*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
145to150
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Kuka take sosai dan sake shi tayi ta dago da fuskanta ta kalleshi wanda idanshi na kanta shima tace mai yasa baka nemeni ba tsawon wannan lokacin yaya yusuf, Yusuf yace aysha, indo da sauri ya kara riketa yana hawayen murna dan sakinta yayi tare da fadin Alhmdlh, aysha.... Yama rasa abunda zaice murmushi take tayi tare da komawa ta zauna dan ta duba wannan bawan Allah da yake zaune akan kujera,dan kallonshi tayi tare da fadin Baba maike damunka? Matar tace hawan jini ne yake fama dashi kwana biyu yaki sauka na rasa mai yake tunani haka, dazu muna tsaye kawai ya fadi kasa, koda ya farfado ya kasa koda daga hannu... Ta karasa maganan cikin damuwa, nan indo ta tashi ta nufi inda mutumin yake ta dan dubashi, sannan ta dawo inda take tayi yan rubuce2 sannan ta kalli mutumin tace Baba ina yake maka ciwo, da baki yake magana amma baya iya daga komai nashi, yace gaba daya jikina bana jin dadinsa ji nake kaman jikina baya tare Dani, magani ta rubuta mai tare da fadin za'a dinga Kawo shi duk sati daya ana mishi gashin kafa domin jikinshi ne ya shanye amma idan akayi Sa'a ...... Matar kuka tasa cikin damuwa nan yusuf ya karaso inda take yana fadin kiyi hakuri ummi komai zaizo da sauki insha Allah zai warke, indo ta amshe da fadin insha Allah kawai abunda za'ayi yanzu shine ku dinga bashi Magani akan lokaci, sannan ku dinga Kawo shi duk sati dayan, duk wani abu da zai sashi tunani a kauce ma abun nan taita basu shawara shiko mutumin babu abunda yake sai hawaye, abun ya daure ma indo kai ganin dan uwan nata shima yana hawaye toh miye alakansu da wannan mutumin? Jin muryan yusuf din yasa ta dawo daka duniyar tunanin data shilla, yace Sis yanzu sai kizo mu tafi tare koh? Dan ya kamata ki dauki excuse, tace dama saboda duba wannan bawan Allah aka kira ni, nan suka fita tare wannan karan yusuf ke tura mutumin, har wajan jibgegiyan motarsu mai kiran jeep yusuf da yazeed suka kamashi suka saka shi cikin motar, matar ta shiga gaba yusuf wajan driver, indo suka shige baya ita da yazeed domin kalan jeep din nanne mai shigen seyana, mai kujera baya tsakiya da gaba, yazeed kallon indo yake tayi tare da lumshe ido yana jin kamshin turarenta a hankali yake jin sonta na kara kamashi gashi yau yana farin ciki sister din abokinshi ce duk da yana cikin rudani akan ya suka rabu, itako ta gefen indo murna take sosai na ganin dan uwan nata gefe daya kuma tana tunanin wani hali A Majeed yake ciki, jin an taka birki ana horn yasa ta kalli inda suke wani katoton Gida ne sukai parking lokaci daya mai gadi ya wangale Gate din suka shiga, Nan masu aikin gidan suke ta faman zuwa gaida Alhaji da matar tashi, yusuf bayan ya fito haka itama indo da yazeed, kama mutumin sukayi Suka shiga cikin katon falon gidan, har zasu kaishi ciki yace a ajiye shi a falo zaiyi magana hakan koh akayi wata yarinya ce ta fito kyakyawa hannunta dauke da Baby daka gani bata dade da haiyuwa ba, da sauri ta nufi wannan mutumin tana mai sannu daka gani babanta ne, Alhaji yace kowa ya zauna, zama sukayi su duka banda yazeed da yake musu sallama akan zai wuce, mutumin yace shima ya Zauna a gabanshi za'ayi komai, kallon yusuf yayi yace miye tsakaninku da wannan dr din ko itace kanwar taka? Yana magana ne amma daka ji yana jin jiki, yusuf yace eh kanwata ce abba itace indo da nake fada muku, yusuf ya kalli indo yace aysha ban taba tunanin zan sake ganinki ba a rayuwa tun da nabar taraba na shigo garin abuja na fara wanki da guga ina samun albashi duk da bawai yana isana bane tunda a ciki nake ci insha, domin basa bani abinci, gashi ina dan tara wani abu dan inci gaba da karatu, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi gashi bani da ikon inje in ganki dan gargadin da mai Gari yayi min wanda shairi aka kulla mana ni dake wani hawaye mai zafi ya zubo mai a fuska, sannan yaci gaba da fadin gidan da nake wanki wata rana ina dakin da aka bani saiga matar mai gidan ta turo a kirani koda naje dan shuru yayi na wani lokaci kafin yace ta nema in bata hadin kai naki amincewa, na nuna mata hakan haramun ne tare da dan mata nasiha shuru tayi kaman ta dauki nasihar sai ji nayi tace wlh dole saina biya mata bukatan ta yana magana yana hawaye, da dai taga bazan yarda ba tasa masu gadin gidan suka Fara jibgata da yake sodoji suke gadin gidan, summin duka sosai ba tare da tace musu ga abunda nayi mata ba , mijinta baya zama washe garin ranan sai gashi ya dawo gari nan yasa a kamani a kara min duka dan shuru yayi yana kuka Kafin yaci gaba da fadin ranan na daku sosai har da karaya suka min wai naje ina son inma matarshi fyade, haka suka daukeni suka jefani cikin daki aka rufeni ga karaya a kafa da hannu, gashi babu abinci balle ruwa indo kuka tasa sosai dan tausayin dan uwan nata, yaci gaba da fadin Allah yasa inada sauran kwana a gaba, ranan dana cika sati suka daukeni suka jefar Dani a bakin titi tare damin kashedin karsu kara ganina, Ashe duk abunda ya faru lokacin da aka jefar Dani a idon Abba ne lokacin zai koma Gida nan yasa driver dinshi ya faka, dan a zaton shi yan yanka kaine suka kamani sukayi tsafi Dani amma ganin ina numfashi yasa suka kamani shida driver dinshi suka kaini asibiti nan Dr suke ta fada akan ya za'a bar mutum ya karye har a barshi Ya dauki lokaci ba'a daurashi ba, nan abba yaita basu hakuri, Dr ya fadama abba idan akayi daurin Allah yasa yayi abba yace dan Allah suyi ko nawa ne zai biya amma daurin yayi kyau, nan Dr suka ce babu damuwa gobe za'ayi, abba ya tausaya min ranan shiya koma Gida shi daya driver dinsa yasa ya kwana dani, washe gari sai gashi da matarshi da yarsu sunzo lokacin har an fara min daurin nasha wuya sosai lokacin harna gwammaci in mutu, haka akayi daurin na koma gidan abba ina zama ana jinya na, yarinyar abba wacce ita daya ya mallaka zaliha kullum tana dawainiya Dani ita da ummi, nayi zaman jinya sosai lokacin da aka kwance ni hannun ya gyaru amma kafar akace akwai matsala sai an sake min aiki, haka aka sake min wani aikin aka sa karfe a wajan nasha wuya sosai lokacin har zan iya cewa gwara na farkon ma, na jinyatu sosai, kuma duk wannan zaman da nakeyi a gidan abba bai san ko daka ina na fito ba, tunda ya tambaye ni iyayena nace mishi sun rasu bani da kowa, haka naita zama ana jinya Na, har Allah yasa na warke, lokacin ne nace zan tafi domin inzo in nema kudi inje inga yanda kike ciki koda kuwa za'a kashe ni tunda a lokacin na cire rai da duniya dan nasha wuya, Abba ya hanani tafiya inda ya nemi yasan daka garin dana fito ban boye mai komai ba na fada mishi harda abunda akamin lokacin daya sameni, nan ya tausaya min yace kar inje garin namu yanzu in zauna na wani lokaci a nan, haka naita zama yana sani cikin harkan kasuwancin shi na canji da saida motoci ganin yanda na rike Mai amana gashi na iya kasuwanci yasa ya kara sona gashi Mace daya Allah ya bashi bai kara haiyuwa ba yasa ya turani london karatu inda na karanta kasuwanci a nan muka hadu da yazeed komai tare mukeyi yazeed yayi min taimako sosai wanda ban san damai zan saka mishi ba, dan ya wuce abokina ya zama dan uwa Na, shekara uku na dawo Gida, cike dason inje in ganki lokacin dana dawo abba yaban jari sosai inda muka hada da yazeed duk da kudinshi yafi yawa ninkin nawa wajan uku, amma idan aka samu riba biyu yake rabawa yaban rabi shima rabi haduwan da nayi da yazeed yasa na samu kudi sosai domim bashi da mugunta ko kadan samun irinshi sai an tona....
Taku Maryam obam😘

YOU ARE READING
TAMBARIN TALAKA
Short Storylabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.