RUWAN DAFA KAI

3.7K 348 24
                                    

RUWAN DAFA KAI 121~125
Na SUMAYYA DANZABUWA

Ana idar da sallar laasar su Ango yusuf aka fara shirin juyowa saboda gudun kada dare yayi musu a hanya Ga Dinner da aka shirya zaa gudanar da misalin karfe takwas.
Abu ansha kukan rabuwa dasu Baba,bawai don bata taba barin gida ba kowani abu, aa sai don sanin wai gidanta zata tafi, gidan aurenta,don ko farkon zuwanta gidansu yusuf saida akayita fama,saboda mutum ce da bata son barin gida ko da wasa,lokacinma  don abubuwa sun tsananta  ne agidan nasu,ba yadda zatayi  shiyasa,fada kuwa da nasihohi ta shasu harta gode  Allah,ita kuka su Baba kuka,dahaka aka rabu suna shi mata albarka damata fatan alkhairi.
G laure dawasu yanuwan nasu dabasu wuce mutum biyar bane aka taho tare dasu rakiya dakuma ganin  inda zata zauna.
Yusuf yaso ace mota daya zasu shiga shida ita,Amma ina kafin yagama sallama da jamau,ya karaso ya tarar yanuwanta sun sakata a tsakiya shikuma  tsananin kara da kunya yasashi kasa magana,dole ya hakura,don indai girmama na gaba dashi ne ba wasa,haka yashiga tasu shida bash da Amin yadda sukazo suka kama hanya.

Basu shigo gari ba sai bayan  Maghrib,ko daaka karasa gidan Amarya bakin jamaun daaka tafi dasu kasa rufuwa yayi saboda tsananinmamaki don ko tangamemiyar gate din gidan abar a kalla ce,haka zalika dasuka karasa cikin gidan,sunji mata dadi kwarai da gaske,don su ba makiyanta bane,masoya ne na kwarai masu kaunarta tsakani da Allah,hakika suna tayata murna kwarai da gaske"chab,yo wannan gida ai shine aljannar duniya ke kuwa Abu kin huta abinki Allah ya baki Allah yasa gidan zamanki ne ya kauda fitina"shine kawai abinda suke cewa.
ya Asmau suka tadda don Aisha bata gari da wasu yanuwansu yusuf din agidan dasuka zo tarbar amarya,inda suka samu kyakkyawar tarba,don sun karbesu hannu bibbiyu abin sai wanda yagani.

Dakin daaka saukesu suka shiga,suka bar Abun da su Ya Asmaun don yadda suka ga sunata nan nan da ita abin gwanin ban shaawa,tabbas Abu tayi dacen miji da dangin miji,Allah yasa adore  sukace bayan sun shiga,tabbas dakin nasu shima ya kawatu sai kace na amaryar.
suna zaune suna hutawa  ne daya daga cikin matan  dasuka tarar tashiga ta sanar dasu cewar fa su shirya akwai  liyafa daa ka shirya wa Ango da Amarya,yar dariya G laure tayi,"to ai mu ba saimunje ba ko don bamu masan zaayi ba"aa ku kuwa dai ai kwaje bansan ya akayi ma bai sanar daku ba tun acen din kai yusuf akwai shiririta fa shima wani lokacin",tace tareda yar dariya,suma suka dan murmusa,"ku shirya don Allah Zainab bazataji dadi b itama idan bakuje ba,ga lokaci yariga ya tafi"tajuya tafita,"to Allah yasa dai cikin kayan nan naku kun taho da abin kirki"G laure tace dasu bayan ta fita,"ah bazaa rasa ba"sukace tareda janyo jaka"zamuzo birni kema dai kinsan ai mazo da sabon dinki"sukace sannan akayi dariya,kafin kuce kwabo sun chachanja sun shirya,ba laifi dai kunsan mutumin kauye yan atampopinsu suka saka,kuma dama dukansu manya ne babu wasu yanmata acikinsu,don duk yanmatan dangin nasu sunyi aure Abunce dama kawai  ta rage kuma gata batada ko kawaye.

Abu kuwa tana cen,har anyi nisa dafara tsantsara mata kwalliya don musamman aka dauko wata shahararriyar mai kwalliya data kware akan aikinta kowa kuma yasanta,wato masu karatu duk wanda yasan Abu ada,yakuma ganta da kwalliyar nan karyarshi yace ya ganeta don wani sheki take tana walwali,tasha irin  eyeshadow dinnan mai walwali,da daukar ido, ga wata winged liner daaka ja mata kamar da ita akayita tsabar tsaruwa,hakika tayi wani mugun kyau,ita kanta data ganta amudubi saida tadan tsorata.
yusuf ne yasake shigowa karo nawajen nawa kenan tun fara kwalliayar  yana cewa ayi sauri an riga an makara already sai waya ake mishi don yaga kwalliyar tana daukan lokaci,"ka rabu damu mana kai kuwa muyi  abinmu  a nutse kadaina azalzala ko bakaso tayi kyau ne?"cewar yaya,"so kai,ai tariga tayi ma,mashallah fa tabarakallahu Ahsanul khalikin"yace bayan  sun hada ido da ita,tayi mai wani fari dayasashi rikicewa don wani mugun kyau datayi ga Eyelashes din sun karawa idanunta kyau,"ko kunya"Yayan tace dashi,"toh mutum da matarshi"kalamanshi ne yasa kowa nawajen dariya,Abu dai kuny taji,shima yar dariyar yayi yajuya ya  fita.
ko da  aka gama kwalliyar wani dakin suka shiga inda yaya ta dauko wata riga doguwa maroon datasha  ado,sai kyalli take tana sheki,ku kuna  gani kunsan wasu makudan kudin aka kashe anan,don bama a nan Nigeria aka dinka ta ba,shiga rigar tayi don bazaace sawa ba takuwa fito das da ita,kamar ajikinta akayi dukda dai ba fitted bace,saida tagama saka rigar yaya ta gyaggyara mata sannan suka fito mai kwalliyar  tamata dauri irin turban dinnan yayan  dakanta tasaka mata sarka da dankunne dasu Abin hannu da agogo don haka kawai takejin son yarinyar da kaunarta,ga nutsuwa da kunya,tun ranar dasuka farazuwa tamusu girki taji tabirgeta tun lokacin tafadawa su Hajiya tayiwa kanin nata shaawar kasancewarta matarshi to ashe dai ashe shima ya dasa,"Abu kamar ba ke ba ni laure lallai wato kwalliayr nan tazamani mayar da mutum take wani daban,jibi yadda idanunta suka kara girma nikam "cewar g laure bayan sun shigo,"wallahi kuwa ikon Allah" sauran sukace ita dai  Abu ba abinda take sai dan murmushi don dama bata fiya magana ba kuma ma ai dama manya  ne mezatace musu,"hotuna g laure tayiyyi mata don idan ta koma tanunawa su gwaggo dasauran yanuwa.
Wani takalmi kirar Christian Loubuotin mai shegen kyau,dakuma uban tsini,yayan ta dauko da yar jakarshi irin wadda amare suke rikewa,ganin Abu ta zaro ido fuskarta dauke da damuwa da tsoro ne yasa  yayan dakatawa,"Zainab tsoro yabaki haka?Ya miki tsaho ne dayawa"?gyada kai tayi alamar eh,"chab ta ina dama zata iya hawa wannan takalimin  tserere,ai yayi tsaho dayawa wannan ai saita karye" daya daga cikin gwagganin nata tace,"bazata karye ba ai,ki gwada kinji zaki iya bazaki fadi ba kinga angon naki mai tsahone sosai,ko ke bakyaso ki dan kamo shine"Yayan tace tana dariya tareda kokarin kakaba mata shi akafa,"Nidai tsoro n...."shiru tayi bayan sun hada ido da g laure taga ta galla mata wata  harara,don ta tsani kauyanci,"ki gwada mana akace kigani idan kin kasa ai ba dole saiki cire,amma baki gwada abu ba kice bazaki iya ba"ta kara,dakyar zuciyarta na harbawa kamar zata fito waje,ta tashi tana rirrike  antin cikeda tsoron karta fadi,"jeki bangon cen ki dawo mugani idan kin kasa din sai a chanja"bangon ta tafi ga mamakinta saitaji kuma ashe dai zata iya gashi bata ko gurdewa kawai dai tsahon takalmin ne a zahiri mai tsoratarwa amma gashi data sakashi  kamar bata saka komai ba,jinta take dai kamar a tsauni gawani tsaho data kara,murmushi tayi"zan iya dai ashe"hakan ne yasa dukkaninsu dariya.
Fesheta akayi da turarruka kala kala masu dadin kamshi,aka kawo dan mayafi aka dan yafa yadda dai amare sukeyi,aka fara hotuna.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now