245to250

2.8K 123 4
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      245to250





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*


*LAST PAGE*


Koda ya shiga ya rufe kofar ya fara jibgarta Tana ta ihu jin ihun nata yasa iyayen shi suka nufi dakin akan ya bude kofar amma ina baibi ta kansu ba sai faman jibganta yake saida mai Gari ya kira matasa suka balla kofar aka fito da abu ya mata jina2 ko gani batayi dan ya kumbura mata fuska jini ta hanci ta baki duk fuskanta ya canza ya kumbura sumtum ko kuka ta kasa dan azaba ga hakori biyu daya cire mata nan take yace ya saketa Saki uku tare da fadin tabar mai Gida kafin ya fito ya kara ganinta haka ta tawo Gida jina2 hankali na ya tashi naji raina ya baci duk da bani da lafiya haka na nufa gidan dan in musu tujara duk da ana tsoran mai Gari koda naje na tarar da mamanshi da yan uwanta na fara Bala'i haka suka taru suka min duka wanda shine silan kara durkushewa na ciwo yaita kamari tun daka lokacin na daina tafiya kuka ta saki tare da fadin nasan ba komai bane sai hakkin ku ganin ciwo naci na gashi babu Magani nace musa ya saida gidan nan mai gari da yaji labarin zamu saida gidan yace karmu fara haka muke ta zama gashi babu abinci abu kuma idan ta fita aita jifanta wai Tana bin boka haka muke ta zama a Gida Mlm gashi babu Sana'a gashi bintalo sunyi gobara sun kone ita da mijinta da yaranta, mutane sun tsanemu a kauyen nan wlh raban mu da muci abinci kwana uku kenan sai ruwa dan Allah indo ku yafe mana dan Allah wlh hakkin kune yake cin mu Abu itama kuka ta Saki tana kara roqan indo, Yusuf yace inna kiyi shuru mun yafe miki duniya da lahira tunda gashi abunda kika mana yasa mun hadu da arzikin mu, indo da fuskanta ya jagule da kuka tace inna ina inna jamila fah? Tani tace sun tashi daka nan Abu fita ki fada mata ga indo tazo, da sauri Abu ta dauko wani bakin hijab ta fita indo tace Ashe sun tashi? Tace eh jamila ta kasa zama saboda mun hanata sakat tunda tabar gidan nan bata kara lekowa ba, mlm musa ne yayi magana tare da fadin yusufa dan Allah ku yafema kawunku wlh duk shairin tani ne ita ta sani yin duk wani abu dana aikata wlh da badan wani abu ba dana rabu da ita da sauri indo tace kawu kayi hakuri karka rabu da inna ka yafe mata kaman yanda muma muka yafe ko Allah ana Mishi laifi ya yafe balle mu,yusuf ya amshe da hakane mlm musa yace naga bakin fuska su waye? Yusuf yace ga mijin aysha da yaranta ya nuna yaran da suka manne a jikin babansu dan tsoran ciwon tani suke ga iyali na ya nuna zaliha, mlm musa ya mika ma yaran indo hannu da nufin suzo suka noke kaman za suyi kuka yace kuzo yan nema, ya miko hannu kaman zai daukesu suka sa kuka tare da kankame babansu dariya Mlm Musa yayi tare da fadin kuyi hakuri bazan daukeku ba tunda baku sanni ba, ganin ya koma ya zauna yasa sukai shuru tare da yin ajiyan zuciya, A Majeed dariya shima yayi tare da fadin toh ya isa haka baza a daukeku ba, dai2 lokacin inna jamila ta shigo gidan ta kara tsufa amma babu laifi Tana cikin shiga mai kyau duk da kauye ne, indo da sauri ta tashi ta rungumeta Tana kuka inna jamila ma kwallan takeyi tare da fadin aysha Ashe zan sake ganinki a rayuwa, indo tace innata gani inna ta tana maganan Tana kuka sun dauki lokaci a haka kafin suka zauna inna jamila tace Ashe zan sake ganinki sai yasa naki barin garin nan dan kullum ina sa ran ganinki Allah Sarki indo na aysha indo Allah kenan mai yin yanda yaso inda a hanya na ganki bazan ganeki ba Ashe haka kike da kyau da fari kauye da wuya duk sun boye miki, dariya indo tayi tare da fadin innata ga Yusuf fah tace Allah Sarki Yusuf nan suka gaisa harda A Majeed kamo hannun zarah tayi Tana fadin kai tubarkallah yarinya kyakyawa Zarah batai mata kiwa ba ganin zarah a hannunta yasa su arfan suma zuwa wajanta suko su tani suna ta kallon ikon Allah yaran da suke manne jikin babansu amma yanzu sunje wajan jamila, Tani tace Abu ba'a basu koh ruwa bah, Yusuf yace a'a inna barshi mun gode, nan A Majeed ya ciro kudi bandir din kudi yan dubu daya2 yaba inna tani bandir daya dubu dari kenan yace gashi inna kusai kayan abinci yaba mlm musa bandir din guda uku yace gashi Baba ka rike wannan a hannunka mlm musa da tani sai washe baki suke, tashi yayi yace ina zuwa fita yayi jim kadan sai gashi ya dawo tare da karamin leda a hannunshi kudi ne cike a ciki inna jamila yaba dubu dari biyu yace gashi ta rike kafin su dawo nan taita godiya tana fadin Allah ya saka da alkhairi dubu dari yaba Abu itama Tana ta murna, Yusuf yayi mai godiya sannan yace aysha inaso a kira liman ya raba mana gidan nan domin ni nawa zan barma su Baba tace nima abunda nake shirin yi kenan amma ban Sani ba koh mijina zai amince? A Majeed murmushi yayi tare da fadin baki da matsala aysha duk abunda kika yanke nima na amince nan mlm musa yaita rafka godiya harda kuka itama Tani harda kuka Tana godiya Yusuf yace zansa a gyara gidan zanje wajan mai gari inbar komai a wajanshi sannan zaku koma wani gidan kafin a gama nan, inna ke kuma zamu asibiti dake a duba ki, tani kuka take sharbe2 Tana godiya tare da fadin su yafe mata tayi kuskure *hmmm rayuwa kenan sai yasa hausawa ke cewa d'a na kowa ne baka san mai rikeka ba duk Yaron da aka baka rikon shi kiji tsoran Allah ki rikeshi amana dan baki san gaba ba May Be shine zai rikeki kar kice wai kina da yara zasu kula dake bafa lallai bane yaran nan naki in Sun girma suji qanki ba, inma sun tausaya koda ciwo ya kamaki sun biya kudin Magani akwai laluran fitsari bayan Gida kuma idan lokacin yazo ga girma ga ciwo kina bukatan kula ba lalle bane yaranki su miki komai ba wlh sai yasa wlh muji tsoran Allah musamman ma mu mata ni wlh wasu matan mamaki suke ban mata fah mune aka sani da tausayi amma saboda an baki riko sai ki cire tausayinki akan dan rikon kita gana mishi azaba haba mata ina tausayin namu yake, sannan maza kuma kuji tsoran Allah ku daina kama maganan Mace har sai kunyi bincike domin wlh mata akwai iya kulla makirci ko shaidan na tsoran kaidin Mace idan Mace ta zauna ta tsara karya sai kaji namiji ya dauka har an fara Bala'i Dashi wlh ko mamanka ta fada maka magana akan wata yana dakyau kayi bincike akai sosai kafin ka dauki hukunci domin wlh rashin bincike akan abu zai sa mutum daya san, akwai kiraye2 da dama da nake samu akan irin wannan matsalan musamman mata masu zama Gida daya da uwar miji  zan danyi bayani kadan akwai wacce ta turo min txt wai Tana zaune Gida daya da uwar mijinta komai tana mata na biyayya amma uwar mijin ta tsaneta taita tsangwamanta Yaron duk yana lura da irin biyayyan da take ma mamanshi kuma yana kyautata ma matar tashi dan yana jin tausayinta akan abunda mamanshi take Mata gashi kuma ita tana Mata biyayya wai yanzu uwar mijin taita kulla mata shairi wajan mijin tun baya kamawa har ya fara yarda yanzu ta hadasu rigima har tasa ya saketa Saki daya gashi yana son matarshi ta hanashi ya dawo da ita wai ya kara aure.....  Haba mata mai yasa idan danki yana da Mata sai kibi ki tsani matar karfa ki manta kema fah Mace ce shin dama ciwon y'a Mace da ake cewa na y'a Mace karya ne tunda gashi yanzu dan Mace na auren danki saiki tsaneta karki manta fah kema kina da yara mata idan aka musu abunda kike ma matar danki zaki ji dadi koh da baki da yara mata Ai kina da yaran yan uwa mata wanda na tabbata idan aka musu abunda kike ma matar danki ranki zai baci dan Allah mata mu dinga kawar da idonmu akan matan yaranmu da yan uwanmu domin duk abunda kama dan wani sai anma naga majority mata basa son uwar miji saboda irin wannan matsalolin sannan mata masu tsanar uwar miji ku daina domin itama uwarku ce tunda ba zaki so danta ba kice ita baki sonta dan ance maso Husaini yaso hassan Allah yasa mu dace* su Yusuf sunje wajan mai Gari inda suka sami su Sulaiman a can shi baima gane indo ba bayan an gaisa nan Yusuf ya gabatar da kanshi mai Gari yace au Yusuf ina tama kallon sani kai kuma tunda kazo sai ka tafi kaki dawowa kaga kanwar taka? Yace eh ga tanan mai Gari indo ce wannan haka sai a sannan sulaiman ya kara dagowa ya kalleta danshi a zaton shi larabawa ne suka zo ya bude baki zaiyi magana yaji yusuf na fadin ga mijinta nan da yaranta sulaiman hawaye ya fara fita a fuskanshi ya tashi yabar wajan indo itama ido ta bishi dashi domin sulaiman ne masoyinta na farko wanda ya sota tsakani da Allah ganin yabar wajan yana hawaye yasa itama guntun hawayen da take boyewa ya fito da sauri tasa hannu ta goge dan kar mijinta ya gani, nan mai gari suka gaisa da A Majeed inda Yusuf yace zai bada a gina masu gidansu a rushe wannan yace MA mai gari zai bada amanan komai a wajanshi A Majeed yace Yusuf ka barshi ni zanyi komai nan ya dauko wani akwati yaba mai gari tare da fadin 6mil ne a fara aikin mu gani mai Gari yace ai yayi yawa gidan bashi da girma A Majeed yace a fara toh sannan a nema musu wani gidan su zauna kafin a gama, nan mai gari ya amsa da toh tare da kallon Mlm musa yace mlm musa ka gode Allah yarannan basu rikeka ba mlm Musa yar guntun kwallanshi ya fito yace hakane shairin shaidan ne da kuma makiran matar dana samu , suna cikin magana sai ga dan jummai wasû samari sun rukoshi sun mai jina2 ga jummai kuma nata kuka mai gari yace lafiya? Matasan suka ce kanwar mu yama fyade kuma yasan yana da HIV nan mai gari ya Saki salati tare da kiran yan sanda aka tafi Dashi jummai nata bada hakuri akan a barshi mai gari yace idan ta kara magana sai an hada da ita taja baki tayi shuru tare da kokarin barin wajan mlm musa yace jummai ga indo koh baki ganeta ba ashe Allah ya taimaketa da yanzu danki ya kashe ta da sauri ta kalli indo sai kuma ta kara fashewa da kuka tace Allah sarki wlh yaso ya aureta lokacin nice na shiga na fita na hana auren mai gari yace kinga koh kin taimaketa ga tarin zunubi da kika tara ma kanki haka jummai tabar wajan jiki a sanyaye, Yusuf yace tunda A Majeed ya dauki komai shima ya bari ya samu lada yakai Tani asibiti hakan akayi a ranan aka samo mota aka tafi da ita asibiti su indo kuma suka koma Abuja dan A Majeed yace baza su kara kwana ba, bayan sun Isa Abuja taga A Majeed ya wani tamke fuska bata kulashi ba taja hannun yaranta sukai ciki tunda suka dawo bai shigo ba Dan yau gidan zainab yake, ta mishi uziri dan tace May be gajiya yayi ga yaranta sun dameta dady dakyar ta samu sukai bacci washe gari har wajan 5 bai shigo ba gashi ta kirashi yaki dauka sai wajan isha taji ihun yara suna daddy lokacin Tana kitchen batai fushi ba ta fito domin bai taba mata haka ba tace daddy lafiya kuwa inata kira kaki picking kodai gajiyan ne yasa haka? Wani irin kallo ya mata Da yasa tayi shuru Tana mamakin mai tayi wasa yayi da yaran sannan yaja su dakinsu yasa musu kayan bacci yace suyi bacci dare yayi dan kullum haka yake musu sai yasa jiya da bai zoba Suke ta rigima, bayan Ya fito ne ta nufeshi amma kallo daya ya mata ya kauda kai tace my one tafiya yaci gaba dayi bai tsaya ba da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi Tana kuka tare da fadin mai nayi mijina yake fushi dani kukan nata yaji har ranshi a hankali ya rikota tare da dago mata Kai yace aysha mai yasa kike kuka lokacin da kika ga saurayinki ya tashi dama har yanzu kina sonshi tace haba My One kasan Kai daya nake so dama akan wannan abun kake fushi kawai tausayi yaban saketa yayi tare da fadin sai kiyi tajin tausayin nashi ai kara rikeshi tayi ta fara rarrashin shi dakyar ya hakura tare da fadin baya son ma ya kara jin tayi maganan sulaiman dariya tayi sosai tace ta yarda ankai Tani da kwana biyar asibiti ta rasu wanda yasa indo dole ta koma kauyen kasancewan an fara aikin gidansu a gidan mai gari ake zaman makoki sam A Majeed yaki yarda indo ta kwana wai jalingo zasu koma hakan akayi dan su biyu suka zo yaran na wajan Zainab dan ta yaye su nono bai damesu ba, kwanan su uku suka koma taso ta dauki Abu amma yusuf yace gidanshi zata koma da zama tare da Abu Yusuf ya koma abuja, duk wannan abunda ake indo nada ciki bata sani ba dan tana period dinta rannan suna zaune da A Majeed yace Baby anya ban baki ajiya ba kalli yanda kika kara cika da kyau tace haba My One yanzu idan nayi ciki ai na shiga uku banfa manta wuyan da nasha ba  kuma su zarah ko shekara biyu basu yi ba kaga aiko su sun ishemu yace Baby nifa ina son yara wannan ma Mum so take mu bata su naki ga Zainab itama Tana So kinga idan kika kara haiyuwa sai aba Mum da zainab tunda yan uku nake baki dariya tayi tare da fadin Na yafe tashi tayi ta nufi daki dan itama Tana dan jin canji aiko gwajin farko data gwada taga Ciki ne cikin tashin hankali ta koma inda ta barshi tace my one na shiga uku wlh ina da ciki dan Allah muje a zubar wlh banso in kara haiyuwa yanzu, daka mata tsawa yayi tare da fadin wlh idan kika zubar min da ciki saina Saba miki wlh yana fadin haka yabar falon rai bace ita ko kuka ta Saki mai karfi tare da fadin wlh bazan yarda ba inna mutu aishi kenan dama ba sona yake ba kuma ciki ne wlh bazan yarda Dashi ba koda A Majeed ya fita dakin Zainab ya nufa ya ganta Tana kuka da sauri ta Fara gogewa kallonta yayi tare da fadin Zainab lafiya kuwa? Cikin kuka tace A Majeed na kasance ina son haiyuwa naje asibiti da dama ina amsan Magani dan in haiyu duk bada saninki ba Amma daka baya sai akace bazan iya haiyuwa ba wai mahaifata ta sake inko na samu ciki komai zai iya faruwa Dani duk da bama sa iya tunanin zan haiyu kullum inna Tuna da wannan abun nakanyi kuka ina dana sanin shan......  Shuru tayi dan tunawa da tayi dawa take magana, yace Zainab shan me??  Shuru tayi lokaci daya kuma ta kara sakin kuka tace A Majeed shan maganin hana daukan ciki ya jefani cikin wannan Bala'in dan Allah ka yafe min wlh nayi maka laifi ina shan Magani ba tare da saninka ba gashi yanzu ina son haiyuwa ido rufe amma babu dama kukan da takeyi ne duk da ranshi a bace yake yasa ta bashi tausayi har ya fara rarrashinta tare da tunanin aysha na gudu ita gashi wannan Tana nema duk da ita taja ma kanta.






To już koniec opublikowanych części.

⏰ Ostatnio Aktualizowane: Dec 21, 2018 ⏰

Dodaj to dzieło do Biblioteki, aby dostawać powiadomienia o nowych częściach!

TAMBARIN TALAKAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz