160to165

1.6K 68 1
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      160to165





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*









Gaba daya ta gama sa abunda zata bukata cikin akwati, duk da ba komai ta dauka ba, fita tazo yi amma saita tsinta kanta da kasa bude kofar dakin, domin tunanin alkawarin da tayi ma Mum ya fado mata, bani da yawan dangi koh yara, naso ki zauna dani har abada sai dai hakan bamai yuhuwa bane dan za kiyi aure May be Ma mijin da kika aura ya hanaki hulda dani, sakan akwatin tayi tana kara rusar kuka, tunawa tayi da amsan da taba Mum, bazan taba barinki ba mum duk mijin dazan aura dole ya soki a matsayin Mum dina, zama tayi a wajan tana kuka gwanin tausayi, mai yasa talaka bashi da gata mai yasa wanda bashi da iyaye yafi shiga irin wannan matsanacin rayuwan mai yasa, A Majeed mai yasa kake son Sani cikin kunci koda yaushe mai yasa maina maka, ni nasan bawai dan kana sona dagaskiya kake wannan abunba, kanayi ne dan wata manufa taka ta daban, dan shuru tayi kaman Tana dan nazari lokaci daya kuma ta lumshe ido hawaye na zuba jin karan wayanta ne yasa to bude ido Bros taga an rubuta da sauri ta dauka tare dayin sallama, bayan ya amsa yace sister lafiya Kuwa?  Naji muryanki kaman mai kuka, dan murmushi tayi na karfin hali Kafin tace lafiya qalau bros, yace ya mai jikin da fatan dai da sauki koh?  Tace eh Alhmdlh da sauki bros, nan suka taba dan fira kafin sukai sallama akan cewa gobe zaizo gidan, yana kashewa kiran yazeed ya shigo wayanta, kaman karta dauka harya kusa tsinkewa ta dauka tare da fadin Hello, daka gefenshi shima ya amsa da fadin barka da dare, dan lumshe ido tayi tare da fadin barka kadai, yaka koma Gida? Ya amsa da lafiya dan shuru ya biyo baya, jin muryanshi tayi yana fadin aysha tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki a raina, sai dai kuma a lokacin baki bani lokaci ba dan kin nuna kina sauri, amma haka zuciyata taci gaba da tunaninki duk da ban san inda zan kuma ganinki ba, sai dai nabar ma Allah komai sai gashi kuma ya kara hadamu cikin sauki wanda ina fata wannan karan zai zama shine hanyar da zamu kasance har abada, domin dai ni bada wasa nazo ba, dagaske nake aurenki zanyi sannan bana son ya dauki Lokaci mai tsawo, amma fah inkin amince dani, dan shuru yayi alaman yana jiran amsa, kanta ne ya kulle tama rasa abunda zata ce mai jin muryanshi tayi yana fadin ban samu karbuwa bako? Tace a'a yaya yazeed na amince Allah yasa hakan shine alkhairi, cikin jin dadi ya amsa da ameen, tare da fadin insha Allah zaki farin cikin kasancewa mata2 sannan dan Allah inaso kar aja da tsawo inaso ayi komai nanda wata biyu, bata iya cewa komai ba dan tama rasa abunda zata cemai tadai yardan mishi ne kawai badan tana sonshi ba ko Tana jin wani abu a kanshi ba, sai dai auren nashi zaisa tabar gidan nan gaba daya hakan zaiba A Majeed daman tashi tare da wargajewar wani abu da yake nufi a kanta, jin tayi shuru yasa yazeed ya kira sunanta tare da fadin gobe zanzo sai muyi magana, tace Allah ya kaimu tare da kashe wayan, Mum ce ta shigo dakin ta ganta a bakin kofa ga akwati a gefenta, kallon akwatin tayi sannan ta Kalli indo wacce fuskan ta tayi ja ga idonta duk ya kumbura dan kuka kun san farar Mace, Mum tace aysha lafiya kuwa? Maiya sameki wannan akwatin fah? Badai kina nufin Zaki barni bane,? Wannan tambayar duk a lokaci daya Mum ta mata shi, indo gaba daya kunya ya hanata magana dan bata so Mum ta shigo dakinba ba tare data maida komai wajanshi ba, mum ta tsugunna tare da kiran sunan aysha tace aysha mai aka miki da zakiyi irin wannan danyan aikin, koh wani ne ya bata miki rai? Indo kuka ta kuma saki tare da fadin Dan Allah mum kiyi hakuri wlh na rasa abunyi ne, gaba daya komai ya jagule min Mum dan Allah karki min wani fahimta ta daban....  Kuka yaci karfinta dan haka tayi shuru ba tare data karasa abunda tayi niyan fada ba, Mum janyota tayi jikinta Tana shafa mata baya tare da fadin aysha na fahimce ki, amma mai yasa ba zaki iya fadamin abunda yake damunki ba, saiki yanke hukunci dakanki? Cikin murya mai sanyi tace Mum A Majeed yana son kara bata min rayuwa Mum......  Shuru tayi dan tunawa dawa take magana, jin muryan Mum tayi Tana fadin aysha kiyi hakuri A Majeed bai isa yasa kiyi abunda baki niya ba, bashi da iko akanki, sannan ba zamanshi kike ba, kiyi shuru ki daina damuwa da komai kinji, bazan bari ya kara miki wani magana makamancin hakan ba, sannan idan kina da wanda kike So ki bashi dama ya fito kinji? Ido kasa amsa ma mum tayi dan gaba daya jikinta yayi sanyi, tare dajin kunya yau gashi Tana nuna bata son jinin Mum, wani hawaye mai zafi ya zubo mata sai dai hakan bazai sa ta canza ra'ayi ba, dan tasan bawai sonta yake ba, yaudara ce kawai irin tashi, shida yake da zee mai zaiyi da ita, gata yar masu arziki nida ba yar kowa ba, bazan iya kishi da itaba .... Wata zuciyar tace mata sai kace ba Mace ba, ai indai Mace ce ko wacece zaki iya zaman kishi da ita, ido ta lumshe ba tare data gamsu ba, Mum ce ta katse mata tunani tare da fadin tashi kije kiyi wanka ki sauko kici abinci, tashi tayi ta nufi toilet Mum kuma tabar dakin, ta nufi dakin dan nata dan taga ya yake ciki.





Mum bayan ta shiga dakin taga dady a kusa dashi yana dan mishi fiffita duk da akwai AC a cikin dakin, amma zufa yakeyi, cikin damuwa tace zafi yakeji? Wajan gadon ta nufa taga yanda yake zufa, hannu tasa a fuskanshi Tana share mai zufan fuskan nashi, tare da fadin son, idonshi dake lumshe ya bude, ya kura ma mum din ido, gabanta ne ya fadi ganin irin ramar da yayi lokaci daya, tace mai yake Damunka? Dad yace wannan wani irin tambaya ne fatima bayan kin san komai, tace dan Allah ka bari yaban amsa domin inaso inji da bakinshi kuma cikin hayyacinshi, Dad shuru yayi amma ranshi a bace yake dan gaskiya abun yana matukar damunshi wai tilon dan nashi ne yake kwance babu lafiya gashi yaki bari a kaishi asibiti, duk da ya bayyana matsalanshi amma Mum tana nunawa kaman bata damu ba, lallai komai ya samu danshi laifin Mum ne.... Jin muryan A Majeed ne ya katseshi da yake fadin Mum babu abunda yake damuna Just kawai ina son inbar kasar jibi shine kawai nake So, Dad yace son indai zaka cire komai a ranka a gobe ma zaka sami flight, yace yes Dad plz inason fita london, I need to rest for some month , Dad yace shikenan amma sai kamin promises zaka ga Dr a can? Yace I promise Dad, cikin jin dadi Dad din yace shikenan saika shirya,gobe 6 in d morning zaku tashi, inda badan dare yayi ba da yau zaka tashi, A  Majeed yaji dadin hakan duk da zuciyarshi a tunkushe yake yana son ganin aysha ko zaiji dadi sai dai bazai nemeta ba dan Yana son yayi nesa da ita ko hakan zaisa ya Manta da ita, dan lumshe ido yayi yana mai jin zafi a ranshi, Mum kam kasa magana tayi gnin Dad ya fita daka dakin yasa ta kalli dan nata tace mai zaka ci son?kai ya girgiza alaman babu komai, Mum tace haba son ya zaka zauna kana ciwo kaki cin komai, plz tell me mai kke son ci? Yace aysha plz am o.... Bai karasa ba yayi shuru dan jin sunan daya kira Mum din nashi dashi, Mum dan murmushi tayi tare da tashi ta fita daka dakin, tashi yayi dakyar ya nufi toilet, ya dade a ciki sai gashi ya fito da towel a kanshi alaman dai yayi wanka, yana tafiya kaman babu jini a jikinshi domin gaba daya babu kwari a jikin nasa, jallabiya yasa, tare da zama akan gadon kayan aikin indo ya gani da sauri ya kawar da kanshi Dan baya son gninsu dan So yake ya manta da komai nata, duk da yasan hakan ba abu bane mai yuhuwa, kwanciya yayi ta baya yana ganinta a idonshi yana cikin haka Mum ta shigo dauke da tray a hannunta ajiyewa tayi akan Side drawer, tace son tashi kaci abinci koh kadan ne kaji? Tashi yayi yana kallon Mum sannan yace Mum bana jin yunwa, tace Abdul-majeed ka daina horar da kanka, wannan abunda kakeyi bashi zai kawo maka karshen wannan matsalan da kake ciki ba, kallon Mum yayi da sauri ta daga mai kai alaman eh, zaiyi magana tace mai Ya Isa haka tare da bashi Tea din data Kawo mai da snack, amsa yayi ya fara ci tare da tunanin mai Mum ke nufi, suna cikin haka Abdul ya shigo dkin hankali a tashe, ganin A Majeed din yana shan Tea yasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin kama warke Ashe, karaso wa yayi ya gaida Mum, inda take tambayanshi kwana biyu yace wlh Mum naje Kaduna ne amma wannan karan anyi nasara komai ya daidaita yayar yarinyar Ashe wai Tana tsoran bata mai kudi ne saboda gudun wulakanci dakyar dai aka shawo kan matsalan, ni da farko ma nasha ko rikonta take Ashe yayarta ce, Mum tace toh Alhmdlh yanzu saura musha biki kawai, dariya yayi ba tare da yace komai ba, Mum fita tayi ta barsu,Abdul matsawa yayi kusa da abokin shi, yace kai Man irin wannan rama haka gskiya kaji jiki fah, wai maike damunka ne haka? A Majeed yace aysha, Abdul yace aysha kuma? Kai ya daga mai alaman eh, Abdul dariya yayi tare da fadin wai mai kake nufi ne? Kodai ka sami wata chicks ne, dan tsaki yayi kalan na mai jin jiki, kafin yace kana da matsala Abdul wace aysha nake nufi inba matata ba, abdul yace wannan yar kauyen? Cije baki A Majeed yayi tare da ajiye Cup din Tea din ya kwanta, Abdul yace haba Man magana zaka yi, A Majeed cikin murya irin name jin jiki yace, Abdul joke apart ina son aysha sosai duk wannan abunda nake ciki saboda sonta nake cikinsa, ban taba jin wani abu akan wata Mace ba kaman yanda nakeji akanta, Abdul nayi nadaman abubuwan dana mata duk da a lokacin wani abun bada san raina nake mata ba, dan Allah ka tayani bata hakuri dan nasan zata iya jin maganan ka, bance lallai saita soni ba amma ta yafe min,ta cire komai dana mata a ranta duk irin son da nake mata bazan matsa mata akan dole saita soni ba, dan bazan iya auren macen da bata jin wani abu a kaina ba, am not dat selfish, koda sonta zai kashe ni bazan matsa mata dole ba dat Why na yanke decision akan inbar kasar ko zan manta komai duk da nasan ba abu bane mai sauki, but I will try, domin gaba daya bata san ganina kaman yanda na fahimta indai nesa da ita da zanyi will make her happy, I will do anything just to c her happy .... Dan shuru yayi domin jin zafin da kirjinshi yake yi, Abdul ne ya tabashi tare da fadin karka damu Man zan mata magana and I knw baza tayi rejecting dinka ba, abunda naji dadi shine ka fahimci abunda Mum take nuna maka akan aysha din,wanda tun farko kaki ka fahimta saida lokaci ya kure but i will try inga komai ya koma normal insha Allah.......  Toh fah ku biyoni kuji ynda zata kaya...







Taku maryam obam😘

TAMBARIN TALAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora