tallahi sai na baka mamaki,"ke!wai meyasa bakida tunani ne bakida hankali?ko don kinga ina miki shiru duk iskancin dakike na zuba miki ido?wallahi ki kiyayeni kada ki kuskura kinkaini bango halayenki na rashin tarbiyya da rashin mutumci sun fara isata kuma,"heyye,ah lallai, ma wato duk akan wayannan jahilan kake zagina kana gayamin magana to walahi nima ka fara kaini bango don na fuskanci baka tashi wulakantani sai anyiabinda yashafi abokanka ko matansu,n...."bata karasa ba wayar yusuf tafara kara wanda tun sanda yagama magana yake shiri yana saka kaya,yana daukan wayar yaga bash ne alamun sunzo kenan,har lokacin farida bata bar masifa ba hakan nema yasa bash din danson yajiyo abubuwa.
"Yanajiyo kamar ana fada"cewar Amina wadda itama da wayar baa kunnenta take ba saida tajiyo masifar farida,"nima dai naji amma dai nafi zaton ko tv ce"cewar Bash,"to inaga tace,sannan suka fito suka jera suka shiga ciki.
Haka ya barta tacigabada masifa batareda ya sake cewa da ita uffan ba,don yasan ayau dinnan idan yacigaba da biye mata wallahi babu abinda zai hanashi nada mata tsinannen duka tunda ita batasan mutumci ba,haka tacigaba da balai har tana kuka tana cewa sai dai yazaba kuwa ko ita ko abokananshi da matansu tunda babu wanda yaraina duk duniya sama da ita.
Bacin ranshi ya hadiye ya sauko tareda murmushi a fuskarshi,wai don karsu fuskanci wani abu,waje yasamu yazauna sannan suka gaisa,saida aka kusa minti 10 sannan gloria ta fito daga daki,wai taji anyi baki bari tazo takawo ruwa kar tasha masifa wajen farida tace batasan meya kamata ba,"Amina da mijinta kallo kawai suka bita dashi,cikeda mamaki sai yanzu bash ya kara fuskantar halinda yusuf yake ciki lokacin dayaje mishi da zancen yarinyar(gloria),hira suka fara kafin gloria ta fito da ruwa da lemo,fuskarta cikeda murmushi ganin cewar babu farida a wajen,ko kallonta yusuf baiyi ba bare har ya dakatar da ita kasancewar hankalinshi bama anan yake ba,ranshi ne yaketa kuna,"wannan kuma fa?"Amina tace bayan glorian tashige dakinta,"mai aikinsu ce"bash yabata ansar atakaice don ko wancen karon da yusuf yabashi labarin komai bai fadawa Amina ba ganin cewar yariga da ya kwantarwa da yusuf din hankali yabashi hakuri,"madam din bata nan ne?"bash yakatsewa yusuf tunani wanda hankalinshi kwata kwata inda yake daban tunninkala kala yake kawai,shi bashir yasan ba lafiyarshi kalau ba sarai kallo daya ya mai ya fuskanci damuwa a tattare dashi,"bata nan taje gida "kawai yabada ansa,"au bama tanan ai kuwa da banzo ba,"cewar Amina.
Nan suka zauna aka fara dan taba hirarraki yusuf yanataso yadan saki jikinshi amma ranshi abace yake daurewa kawai yake,kuma bashir sai tambayrashi yake ko ba lafiya ba,yace komai lafiya kawai dai baya danjin dadi ne,jin an bugo kofar saman damugun karfi kamar zaa karyata shiyasasu duka dan razana,tunda ance bata nan,"lafiya dai?"bashir yace,kafin yusuf yabada ansa Farida ta sauko fuska duk hawaye ta janyo dan akwatinta,kallon kallo Amina da mijinta suka farayi,yusuf kuma ya sunkuyar dakanshi don yasan yamusu karya,kuma ahalin daake ciki ko ganinta bayasonyi,babu wanda ta kalla awajen saima muguwar harara data watsa musu dukkaninsu tayi hanyar fita,"ina zaki?"yusuf din ya watsa mata tambaya?,"banza tamai taja tsaki tabude kofar palon tayi fitarta,"wai meke faruwa ne "cewar bash,shiru kawai yusuf yai mishi,yabarshi yanata tambaya,"ka tashi kabita mana naga ranta abace kar taje tashiga wani hali,"ai shine ka bita don Allah "cewar Amina,duk ta rikice,"ku kyaleta ta tafi babu inda zan bita"kawai yace musu,hayaniyar da gloria tajiyo ita tasata lekowa ganin komee faruwa,babu yanda su bash basuyi ba akan ya bita ya tsayar da ita amma kememe yaki don ranshi yariga yagama baci,shi bashir dinne ma yatashi dasauri jin maigadi na kokkarin bude mata gate kafin ya fita kuwa tafigi motar aguje kamar zata tashi sama.
Wani dadine ya kashe gloria,kamar kamar me,shikenan yanzu zataci karanta ba babbaka,dole yusuf yazama mallakinta.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now