155to160

1.7K 74 2
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      155to160





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*







Saukan numfashin shi take taji akan fuskanta, fuskanshi ta kalla ta gefen idonta amma taga idonshi a rufe alaman dai bacci yakeyi bai san abunda yakeyi ba, dan ajiyan zuciya ta sauke tare da rike dayan hannunshi ta sauke daka rikon da yayi mata, tazo zata sauke dayan taji yana magana kadan2 saida ta saurara dakyau taji yana kiran sunanta Aysha I really love you, da sauri ta cire hannun nashi daka jikinta ta tashi ta koma kan kujeran dakin Tana mai sauke ajiyan zuciya, kanta ta kifa a kasa tare da lumshe ido anya A Majeed ba gamo yayi da aljana mai sunanta ba, wannan wani irin So ne wanda ban taba jinsa ba sai a film koh a littafan hausa, dama hakan yana faruwa dagaske mutum ya zauce akan Mace kaman yanda marubuta suke fada a littafin su, wani irin hawaye taji yana zubar mata data tuna da maganan mum, gskiya Mum ta cika uwa ta Gari Wanda irinsu kalilan ne, wata uwar zata iyasa kowa cikin kunci dan nata yayi dariya, sai gashi ita Mum dan wani takeso yayi farin ciki akan nata, A Majeed yakai namijin da duk wata Mace zatai burin aure sai dai kash matarshi tafi karfinsa dan yana mata son da baya ganin laifinta koh kadan, wani hawaye ne ya kuma sauka a kan fuskanta tunawa da yanda ya kaskantar da ita a gaban matarshi wai yar aiki ya Kawo mata, jin karan bude kofar ne yasa tayi saurin goge hawayen fuskanta tare da dago kanta, Mum ce ta shigo dakin ganin fuskan aysha yasa Mum tace aysha lafiya Kuwa?  Indo tace lafiya Mum? Mum kallon gadon dan nata tayi wanda yake bacci har yanzu dan Dr yace zaiyi baccin wajan awa 6, sannan ta maida idonta kan indo wacce take dan murmushin yake dan kar Mum ta zargi wani abu, Mum tace haba aysha ai duk wanda yaga fuskanki yasan kinyi kuka, nifa mahaifiyarki ce dan mai yasa zaki dinga boyemin damuwar ki, indo tace Mum babu komai kawai ina kukan murna ne yau naga dan uwana, Mum da sauri ta zauna kusa da indo Tana tambaya a ina? Nan indo ta bata labarin inda suka hadu, Mum ta taya ta murna sosai tare da fadin ina fata dai baza'a gujeni ba koh?  Dan murmushi indo tayi a dai2 lokacin A majeed ya farka yana mika tare dayin salati, gaba daya idonsu ya sauka a kanshi wanda shima din su yake kallo, da sauri Mum ta tashi ta nufeshi Tana fadin son ya jikin naka? Dan murmushi yayi ba tare da yace komai ba, Mum ta tashi tare da fadin bari in kira Dad dinki, indo ganin kallon da yake mata yasa ta karaso wajan gadon Tana fadin sannu ya jikin naka? Yace ai baki damu da kisan halin dana shiga bah yana maganan ne cikin murya irin na mara lafiya dake jin jiki, za tayi magana su Mum suka shigo dakin, Dad zama yayi kusa da dan nashi yana tambaya son ya jikin naka hope ka warke? Kai ya girgiza alaman a'a yace Dad bana tunanin zan warke har sai na samu abinda nake So, Dad kallon Mum yayi kalan kinga ni koh, Mum yi tayi kaman bata jiba, Indo kuma wani hawaye ne ya zubo mata wanda yasa tabar dakin da sauri, ganin indo tabar dakin yasa Dad fadin kinji dai da kunnanki koh? Mum tace dan Allah kabar wannan maganan mu nemi lafiyar yaron nan kawai, A Majeed da baisan akan me suke maganan ba yasa ya lumshe ido, Mum matsawa tayi kusa Dashi tasa hannunta a gashin kanshi wanda duk ya yamutse tana shafawa bude ido yayi a hankali Mum tace son muje gidan mu saika zauna acan kafin muyi arranging na fita dakai waje, kai ya girgiza tare da fadin No Mum am OK ni nasan miye matsalata babu Dr din da zai bani Magani sai Dr aysha ki bari ita tai treatment dina, Mum taji tausayin dan nata sosai, duk da tasan shiya jama kanshi yanzu ga matar tashi nan da yake Bala'in so bata ma san baida lafiya ba tunda bata kirashi ba ko Mum taji ya yake ba, Mum taji zuciyanta na mata suya, mum dakyar ta lallaba shi akan yazo su koma gidanta toh, security din Dad ne suka kamashi akai mota dashi, wanda indo dake zaune Tana kuka a wajan ganin an fito dashi yasa hankalinta ya tashi, Mum tace mata tazo su tafi jiki a sanyaye tace ma Mum bari in dauko abu a ciki ledan maganin data shigo dashi ta dauko sannan ta shiga motor da Mum ta shiga wanda shima A Majeed din yana cikinta, Mum ce kusa dashi yasa kanshi a jikinta, gaba daya kamshin turaren Indo yake ji a motar duk da yasan tana ciki wani irin mugun sonta yake karaji yana shiganshi, sai dai yasan duk santa da yakeyi a yanzu bazai iya matsa mata akan ta soshi dole ba, itako indo gaba daya jikinta yayi sanyi, sai dai duk da haka bata tunanin zata iya aurenshi domin tana ganin kaman Akwai abunda yake shiryawa akanta shida matarshi tana ganin kaman So yake ta koma gidansa yaci gaba da azabtar da ita a matsayin yar aikin su shida matarsa da yake Bala'in so, wani hawaye ya zubar mata wanda tasa hannu ta goge da sauri dan kar a gani, idan A Majeed dake kwance cikin Mum yana ganin duk abunda takeyi wani iri yaji domin baya son ganin damuwanta a yanzu, bayan Sun karaso aka shigar dashi har dakin da yake da, Dad bai shigo ba dan anata kiran sallah magrib ya tsaya yayi sallah, itama indo alwala tayi dan tayi sallah,bayan ta sallame ta tsinta kanta da yima A majeed addu'a akan Allah ya bashi lafiya, bayan ta shafa addu'a ta dauki wayanta da ledan Magani tare da sauran kayan aikinta ta nufi dakin, Mum na ganinta tace yauwa dama So nake naje nayi wanka da sallah tunga gaki bari ki zauna Dashi kafin in dawo, tace toh Mum, bayan fitan mum ne indo ta matsa kusa dashi tana fadin yanzu mai kake ji yana damunka? Yace ke, tace mene? Yace ina nufin kece matsalata aysha nasan ban kyauta miki ba, kuma duk wani hukunci da kika dauka akai na kinyi dai2 dan na fusknci hukunci fiye da abunda kike min a yanzu, sai dai ke a wajanki ba komai kike daukan hakan ba, amma ni a wajena hakan da kike min.....  Dan shuru yayi alaman ciwo na damunshi kafin yaci gaba da fadin hakan zai iya shafan rayuwa na, da sauri ta kalleshi dan ta tabbatar shi dinne yake magana ganin ita yake kallo yasa tayi kasa da kanta, aysha a da ban taba tunanin zanzo wata mace ba sai zainab, amma a yanzu Allah ya jarabce ni da sonki wanda ko Dashi aka barni na horu ban taba jin kishin wata Mace ba kaman yanda nake jin naki sai yasa na bada aikin gina miki asibiti dan banso kina aiki a karkashin wani namiji sai dai ayi a naki,  dan shuru yayi yana kallonta ganin Tana hawaye yasa yace aysha dan Allah ki yafe min koh Allah muna masa laifi ya yafe mana,  jikinta yayi mugun sanyi ganin ita yake kallo ysa ta daure tace zan gwada maka VP in gani ko yyi normal, dan murmushin yake yyi tare da fadin No ki barshi kawai bana bukata, kallonshi tayi taga idonshi a rufe, tace lafiya shine komai mai yasa kake son horar da kanka da ciwo? Idonshi a rufe yace bani nake son horar da kaina da ciwo ba kece kike neman horar dani da ciwo aysha ko kin san sonki zai iya zama ajalina? Bazan iya rayuwa in ganki da wani namiji ba Face ni ba, cikin siririyan muryanta da tasha kuka tace A majeed ni nasan ba sona kake ba akwai abunda kake nufi dani amma daka yau ina tunanin zan bar gidan nan May be idan nayi nesa dakai zaka tashi, amma ina rokan ka da kabari in duba ka,jin yayi shuru yasa ta matsa kusa da gadon tare da zama akai bude ido yayi wanda suka hada ido wani irin shock taji tayi saurin kawar da kanta gefe, yace Aysha keda za kiyi nesa dani mai yasa kike son dubani? Baki damu dani ba mai yasa kika damu da ciwo na? Aysha kiban amsa? Tace saboda ina son ka warke kaci gaba da rayuwa kaman da dan Allah karka kara tambaya na ka bari in duba ka, yace bana bukatar wani koh ke ki duba ni, har sai kin fada min amsan tambayar da zan miki, jin hanunshi tayi cikin nata wani abu taji tun daka sama har kasa, kokarin cire hannunta tayi daka nasa amma ya rike sosai dan haka ta hakura ,yace aysha ki kalleni ki fadamin cewa bakya so na, indai kika min haka na miki alkawarin zan cireki a raina har abada tare dayin nesa dake, kuka ta fara mai sauti gashi hannunta yana tare da nashi babu daman tabar wajan, shiko jin kukan yake har cikin ranshi amma babu yanda ya iya dole yana bukatan amsar ta,cikin kuka tace dan Allah ka sakemin hannu, baice komai ba haka kuma bai saki ba, Dad ne ya shigo dakin ganin Dad yasa ya sakar mata hannun to tashi tabar dakin da sauri tana kuka, dakinta ta nufa ta fara hada kayanta domin bazata iya ganinsa a hakan ba kuma ba zata iya yarda da abunda yake bukata a wajanta ba duk da har yanzu ta kasa gane mai zuciyarta to yanke akai amma d Best tin shine tabar gidan cikin daren nan hakan zai bata daman ci gaba da rayuwa cikin salama shima idan yaga ya daina ganinta tasan zai tashi yaci gaba da rayuwa.... Hmmmm ku biyoni sannu a hankali









Taku Maryam Obam😘

TAMBARIN TALAKAOnde histórias criam vida. Descubra agora