*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA**🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
240to245
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*Kwashe yaran akayi ganin kaman bata motsi yasa aka sa mata oxygen amma baya moving gaba daya Dr din sun sadakar ta rasu lokaci daya kuma oxygen din ya fara tafiya alaman Tana da rai tayi doguwan suma ne, nan sukayi kanta ana dubata tayi wajan 30 mnt Tana numfashi a lokacin an kimtsa yaran sannan Dr din da kanta tasa nurse suka tayata kamata akai toilet da ita dakanta Dr din ta mata wanka har lokacin idanta a lumshe yake bata bude ba da duka alamu bata cikin hayyacinta har Dr din ta gama gyara mata jiki Sannan tasa mata wata doguwar riga daka cikin kayanta da suka zo Dashi tare da pad, Dr din ta fita da sauri A Majeed ya matsa kusa da ita yana tambaya tace congratulations ur wife give birth to triple yace yan uku, Dr tace yes a hankali yace itafa hope babu abunda ya sameta? Dr tayi shuru ba tare da tace komai ba yace Dr ta mutu ta mutu koh Dr tace bata mutu ba amma har yanzu bata farfado ba jikinta yayi weak Allah yasa ta haiyu da kanta ba'a kai dayi mata aikin ba yanzu sai mu jira kadan muga yanda abun zai kasance, da sauri yace Dr zan Iya ganinta tace eh amma ka bari a kaita dakin hutu nurses ne suka fito da yaran Mum da Dad suka amsa Zainab ta amshi daya itama A Majeed kam ko kallon yaran baiyi ba danshi burinshi yaga matarshi kawai yaran kyawawa kaman babansu sak gasu farare tas dasu duka kamansu daya sai dai macen ta fisu haske sosai, Zainab wani irin hawaye ne ya zubo mata wannan ne rana ta farko da taji Sha'awar haiyuwa domin yaran sun burgeta dana sanin shan maganin hana daukan ciki duk taji ya kamata lallai itama Tana bukatan haiyuwa duk da lokacin da tasan indo nada ciki ta daina shan maganin amma har yanzu batai ciki ba dole taje hspt a dubata dan itama Tana da bukatan haiyuwa a yanzu, fito da indo akayi akan gadon marasa lafiya ana turata hankalinsu duka ya koma kan gadon A Majeed Da sauri ya nufi gadon tare da rike mata hannu yana hawaye kaman karamin yaro har dakin da za'a kaita suka shiga hannunshi na manne da nata yana hawaye tare da fadin get up aysha tashi kiga yaranki plz kowa dake wajan yaji tausayinshi musamman yusuf da yake ganin gudan kanwar tashi a kwance bata motsi iya tashin hankali shima ya shiga Mum ce ta dafa ma A Majeed baya tare da fadin son kayi hakuri insha Allah zata tashi rungume Mum yayi yana kuka Mum nata bashi baki lokaci daya indo ta bude ido Tana ganin wani irin dishi2 a hankali ta Gama bude idan ta ganta a kwance mutanan dakin ta fara kallo lokaci daya kuma abunda ya faru ya dawo mata ido ta kuma lumshewa sannan ta bude karaf ya sauka akan na A Majeed Da sauri ya kira sunanta da aysha murmushi ta sakar mai da sauri yace mum ta tashi Alhmdlh nan Yusuf ya fita ya kira Dr ta dubata tace komai normal dama ta tsorata ne sosai tun farko shiya ja mata suman da tayi yanzu dole ta kwana dan muga yanayin jikin, sai a sannan A Majeed ya kalli yaran tare da amsar wanda ke hannun mum ya mika ma indo tare da fadin kinga dani suke kama dariya tayi kowa ya fara mata sannu tare da barka fita Su Mum sukayi aka barta ita da mijinta zainab kam Gida ta wuce nan A Majeed ya fara fadin aysha dama nasan ba zaki mutu ki barni ba dariya tayi tare da fadin hakane nima bazan so in tafi in barka ba kodan yarana ma zanso in rayu dan kar suyi rayuwa irin nawa, matseta yayi da karfi a jikinshi yana fadin I love You baby macen ce ta tsala ihu da sauri ya Saki indo ya dauketa yana jijjigata Mum ce ta shigo ta amshi yarinyar tare da bama indo ita tace yunwa take ji, indo kunyan amsan yarinyar tayi mum tace amsheta mana aysha babu yanda ta Iya dole ta amsa tare da fadin Mum ina kayana? Mom ta janyo mata akwati ta Dan tashi kadan ta dauko hijab tasa sannan ta Fara bama yarinyar nono Mum dariya tayi tare da barin dakin ganin Mum ta fita yasa A Majeed komawa kusa da matar tashi yana ma sauran yaran wasa, inna Maryam ce ta shigo dakin ita da mum hannunsu dauke da basket bayansu mai aikin Mum ce dauke da flask da kayan tea indo tace inna Maryam saukan yaushe? Tace yanzu nan indo ta gaidata inna maryam ta amsa tare dayi ma indo barka, inna Maryam ta hadama indo Tea mai kauri tare da zuba mata farfesun naman rago amsan yarinyar tayi ta ajiyeta sannan taba indo Tea din da naman amsa tayi ta Fara ci duka naman ta cinye inna Maryam tace bari a karo miki tace a'a ya isa, A Majeed yaso ya kwana wajan matarshi Mum ta korashi inna Maryam ce ta kwana da ita Yusuf suma suka shigo suka kara yi mata barka tare da sallama suka wuce washe Gari wajan karfe 7 A Majeed yazo asibitin nan inna Maryam take ta tsokananshi wai yayi sammako shidai babu abunda yake yi sai dariya wai yau shine yake da yara har uku, ikon Allah, mum itama tazo asibitin tare da abinci nan aka zuba ma indo shima zama yayi suna ci tare Mum fita tayi dan taga dan nata wani sabon fitsara ya koyo, Abdul Da matarshi suma sun zo asibitin Sun dade kafin suka tafi A Majeed babu abunda yake sai daukar yaran hoto sai wajan karfe 5 Dr ta sallamesu dan taga jikin da sauki, gidan Mum suka nufa direct, A Majeed sai kashe kudi yake tayi akan yaran Zainab bata kara zuwa ba tunda tabar asibiti dan tace sai ran suna zata ta gefen Mum ma sai kashe ma yaran kudi take tayi......... Yau akayi sunan yaran inda aka kashe naira kaman babu gobe namijin yaci sunan dad muhd suna kiranshi da irfan dayan kuma Aminu sunan mahaifin indo suna kiranshi arfan macen kuma sunan Mum fatima suna kiranta da zarah Zainab itama tama yaran kaya na kece raina duk da tana jin kishi amma Allah yasa mata son yaran sosai a ranta, haka akaci suna aka watse kowa nasan barka, saida indo tayi arba'in sannan ta koma gidanta Mum tasa an hada mata ita sosai yanzu da masu aiki uku aka hadata dasu, koda ta koma Gida taga dakin da aka ware ma yaran an kashe kudi sosai komai ansa na wasan yara kala2 ga gadajensu nan guda uku kowa da nashi ji tayi an rikota ta baya ihu tasa a hankali ya furta kin cika tsoro Baby dariya tayi tare da turo baki kuma yace mai nene kuma? Tace nayi missing dinka yace really toh muje a amshe ni ido ta zaro tare da fadin ba irin Wannan missing din ba yace toh ni nayi wata nawa banji dumin jikinki ba dariya tasa tare dayin dakinta da gudu shima binta yayi a dakin yaga yaran ko wanne adan gadonshi mai keke yana tura Su, yace Baby nikam mai zan miki kiji dadi a rayuwa? Dan shuru tayi can tace inaso inje garinmu domin inga inna tani da Baba Musa, shuru yayi kafin yace banda wannan mai kuma kike so dariya tayi tare da fadin soyayyan miji na, yace ai kin samu tun tuni yace plz tell me mai kike so? Tace kaman yanda nace inason zuwa garinmu da kuma soyayyarka, yace shikenan ki bari yara suyi kwari sai muje kinji kai ta daga alaman toh nan aka shiga duniyar da yara basa zuwa sai sun girma😝 ranan dukansu Sun san sunyi missing din junansu sosai watan indo biyu da haiyuwa ta fara aiki a hspt dinta lokaci kadan tayi suna sosai danta kware a aikinta abban Yusuf ya sami lafiya sosai babu inda baya zuwa gashi Yusuf ya rike Mai amana na dukiyarshi dan lokacin da yake ciwo Yusuf yake ta juya dukiyar gashi an sami riba sosai ganin haka yasa yace Yusuf yaci gaba da juya kudin sannan ya dinga raba riban uku biyu na Yusuf daya nashi Yusuf rasa bakin godiya yayi dan murna a lokacin zaliha Tana dauke da ciki itama na wata 7 Yusuf ya kara kudi sosai ya kara kyau da girma.

VOCÊ ESTÁ LENDO
TAMBARIN TALAKA
Contolabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.