*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA**🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
210to215
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*Fita yayi tare da rufe mata kofar dakin, kirjinta ne ya fara buga mata da sauri ganin ya fita din, yana fita yasa akwatin cikin mota tare da shiga ya tada motar yabar gidan, da sauri ta tashi ganin ya tada mota dan batayi zaton zai fita dagaske dinba, hanyar fita tayi ko kafin ta karaso yabar gidan wani irin ihu tasa mai karfi tare da sakan kuka lokaci daya, dama nace baya sona tunda harya tafi dagaske inda yana sona bazai tafi ba, zama tayi a falo tana ta rusar kuka har kanta ya fara ciwo lokaci daya kuma taji wani irin kishi na shiganta dama nasan gidan matarshi yake son zuwa sai yasa bai musa minba ya tafi, gaba daya ta kasa rintsawa domin wani irin azababban kishin shi takeji dan tana ganin kaman yana can wajan matar tashi, wata zuciyar tace toke ina ruwanki keda ba sonshi kike ba, kai ta girgiza tare da fadin miji nane dole in damu akan komai nashi, ranan gaba daya kasa bacci tayi sai juyi take tayi a parlour har aka kira sallah asuba, kuka ta kuma Saki tare da rufe kofar parlour ta haura Sama dan tayi sallah tsintar kanta tayi da rokan Allah akan yasa mijinta Ya dawo gareta yanzu, yasa mishi sonta fiye dako wace Mace, taita addu'a tana kuka a wajan baccin wahala ya dauketa.
Shiko tunda ya fita yake jin wani iri mai yasa aysha bata sona haka, wani irin kiyayya takemin har haka, anya zata soni kuwa a rayuwa, wannan shine kaddara na ban taba tunanin zanso macen da bata sona ba, hotel ya kama dan anan yake ganin zai iya samun hutu dan baya tunanin ma zuwa wajan Zainab a wannan lokacin, shima bacci dai gagaranshi yayi gaba daya domin zuciyarshi gaba daya a jagule yake bashi da wani buri Face yau ace aysha ta amince Dashi a matsayin miji wanda take so, amma yasan hakan bamai yuhuwa bane tunda ta nemi yayi nesa da ita hakan zaiyi duk da yasan zaiji jiki sosai kuma baya iya tunanin zai iya tsawon lokaci baya tare da ita dan ganinta kawai yana sashi cikin farin ciki tare da nutsuwa, wani irin hawaye mai zafi ya zubar mai a ido wanda bai san fitar suba, bai taba tunanin zaiso Mace bayan zainab ba, yau gashi son wacce ya raina yake mata kallon yar kauye wacce bata wayeba gashi sonta na neman zautar dashi, lallai babu kyau raina halittar Allah a duk yanda yake, yasan abubuwan daya mata a baya yasa take mishi haka a hankali ya furta aysha mai yasa bakya yafiya mai yasa ba zaki iya yafemin ba, nasan nayi miki laifi amma hukuncin naki yayi tsauri da yawa wannan laifin nawa bai kai wannan hukuncin da kike min ba, kanshi yaji yana sara mai gaba daya ya rasa maike mishi dadi shiba dadi yake ji wajan Zainab ba gashi itama aysha wacce take nuna mai kiyayya baro2 haka yaita tunani har aka kira sallah yayi, bayan Ya idar ya kira Abdul bugu uku Ya dauka cikin muryan bacci yace ango kasha kamshi A Majeed yace Abdul kana ina? Yace Gida mana A Majeed yace zoka sameni inda nake yanzu plz, Abdul yace kana ina nan ya fada mishi abdul yace OK gani nan, bayan Sun kashe wayan abdul ya tashi domin zuwa wajan abokin nashi tare da tunanin mai yakeyi a hotel toh, koda abdul ya karasa dakin da yake yayi nocking dakyar Ya tashi ya bude mai Abdul da ido ya bishi ganin yanda yake tafiya, yace Man maike faruwa ne? A Majeed bayan Ya zauna ya kalli abdul tare da fadin Mai yasa aysha bata sona? Abdul mai zan mata ta yafe min laifi na tasan cewa dagaske ina sonta? Abdul yace ban gane ba nan ya fadama abdul abunda ya faru harda wanda zainab tayi, ajiyan zuciya abdul yayi tare da fadin dafarko dai zance ka kara hakuri akan abunda zainab tayi wannan dama dole ne duk wata Mace ta nuna kishi idan aka mata kishiya sai dai ko wacce da irin nata, sannan aysha bata kyauta ba amma kayi Hakuri zan mata magana, A Majeed yace No ka barta karka ce mata komai na riga na yanke bazan koma gareta ba koda kuwa santa zai kashe ni dan Allah karka je wajanta ka barta, Abdul yayi shuru na wani lokaci kafin yace ok yanzu ita Zainab din fah? Yace ban san inda take ba bama na bukatan insan inda take for now, ina bukatan hutu zan manta dasu dukansu Na wani lokaci, Abdul yace haba Man laifin wani baya shafan wani yau fah 8dyz dayin aurenka kuma a ka ida 7dyz zaka ma aysha saika koma gidan zainab kaga Kana cikin kwananta ne ya kamata ka nemeta in baso kake kaci hakkinta ba, nan Abdul yaita mai nasiha tare da nuna mai yayi adalci ya danji sanyi a ranshi ba kaman da ba, harya amince zai nemi Zainab din, koda abdul zai tafi yace su tashi su tafi tare, A Majeed badan yaso ba ya tashi suka wuce direct gidan Zainab din suka nufa koda sukaje kofar parlour a bude yake shiga sukayi suka ganta a parlour Tana bacci, A Majeed sai yaji ta bashi tausayi ko ba'a fada ba yasan anan ta kwana dan ja mata hanci yayi tare da hura mata Iska ido ta bude a hankali ganin A Majeed yasa ta tashi da sauri tare da fadin mai ya kawo ka nan? Lokaci daya kuma tasa kuka mai ban tausayi tare da fadin ka fita kaban waje ka koma wajan wacce mamanka ta baka dama nasan mamanka ta tsaneni gashi tayi nasara tasa kamin kishiya har Kana marina a gabanta, Abdul yace haba Zainab komai ya faru kiyi hakuri tunda kika ganshi yanzu yasan yayi laifi, tace Abdul kalli fuska na yanda ya kumburu babu wani wanda ya taba saka hannunshi a jikina da sunan duka sai jiya kuma namijin da nafi so a rayuwa shine ya mareni saboda wata yar Iska, A Majeed cikin tsawa yace Zainab ki iya bakin ki, ya kamata kisan abunda zaki dinga fada, tace na shiga uku abun naka har yakai haka yanzu baka sona ka tsaneni kuka ta kuma Saki wanda ya hanata karasa maganan, matsawa yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi abdul ganin haka yabar gidan dan ya basu waje ya rarrashi matar tashi, matseta yayi sosai yace control your self plz, cikin kuka tace A Majeed ka rabu dani, yace bazan iyaba Zainab ina sonki keda kanki kin san haka, Zainab ya kamata kimin adalci kin san ni dan adam ne 9 nake ban cika goma ba sannan karki manta duk abunda bawa yayi haka Allah ya tsara mishi a rayuwanshi remote din na hannun Allah mu munayin yanda akayi damu ne, so ki daina fadin wai bana sonki sannan ban mareki ba saida kika min laifi abunda kikayi jiya is out of sense sannan zaki sa yarinyar ta rainaki yaka mata ki kama girmanki, Zainab wlh ina sonki sosai na rasa a ina kika samo wasu halaye da baki dasu da kika daurama kanki,plz ki dawo yanda na sanki... A hankali tace indai kana sona kaman yanda kace toh ka Saki matar da aka daurama, dan murmushin takaici yyi tare da fdin Zainab ki saurare ni ina sonki kaman yanda nace miki sannan kuma hakan bazai sa in rabu da ita ba, kokarin fara jan jikinta daka nashi ta farayi tare da fadin sun kwace min kai sun rabani dakai sunyi nasara, ina sonka A Majeed amma bazan iya zama da wata a matsayin matarka ba, yace Zainab ki dinga tunawa da ko ke yar waye, yanzu ba abun kunya bane ace kina kin kishiya tace so what koma yar waye ni kawai bana so, yace zainab zauna muyi magana, bata motsa ba ganin haka yasa ya kamota ya zaunar da ita yace zainab ina sonki bazan iya rabuwa dake ba haka ita aysha bazan iya rabuwa da ita ba yakama ki fahimci haka sannan ki rige girmanki a wajanta, sanan inaso ki canza halinki plz mu zauna lafiya, shuru tayi tana nazari can tace shikenan na yarda amma zaka hadamu Gida daya coz naga gidanta gidan mata biyu ne, dan shuru yayi can yace keda bakya son takura kaman wajan ya miki kadan, tace eh ina son mu zauna tare yaji dadin hakan yace ok zansa a miki oder din kaya sai a sa miki, shuru tayi tana tunani tare dajin kishin mijin nata wai yau itace akama kishiya har zasu zauna Gida daya, ganin tayi shuru yasa bakinshi cikin nata ya fara kissing tun tana sharewa harta fara mayar mishi da martani baka jin karan komai saina nishin su ranan Zainab ta Saki jiki ta nuna mishi tsantsar so shida kanshi yayi mamaki dan yaji canji sosai, bayan Sun dawo hayyacinsu ta tashi ta nufi dakinta toilet ta fada tana wanka tana kuka yanzu ita A Majeed yama kishiya amma ba komai zan dauki mataki koba yanzu ba, haka tayi wanka ta fito tasa wata riga da wando tayi kyau sosai, tana cikin sa Turare ya shigo dakin daka ganin shi Shima kasan yayi wanka, rungumota yayi ta baya tare da fadin uwar Gida ta, dan murmushi tayi wanda bai kai ciki ba, ranan bai fita koh inaba sai masallaci da yake zuwa hakan yama Zainab dadi harta sake dashi tare da rage radadin da zuciyarta ke mata kuma tana lura bai kira amaryar tashi ba hakan ya mata dadi harta yarda da cewa ita yakeso kawai yayi auren ne dan haka Allah ya tsara mai, ranan duk wata kulawa ta bashi ta gefen A Majeed kuma gaba daya tunanin indo yakeyi koh wani hali take ko taci abinci gaba daya dauriya yakeyi kawai Dan kar Zainab ta lura da hakan.
Indo iya tashin hankali ta shiga tun da ta tashi tayi wanka tasa English wear masu kyan gaske dan tana tunanin zaizo amma taji shuru gashi har yamma tayi shuru, kuka ta farayi tare da fadin dama baya sona karya ne kawai da yaudara tunda ya sami abunda yakeso ai na shiga uku yanzu, wani irin kishin shi takeji wanda kwana daya da bata ganshi ba yasa ta kasa cin abinci tare da yarda cewa tana sonshi daukan wayanta tayi danta kirashi ta bashi Hakuri ya dawo, lokaci daya ta kuma sakin kuka mai karfi tunawa da tayi bata da number dinshi, kuka take sosai tare da tausayin kanta dan yanzu tasan babu komai a ranta sai kaunar mijin nata wanda ya mata kaura, ta gefe daya kuma taji tana kara tsanar Zainab tunawa da tayi itama matar shice wanda take tunanin yanzu suna tare yana ririta ta, kanta taji yana sara mata kaman zai fashe dan ciwo, hannu tasa a kan tare da fadin innalilahi'wa inna ilahira jiun, dama haka so yake mai yasa tun farko ban gane ina sonshi ba sai yanzu mai yasa na kamu da sonshi bayan shi ba sona yake ba haka ta kwanta a falo kaman jiya ga yunwa ga damuwa da ciwan kai, washe Gari da safe dakyar tayi sallah ta kwanta a wajan dan zazzabi takeji sosai ga jiri na dibanta.
Taku Maryam obam😘

CZYTASZ
TAMBARIN TALAKA
Krótkie Opowiadanialabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.