RUWAN DAFA KAI

3.6K 213 16
                                    

RUWAN DAFA KAI 136~140
Na SUMAYYA DANZABUWA

Ko datazo bacci ma saida tasake kiranshi wai dondai ta tabbatar mishi fa ba wasa take ba,yakuma san tana sane dashi,amma bai dauka ba hakan ne yasata tura mishi text message mai dadi cikeda kalaman soyayya,tana mai mishi saida safe,ita kanta wani lokacin idan tana abubuwa takan bawa kanta mamaki,wai yau ita faridace dakanta ta nemi numbar wani namiji wai har ita tafara kira ma,ko ina jan ajin nata oho?hmm tabbas babu abinda son zuciya baya saka mutum,wato idan kanason cimma wani buri a rayuwa idonka rufewa yake,kayita abu ba saiti,shiyasa hausawa suka ce sakai yafi bauta ciwo,amma bakomai yanzu itadai duk bawannan bane damuwarta,don ashirye take tadauki duk wani rainin wayo ko wulakanci daga Gareshi indai har zata cimma burinta shikenan inyaso duk abinda zai biyo baya ya biyo,idanunta arufe suke ayanzu bata gani,don yazama dole ta dage kuma duk hanyar dazataga tabi wajen ganin tariritashi tareda nuna mishi soyayya ita zata bi saboda karta rasashi, zatayi kokari matuka wajen ganin ta boye dukkanin mugayen halayenta don karya fasa,zatakasance mai tsananin ladabi da biyayya yadda koda alumma sun kawo gulma akanta bazai taba yarda ba tunda bahaka yasanta ba.

Haka dai tacigaba da latse latsen wayarta tana tunane tunane har tayi bacci shiru babu reply,bata wani damu ba,don tasan dasannu komai zai daidaita kuma manyan mutane irin wayannan dama communicating dasu sai ahankali.

Washegari ma saida ya rigata tashi,ahankali yadinga gudanar da lamura wai don karya tasheta,saida ya kimtsa tas sannan ya sauka yashiga kitchen don hada musu breakfast,tunda yace Yau basai Su Hajiya sun kawo ba.

Kodata farka bata ganshi ba,hakan ne yasata shiga ta fesa wanka,don garau takejinta,bayan ta fito kuma tayi yan shafe shafenta,su mai da yan turarruka masu dadin kamshi tasha hoda da dan jambaki,don harta dan fara sabawa dayin kwalliyar dukda dai bawani iyawa tayiba.
wata doguwar riga blue tasaka mai sheki,tasaka hijab sannan ta dare dadduma don gudanar da sallar walaha,kodata idar yan adduoi tazauna yi sannan ta tashi,ta gyara gadon,ta dan kimtsa dakin dukda dai bawani datti yayi ba, ta yafo dan mayafinta tasauko.

Tun daga stairs kamshin girkin nashi yake dukan hancinta,a hankali ta karasa kitchen din taganshi yabata baya dagashi sai singlet da 3quater harda Apron ya takarkare yana suyar dankali yana dafa kayan ciki,cikin sassanyar muryarta tafara gaidashi,"aa,my princess,har an tashi"yace bayan ya ansa sallamarta da gaisuwarta,dan murmushi tayi ta gyada mishi kai alamun eh,"karaso mana,ya jikin naki"yasake cewa cikeda nuna kulawa,hakan neyasata jan mayafinta ta rufe fuska don a take yasata tuno komai daya gudana tsakaninsu gashi ganin abubuwan take kanar bagaske ba kunyarshi take,"har yanzu dai kunyar kikeji kenan tab kinada aiki"yasake cewa harda tabe baki bayan yayi hugging dinta ya manna mata kiss a goshi,"hm,dame zan tayaka?"tace dakyar wai don a chanja zancen,tana mai kallon kasa"ba abinda zaki tayani kije ki zauna ki huta nakusa karasawa ma ai"bayadda batayi ba don ganin ta taimaka dawani abin amma yayi kememe,hakan ne yasa ta juya takoma palon tadauki waya tafara lalubar gida,don tun jiya taketa kokarin kira bata shiga,sai a karo nawajen nawa sannan Baba ya dauka,cikeda farinciki da murna,suka gaisa yakara mata nasihohi da fatan alkhairi,sannan yabawa gwaggo itama,sun dan jima suna magana kafin daga bisani suyi sallama.

"Ranki ya dade an kammala"yace bayan yagama shirya komai,murmushi kawai tayi ta nufi inda yake din,"su baba suna gaidakai yanzu mukayi magana""Allah sarki ina ansawa,ina fatan dai komai lafiya"eh lafiya kalau Alhamdulillah"Allah sarki yar gidan Baba"yakarasa zancen yana mai hada musu shayi,ganin yagama zuba abincin ya dauki cokali zai fara bata ne yasa ta cije tayikememe,"aa meya faru habibty? Ko wani abin kikeson ci bawannan ba?"yayi maganar cikeda kulawa,"aa bahaka bane,so nake muci tare",ta kalli kasa,"uhm ah lallai ashedai an damu dani haka,waini da gata nake miki kifara koshi tukunna sai inci kinsan fa ke yar gata ce amma dai tunda haka kikeso ayi hakan zaayi"haka suka fara ci yana bata tana bashi suna dan taba hira,mashaallah tafara sakin jiki sosai dashi.
"Babyna wai daga ni saike agidannan amma kullum cikin lullubi kike, da saka irin wannan binjinemiyar rigar ko mekike boyewa oho?"Yace cikin wasa,dan murmushi tayi don batasan mezatace ba,"yakamata kidan dinga saka abinda kema zaki sake ki wataya kisha iska ko baki ganni bane?dubeni fa"yayi maganar yana mai mata nuni dakanshi,"wai yana nufi nima insako yar shimi da dan wando ko me tab?"tace azuciyarta"kinyi shiru nifa mijinki ne yanzu"har lokacin bata bar murmushi ba saboda rashin abin fada,hakan ne yasa ya rabu da ita suka cigaba dacin abincin saida suka gama ta tashi tafara shirin kwashe kayan don a gyaggyara ya dakatar da ita",komin abinki saifa kinsaba,duk nacin aikinki nafiki,kedai naki kawai kici babu ruwanki dawasu gyare gyare kinji"to amma g....."ke yar hutu ce yar gata babu ruwanki da aiki" ya katseta,"toh nagode","yawwa yanzu dai abinda nakeso dake shine kije kisako kayan dazaki sake kisha iska don wallahi tausayi kike bani idan kina cikin kayan nan kamar wata..."sai kuma ya kyalkyale da dariya,"kamar wata me?"tambayar tata ce tasashi saurin juyowa,yasake tuntsurewa da dariya,"idan kin chanjo zan fada miki,tunda kin fara iya magana"toh"kawai tace hadeda yar dariya itama sannan tayi saman,don ta fuskanci tsantsan tsokana ce kawai irin tashi babu wani abu dazaice.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now