RUWAN DAFA KAI

4.2K 212 25
                                    

RUWAN DAFA KAI 101~105
Na SUMAYYA DANZABUWA

Dakyar take tukin,saboda tsananin azabar datakeji ,don ba karya jikinta ya gaya mata ta daku ainun,ko dayake ma to ita tunda take arayuwarta waye yataba mata irin wnnan dukan?Wani matsanancin kuka tabfashe dashi afili,don tama rasa meke mata dadi wannan wane irin cin mutumci ne da tsantsar raini?yara su sata a loko su mata shegen danbanzan duka  kamar sun sami samfur?,shikenan haka zasuci bilis kenan?hakika bata taba zaton duk tantirancin Da Sammy ta ke fada nasu yakai haka ba,aikiwa ta rantse bazata kyalesu ba saita sa yan sanda sun kama yaniskan sun rufesu rufewa ta har abada.

Saura kadan ta karasa gida,kawai taci birki dukda dakyar take tukin don bama sosai take ganin gabanta ba sakamakon tsatsagewar da gilashin gaban motar yayi,tana tunani ko dai ta wuce gida kawai(gidan iyayenta)don yanzu idan takoma yusuf sata gaba zaiyi yayita mata tambayoyi kamar dan jarida dole sai yaji kwakwaf,ita kuwa batasan irin karyar dazata shirga ba don bazata taba fadar cewar Gloria bace tamata wannan danyan aikin,to gidan ma inkinje meye?dole fa atambayeki jibeki fa kamar wadda aka tono"wata zuciyar tace da ita,kallon kanta tayi taga yadda tayi budu budu,tabbas zuwanta gidababu wani sauki dazai kawowa lamarin saima fada dazata sha a wajen mama,don Abba ba abinji bane yanzunnan zata tsarashi ta dorashi ya hau yayi derere,mama kuwa baa wannan shashancin da ita,bari kawai tayi gidan, tunda yusuf dai saita ga damar yi mishi magana ma duk nacin tambayrshi kuwa,ai hawanta titin keda wuya taje ta daki wata tanker datake a parke,saboda rashin nutsuwar datake ciki,kafin ta ankara wata motar tazo ta daketa da mugun karfi take ta sume,mutumin baiko tsaya ba ya falla aguje,sai mutane ne aka taru don dubawa ko tana da rai duba da yadda motar tayi abindai sai wanda yagani.

Yusuf kuwa yana cen gida yana fama da Abu ta bashi ansa tace yayi hakuri bazata iyaba ita gida zata tafi yanata magiya,baiko damu da rashin dawowar farida ba dukda kuwa dare yayi don yasaba da hakan saitaga damar dawowa idan tayi dare irin haka ya kirata ma bata dauka don kar yace tama ina tadawo gida shiyasa hankalinshi a kwaance kamar koda yaushe  lamuranshi kawai yake.
Fakar  idonshi Abun tayi tashige daki ta rufo don tagaji da magiyarshi kullum zance daya abu yakici yaki cinyewa,yakuma kasa dena wahalar dakanshi acewarta saboda aganinta da tunaninta wannan abune dako amafarki bazai taba yiwuwaba.
wayarshice tafara kara alamun shigowar kira koda ya duba farida yagani,"toooh su madam,,mekuma akeso?ko meya faru?"yace tareda daukan wayar da sallama,"munga numbarka ne awayar wannan baiwar Allahn,yanzunnan tayi hatsar......"innalillahi wainna ilaihi rajiun,"ya katse mai bayanin,tareda sandarewa,"mun kawota asibitin kusa da wajen da abin yafaru wani Better care saika hanzarta zuwa don halinda take ciki sai addua,"nagode ganinan"cewar yusuf duk jikinshi yayi sanyi.

A hanzarce yadauki key yakama hanya yana zuwa ya wuce emergency inda akace mishi  an kaita,saidai babu yadda baiyi ba akan abarshi ya ganta aka hanashi don tana cikin irin critical condition dinnan,waje yanema kawai ya zauna tareda dafe kanshi yana adduoin Allah yasa dai komai yazo dasauki,yana nan azaune  har kusan awa nawa likitoci nata aikin shige da fice,daya daga cikinsu ne yazo yasameshi yamishi bayanin yadda aka kawomusu ita,sannan kuma ahalain daake ciki  zai iya shiga ya ganta"Alhamdulillah"yafara cewa sannan yayi mishi godiya yashiga "ya ilahi! innalillahi wa inna ilaihi rajiun inda badon yasan  farida  ba aida bazai ganetabba kamanninta gabaki daya sun chanja tayi waniniri ga kayanta dasukayi daka daka ko meya faru oho?wannan wane irin hatsarine"?yusuf  wayannan tambayoyin ita kadai ce zata iya bada ansarsu,wata zuciyar tace dashi.

Abba yafara kira sannan yamishi bayanin komai,inda hankalinshi yakai kololuwa wajen tashi,sannan ya kira Hajiya itama haka,kafin  kuce meye wannan kowa ya garzayo masu kuka nayi masu addua nayi don duk wanda yaganta a wannan yanayin dakyar ne bazai zubda kwalla ba.
Haka aka dinga tambayar yusuf akan wai yaya lamarin yakene?wannan wane irin hatsarine haka?"wallahi ina gida aka kirani dazun nan nima bansan ya akayi hakan tafaru ba"shine kawai ansar dayake bayarwa.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now