150to155

1.5K 70 1
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      150to155





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*







Dan shuru yayi sannan yaci gaba da fadin lokacin da naje taraba direct gidan Mai gari na nufa lokacin bai ganeni ba, saida na mishi bayani yayi mamaki kwarai dagaske tare da bani hakuri akan abunda ya faru, nan yake shaidamin kinyi aure ya bani labarin yanda abun ya kasance nayi takaici lokacin sosai haka nabar garin ba tare da naje Gida ba, domin nasan har yau babu abunda ya canza daka zuciyar kawu akan kiyayyar da yake mana, duk da mai gari ya fadamin wanda kika aura hankalina bai sa ya kwanta ba lokacin saida nayi bincike sosai akai naji dan sanyi kullum ina da burin inje in ganki amma babu dama domin shiga gidan governor ba abu bane mai sauki, haka na hakura duk da a lokacin inda na fadama abba zaisan yanda za'ayi in ganki amma sai nayi shuru nabar abun a raina, ana cikin haka abba yaban auren zaliha muka tafi london saboda karatun ta, inda nima naci gaba da masters dina a yanzu haka mun kammala ta haiyu yau kwana biyar jibi suna, indo cikin muryan kuka tace gskiya yaya yusuf kasha wahala a rayuwa sosai amma Allah da yake mai rahma ne saiya hadaka da masu tausayama, ta Kalli abba dake zaune tace Allah ya saka maka abba samun mutum irinka zaiyi wuya a rayuwa Allah ya baka lafiya, duka Suka amsa da ameen, sannan ta kalli yazeed tace yaya yazeed kaima Allah ya biyaka, murmushi yazeed ya mata, sannan ta kalli ummi tace ummi Allah Ya saka muku da gidan Aljanna, tashi tayi da sauri ta dauki yaron yayan nata dake hannun zaliha, Tana kallonshi cike da kaunar yaron dan uwan nata, tace anty zaliha yaron da yaya yake kama zaliha murmushi tayi tare da fadin kai sister wannan son kai haka, dariya duka suka sa, yusuf yace sister yanzu a ina kike yaranki nawa? Dan shuru tayi tare da hawaye tace yaya yusuf bani da aure yanzu, yace mijinki fah maiya faru? Nan ta bashi labari da irin abubuwan da suka faru tun daka kauye har haduwanta da Abdul da irin taimakon daya mata shida Mum, amma ta boye musu irin abunda A Majeed ya mata sai dai tace sun rabu ne a bisa kaddara wanda haka Allah ya tsara yazeed jin haka yasa ya saukar da ajiyan zuciya wanda tun sanda yaji yusuf yace an Mata aure ya shiga damuwa, yusuf yace gskiya sister kema kin hadu da mutane musu kirki tabbas na Allah basa karewa duk da akwai marasa kirki amma Na Allah sunfi yawa marasa kirkin kadan ne,sai dai Sunfi kaurin suna, yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa daya sake hadamu, indo ce ta tashi tare da fadin Bros inaga zan tafi sai gobe zanzo, kallonta yusuf yayi tare da fadin sister har zaki Iya tafiya kibar ni Ai bazan yarda da hakan ba, zadai kije ki dibo kayanki ki dawo Gida na, sannan Kafin ki dawo zanje inyi musu godiya duk da nasan kalman godiya tayi kadan, sai a lokacin ummi tayi magana tare da fadin haba yusuf ai hakan inaga ba daidai bane ace lokaci daya tabar su, ai hakan ba adalci bane, abba yayi gyaran murya shima yace hakane ka barta tayi shawara da kanta Akan abunda ya dace tayi, yusuf yace shikenan abba, indo tayi dan murmushi tare da fadin Bros yaron Mum ne bashi da lafiya nan ta basu labarin yanda ta fito ta barsu, yusuf yace subhanallah Allah ya bashi lafiya kije kiji yanda ake ciki gobe nima zanzo insha Allah, yazeed ne ya tashi shima Amma ranshi a dan jagule dan ya gane A Majeed shita aura suka rabu kuma gashi Tana wani nuna damuwa akanshi dan baida lfya... Yusuf ne ya katseshi da fadin kaima tashi kayi, yace eh nan sukai sallama indo da yusuf da yazeed suka fita, yusuf yace ya ajiye indo a Gida plz baya son barin abba shi daya hakan akayi motar yazeed ta shiga bayan sunyi exchanging number da dan uwan nata, Tana gaba yazeed na tuki yana ta dan janta da hira sama2 take bashi amsa har suka karaso inda ya nemi ta bashi number dinta shima bata musa ba ta bashi sannan sukai sallama ta shiga Ciki.










Kai tsaye falon gidan ta shiga babu kowa, haurawa sama tayi bata ga kowa ba, dan haka ta kira Mum bugu daya ta dauka tare da fadin aysha.....  Indo tace Mum na dawo ban ganki ba, Mum tace aysha wlh gani gidan A Majeed tun dazu muke fama dashi akan muje hspt yaki, kana jin muryan Mum kasan Tana cikin damuwa, wai babu inda zashi aysha na rasa gane mai yake nufi.....  Indo tace gani nan zuwa Mum, indo jiki a sanyaye ta fada toilet tayi wanka tare dayin alwala tayi sallah La'asar dan ankira tun dazu batayi ba, wata doguwar riga tasa ta fita taxi tahau bata jira driver ya kaita ba kai tsaye gidan aka nufa da ita, jiki a sanyaye ta fita taba mai mota kudin, tayi wajan minti uku Tana dan tuna abunda ya faru baya a cikin gidan hawaye ne ya silalo mata tasa hannu ta goge ta nufi Gate din Tana bugawa kirjinta nata dukan uku2,mai gadi ne ya leko duk da bawai ya santa bane ya bari ta shiga, a falo taga dady yasa hannu akai alaman damuwa, indo ta gaidashi cikin sanyin jiki, yace aysha sannu tare da fada mata Mum na ciki direct dakin ta shiga wanda yau ne ta taba shiga duk zamanta a gidan a baya, Tana bude kofar ta hangoshi kwance akan gadon da alama bacci yakeyi daka shi sai singlet Da 3quater jeans ya rame lokaci daya hannunshi an makala mai drive, wani hawaye ne ya zubo mata a fuska lokaci daya tare dajin tausayin shi, dai2 lokacin Mum ta waigo tace aysha karaso mana, karasa shiga tayi tare da fadin Mum ya jikin nasa? Mum tace toh da sauki dai na musulunci, tunda muka zo muke ta fama muje asibiti yaki yarda wai mu barshi kawai..... Hawaye ne ya zubo ma Mum cikin damuwa taci gaba da fadin aysha A Majeed shi daya gareni gashi a kwance yana fadin a barshi kar'a kaishi asibiti wai mutuwa zaiyi, indo itama hawayen take, Mum tace dakyar ya bari akasa mishi wannan Drive din wlh aysha A Majeed yayi mugun d'agamin hankali a yanda muka sameshi yanzu anyi mishi alluran bacci tunda akamai har yanzu bai farka ba, indo tace Mum kiyi hakuri zafin ciwo ne kawai insha Allah zai tashi babu abunda zai sameshi, mai Dr yace akai, nan mum ta bata wata takarda da Dr yace za'ayi mishi scan da test din da Dr yayi mishi da dan rubuce2 da akayi, indo amsa tayi ta fara dubawa, kallon Mum tayi kaman za tayi magana kuma tayi shuru, wata nurse ce ta shigo dakin danta duba ko ruwan ya kare, indo tace mata ta bata number din dr din nurse din ta fadama indo ta rubutu, fita waje tayi dan ta kira Dr din, dialing number din tayi bayan an dauka ta fadama Dr din koh ita wacece inda ta rokeshi akan ya tura mata sauran bayanan ta email dinta yace mata ok, jingina tayi a jikin motar Dad, Tana tunani, lokaci daya tace no hakan bazai faru ba, nasan dai matsalan matarshi ne yake damunshi duba wayanta tayi taga an tura mata dan haka ta fara karantawa harta gama, fita tayi daka gidan, bata dade ba sai gata ta dawo da leda a hannunta, Dad yana falo har yanzu yace aysha zoki zauna inada magana dake, zama tayi a gefen kujeran tare da sunkuyar da kanta a kasa, Dad yace aysha miye tsakaninki da A Majeed?  Dam taji gabanta ya fadi dai2 lokacin Mum ta fito Tana fadin aysha tashi ki shiga ciki, Dad ido yabi Mum Dashi cikin mamaki indo tashi tayi Tana mamakin mai Dad yake son Sani, bata karasa dakin ba taji Mum na fadin haba mai yasa za kayi haka, karka manta irin abubuwan da suka faru a baya nida kaina ina son aysha da abdul-majeed amma dan Allah karka fada mata karta daukemu  marasa adalci masu san kammu da yawa, duk da a yau ina cikin damuwa ga tilon dana a kwance rai a hannun Allah bazai sa ince aysha ta aureshi ba, tunda nayi hakan a farko maiya haifar koda kaji yana fadin aysha ina sonki karka manta yana cikin zafin ciwo ne bai san inda kanshi yake ba....... Indo data tsaya tana ji da sauri ta shige dakin da A Majeed din yake an cire mai drive din, yana kwance abunshi, kuka ta fara mai tsuma zuciya zama tayi a kan gadon Tana kallonshi yayi mugun ramewa sosai jin hannunta tayi cikin nashi ya rike da sauri ta kalleshi amma taga har yanzu bacci yakeyi, kallon hannun Nata tayi wanda ya rike da karfi, wani hawaye ya zubar mata mai zafi lallai Mum ta cika uwa ta Gari mai sadaukar da ran nata dan ta faranta ma bare, wani hawaye ya kuma zubar mata mai zafi dan harga Allah bataji zata Iya aurenshi a karo Na biyu domin har yanzu ta kasa cire abunda ya faru a ranta ,jin kaman yana magana Yasa takai kunnenta dan taji mai yake fada dayan hannunshi yasa ya riketa dole yasa ta kwanto a jikinshi wanda maganan da yakeyi kaman mafarki ne tunda bacci yakeyi, wani irin kasala taji ya kamata ta fara kokarin tashi amma sai taji ya kuma rikota yasa dayan hannunshi ya rungomota dakyau  kirjinta ya shiga bugawa da Sauri........








Taku Maryam obam😘

TAMBARIN TALAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora