225to230

1.8K 74 1
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      225to230





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*









Ido ta lumshe wanda takeji yana mata zafi, ga kirjinta dake mata zafi shima saboda tsabar kishi dan mai yasa zaice zata dawo nan gidan? Harya manta abunda ya faru kenan lallai namiji dama gidanta yaje ya manta Dani shikenan yanzu zan fara ganin wulakanci kala2 wani hawaye taji ya zubo mata anya banyi kuskuren fadawa sonshi ba? Haba so mai yasa kamin haka mai yasa kasa na kamu da son wanda baya sona, jin tayi shuru yasa ya katse mata tunani da fadin Baby kinyi shuru karki sa wani abu a ranki Zainab ta fahimci tayi kuskure ta bada hakuri kuma so ita ta bukaci ku zauna Gida daya saboda hadin kanku, sannan inaso kisa a ranki babu abunda zai faru insha Allah plz ki bani hadin kai dan Allah, dan janyota yayi jikinshi tare da lakutan hancinta kasancewan dakin da duhu baiga hawayen da takeyi ba amma taba hancinta da yayi yaji hawaye tashi yayi da sauri ya zauna tare da fadin aysha kukan mai kikeyi? Bata kulashi ba saima juya Mai baya da tayi nan hankalinshi ya tashi dan baya son damuwanta,a hankali ya kira sunanta tare da fadin banyi zaton wannan abun zai Saki damuwa ba na dauka kema mai son zaman lafiya nane haba aysha karki manta......  Katseshi tayi da fadin ni bance maka komai ba kayi duk abunda kake ganin ya dace gidanka ne ban Isa in hanaka yin duk wani abu da kayi niya ba, ni nasan komai daya faru kaddara ne haka Allah ya tsara ina cikin wanda ba za suji dadi ba wahalan kishiya dana miji shine zai kashe ni mai yasa kake son kunna wuta a gidanka bayan kasan abubuwan dake faruwa kai a tunaninka hadamu Gida daya shine zaman lafiya? Inko haka kake tunani sam ba haka bane wlh idan ka hadamu Gida daya rigima ka hada da rashin kwanciyan hankali ni nasan dama baka kaunata kullum burinka ka kuntata min zanci gaba da zama dakai har Allah ya dauki rayuwa na tunda tawa kaddaran kenan tana fadin hakan kuka yaci karfinta tashi tayi da sauri tabar dakin tana kuka, hmmmm iya tashin hankali ya shiga tare dajin tausayinta inama zai iya bude mata zuciyarshi taga yanda soyayyarta ta mamaye ta, mai yasa aysha bazaki fahimce ni ba mai yasa kika kasa gane ina sonki da yawa, ido ya lumshe yana mai jin takaicin rashin fahimtan da take mai amma duk da haka bazai canza magana ba Zainab dai zata dawo gidan kaman yanda ya yanke shima tashi yayi yabar mata dakin ya nufi dakinshi baibi ta kanta ba.










Kitchen ta nufa tana ta faman aikin kuka tare da kokarin daura breakfast, fere dankali takeyi tana fadin mai yasa zai hadamu da Zainab bayan yasan abunda ta mata a baya da wanda tayi kwana biyu daya wuce dama nasan baya sona so suke su hadu suban wahala kara ta Saki tare da jefar da wukan kasa Hannu ta rike wanda yake zubar da jini domin ta yanke da wukar a yatsa A Majeed dake daki ya fito da sauri kasa ya nufa yaji gunjin kukanta a kitchen shiga yayi da sauri yaga ta rike hannu Jini na zuba, da sauri ya nufeta tare da riko hannun yana tambaya garin ya haka ya faru a hankali ta fara kokarin jan hannunta kallonta yayi tare da fadin plz ki daina baki ta turo kai ya girgiza tare da kamata sukai Sama yace kina da spirit banza Dashi tayi dan tasan spirit yana zafi a ciwo, dakinshi yayi da ita zaunar da ita yayi akan gadon dakin ya shiga toilet jim kadan sai gashi da kwalabe guda biyu da auduga spirit din ya fara zubawa tare da fadin muga hannun kai ta girgiza alaman a'a yace plz idan akasa zai daina zafi miko hannun tayi yana sawa ta Saki ihu tare da fashewa da kuka, dariya yayi tare da fadin u r a doctor fah shine kike irin wannan kukan, tace toh ba abun bane da zafi, yace toh sorry babyna zoki kwanta, tace ni bazan kwanta a nan ba a hankali tayi maganan yace mai kika ce, shuru tayi ba tare data kara nanatawa ba, yace Baby kina da rigima come on ya kamata ki fahimci mijinki na sonki kinga yanzu kinje kina bata ranki gashi kin yanke, a hankali tace toh bakai bane kaja, dan murmushi yayi tare da fadin Baby inaso ki fahimci wani abu yanzu da dah ba daya bane abubuwa sun canza basai na miki bayani ba keda kanki kin san hakan sannan idan Zainab ta dawo gidan nan gefenta daban naki daban kinga babu mai ganin wani sai in kunso hakan so ki daina tunanin wani abu kinji Baby na, hannunta ya kamo tare da fadin kice wani abu Baby, tace shikenan tunda ka riga ka yanke babu damuwa Allah ya kawar da fitina ya baka ikon yin adalci hugging dinta yayi tare da fadin ameen my baby nan yace suzo su koma bacci taki yarda wai zata koma kitchen dakyar ya barta tare da fadin kar tayi amfani da wukan kar ta kara yankewa tace ta yarda, duk da tasan dole nema tayi amfani Dashi din, wajan karfe goma ta gama komai tare dayin wanka tasa wasu English wear riga da mini skirt tayi mugun kyau kunyan fita taji tanayi tana tunanin ta shiga dakinshi haka koh tasa hijab bude kofar dakin yayi ya shigo ido ya kura mata domin tayi mugun kyau dan kunya taji yanda ya ganta a haka amma saita dake tare dayin baya ta zauna akan gadon dakin murmushi yayi tare da fadin u always look so pretty My angel, a hankali ta furta kalman thanks, karasowa yayi inda take tare da kwanciya yasa kanshi Akan cinyanta dake bude lumshe ido yayi domin jin kamshin jikinta a hankali yace Baby am hungry, tace muje dinning na gama breakfast, bude ido yayi tare dayi mata peck a ciki dariya tayi tare da kokarin tureshi shima dariyan ya fara sannan ya dagata suka nufi parlour kan dinning suka zauna tea ta hada mishi tare da zuba mai meat ball da sultan chips and egg sai parfesun naman rago, kallonta yayi tare da fadin Baby ke daya kikayi wannan aikin kai ta daga mai alaman eh, yaji dadi sosai yau zaici abinci a gidansa kuma matarshi ce ta dafa mai abunda yake buri yaga Zainab tayi kenan amma ta kasa sai son jiki gashi girkin ma bata iya ba, cin abincin ya fara yana lumshe ido dan yaji dadin meatball din sosai yaci da yawa ita ko indo tea tasha da Egg, tashi yayi yazo inda take ya fara bata meatball din bata da niyan ci amma dole yasa taci harta ture kai alaman ta koshi sannan ya barta, kujeran falon suka koma suna fira gwanin Sha'awa duk da hankalinta ba'a wajanshi yake ba Tana tunanin irin zaman da za suyi da Zainab idan ta dawo gidan, ido ya kura mata ganin bata magana a hankali ya hura mata Iska a fuska ido ta lumshe lokaci daya kuma ta bude ido yace tunanin mai akeyi Baby? Dan murmushi tayi tare da fadin tunaninka nakeyi dariya yayi yace are u sure? Tace yes haka ta saki jiki sukai ta fira gwanin Sha'awa.










TAMBARIN TALAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora