RUWAN DAFA KAI

4.1K 228 16
                                    

RUWAN DAFA KAI 46~50
Na SUMAYYA DANZABUWA

Da sallama yashigo kamar koda yaushe,yayi hanyar sama abinshi don ya gaji,bacci yakeji,kamar ance ya kalli table din,gani yayi an babbaza kayayyakin, karasawa yayi ya duba yaga ancinye komai,dariya yadingayi a fili,"ashe dai fushin na karyane anaso ana kaiwa kasuwa"yace cikeda murmushi,sannan ya kwashe kwanukan yaje ya wanke ya gyara komai,(don har ya riga yasaba yasan idan bai kwashe ba zasu iya shekara a wajen bata damu ba)saida ya kammala yan gyare gyaren shi  sannan ya hau saman,bai ganta a palon ba hakan ne yasashi lekawa dakin ya ganta a sheme agado,tanata minshari,har ta yaye rabin bargon ma,karasawa gadon yayi cikeda kaunarta ya gyara mata,sannan ya jawo mata kofar yatafi nashi dakin don kwanciya.

Saidai kuma me?kasa baccin yayi sai juye juye yake tabbas yasan yayi rashin matarshi a kusada shi,gashi yana tsananin bukatarta amma babu yadda zaiyi tunda tayi bacci shi ba abin ya tasheta ba,to ma ko a farke take wannan ai saita ga dama ko ka manta ta ne?wata zuciyar tace dashi,sake sake yacigaba dayi,ga bacci yaki zuwa,dole ya tashi  yafara nafilfilunshi kamar yadda yasaba akowane dare,bayan ya idar ne  ya nufi dakin nata ya haye gadon tareda jawota jikinshi,ko minti biyar baayi ba kuwa yayi bacci abinshi.

Tun kafin ya tafi masallaci yake aikin tashinta har ya dawo yana abu daya,dole  ya hakura ya kyaleta ya koma nashi dakin don yadan kwanta,gudun kada ta farka taganshi a gadon yasan halin masifarta musamman yanzu dasuka sami dan sabani,dakyar ta farka,bata ma san ya kwana a dakin nata ba,tana baccin mutuwa.

Bayan  tagama shirinta  tana shirin saukowa kasa taci abinci ne ta tunofa ashe Gloria bata nan,ranta bai mata dadi ba,don yanzu idan tace saita tsaya neman abinda zataci batawa kanta lokaci kawai zatayi,koda ta sauko,yusuf tagani a kitchen,yana musu girki,zuwa tayi zata wuceshi yadda ta saba,"aa madam an sauko?"yace tareda washe baki,banza tayi dashi,dukda kuwa kamshin girkin nashi yamata mugun dadi amma yanzu idan tazauna taci kara rainata zaiyi,jiya ma batasan ya akayi ba zuciyarta ta yaudareta haka,"nakusa karasawa fa ki tsaya kici abinci"yace batareda ya kalleta ba,"wato ga yar yunwa!"tace aranta,"banida time"kawai tace irin atakaice dinnan ,tareda yin hanyar fita,tana jira taji yafara lallabata yana rokonta tazauna taci,"ow ok hakane fa,to maza ayi sauri kada a makara,Bye Bye"kawai taji yace mata yacigaba da yan wake wakenshi yana abinda yake,"ahh da alamun baima damuba wato?tace aranta,wato in tafi banci abincin ba kenan?"tasake cewa aran nata,hakan  ne yakara harzukata tafita a fusace,yana jiyota ta bugo kofa,tuntsurewa yayi da dariya.

"inata kiran wayarki bakya dauka,ko har yanzu fushin kike dani"tace da Sameera bayan sun hadu a office,"meyasa zanyi fushi akan me ma toh?kawai dai duk sanda kike kiran ne bana kusada wayar"amma kuma ai bakya kirana back idan kin gani "tace,"babu network ne shiyasa"cewar sammy batareda ta kalli faridan ba,"abin nan fa bawani abin zafi bane,kawai ni gani nayi kamar sirrinmune nidashi basai anji ba"tace,"nima bacewa nayi kizo kina fadar sirrinku ba amma meye namin karya?kuma ni nazata na cancanci nasan kin koma gida koba komai,amma dai yanzu duk ba wannan bama tunda dai kin riga kin aikata haka nasan matsayina,inshaallah nadaina shiga matsalar gidanki,tunda ko da dinma danake baki shawara nake miki nasiha ai ina zaune kike zuwa kisameni ki fada min,h...."Haba mana waike wace iri ce sai cewa nake kiyi hakuri kina wani jan aji,nifa ba laifina bane duk abinnan daya faru shin....."Hold it,nace kada ki kara gayamin komai tunda bana amfana miki komai,yanzu ni inada inda zanje ma daga nan don haka sai anjima"samira tace sannan ta tashi ta fita.
"Kai gaskiya fa ban kyauta mata ba wallah,yau shekaru nawa dasanina da ita,banida wata kawa fa ni arayuwar nan sai ita,amma meyasa namata haka,?ni yanzu idan tadaina kawancen dani dawa zanyi?ita kadaice class dina daidai kawancena,hmm".
Aranar tadauki Leave don Lokacin Haihuwarta ya kusa,bayadda mama batayi da ita ba tuntuni ta dauka taki saida tagama jigata  tagaji don kanta don kanta tukun.

Tana hanyar komawa gida taji wayarta na kara alamun shigowar kira,ansawa tayi tasaka a speker,"wake magana?"tace,"ah madam its  me Gloria"akace daga dayan bangaren,"aa gloria ina kikajene haka baki ko gayamin ba""Its Oga ooo,cewa yayi in tafi tunda ba zamanshi nake ba idan kin dawo ki dawo dani"Tace,"ok to nadawo jiya inata kiranki wayarki batayi,ki maza ki dawo yau saboda i realy need you kina jina?"tace da yarinyar,"ok I will today Today".
"Hm nasan a rina,saida jikina yabani yusuf ne ya kori yarinyar nan,amma banason in yarda saboda nariga nasan shi da biyayya ga mahaifiyarshi idan ta sa kara baya iya tsallakewa,wato ashe dai bata isa dashi ba kenan?zai sani daga yanzu bazai sake gigin cewa zai korar min mai aiki ba",tace tareda jan tsaki,ta juya kan motar ta chanja Hanya,ta nufi gidan Hajiya,saida taje kwanar gidan,ta parker kamar yadda tasaba duk sanda zata je sannan ta goggoge makeup dinta tafara hawayen karya,don duk sanda take zuwa kai kara wajen hajiya hajiyan ahaka take ganinta a firgice,bata taba ganinta da Wannan uwar kwalliyar ba,"tunda shi baisan mutumci ba gwara in hadashi da maiyimin maganinshi,duk yadda akayi tafiyar nan tawa ma batasan nayita ba,don data kirani rannan ai batamin zancen ba,zaisani kuwa"tace.

RUWAN DAFA KAI 1Where stories live. Discover now