205to210

1.5K 70 3
                                        

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*




                     *NA*

                    
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*


*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*




*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*


https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/







                      205to210





*DEDICATED  TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*






Daura hannu a fuska tayi alaman tagumi, toh ni daba ni akama haka ba nashiga damuwa ina gashi, zuciyarta ta fara mata tunani kala2 mai yasa baibi matarshi ba ya dawo nan, ina ita zainab din take? Tana cikin wannan tunanin taji hayaniya tare da buga kofar parlour din, bude kofar tayi Zainab ce tare da sodoji mata Da maza, kallo ta karema indo dashi Tana mamaki dama balarabiya ya aura, lokaci daya ta cakumi wuyan indo tare da fito da ita waje tayi jifa da ita, indo tayi tangal2 zata fadi amma sai ta fada jikin motar dake pake a wajan, Zainab tace dan ubanki sai kin koma kasarku da kafanki shegiya yar Iska can kasar taku kin rasa mijin aure ne da zaki aure min miji yar Iska, saina canza miki kamanni yau sai kin san kinyi babban kuskure nufanta ta kuma yi, ta wanketa da mari a dai2 lokacin A Majeed ya fito yaja Zainab da karfi tare da wanke mata fuska da mari itama kallonshi ta tsaya yi da mamaki abunda bai taba yi mata ba, kai zama ta iya rantsewa da cewa A Majeed bazai iya dukan ko wace mace ba domin baya daya daka cikin maza masu dukan mata, hannun indo ya kamo tare da fadin bata ji miki ciwo badai koh? Indo babu abunda take sai hawaye tare dajin takaicin abunda Zainab ta Mata yau, jan hannunta tayi daka nashi dai2 lokacin Zainab ta kuma zaburowa tare da fadin nika mara A Majeed akan wata Mace ka Manta wacece ni? Dan murmushi tayi tare da fadin u will regret it, kallon sodojin da tazo dasu tayi tace ku kama min wannan yar iskan kuyi ta duka har sai nace ku barta, matan ne suka fara tawowa alaman zasu bigeta din, A Majeed Ya daka musu tsawa tare da fadin get out of My house tare da nuna masu hanya, Zainab tace baka isa ka basu command ba sai abunda nace kallonsu tayi tace what r you waiting? A Majeed yace duk wanda ya kara wani step a cikinku sai an cire mai uniform dukansu suka tsaya domin sun rasa maganan wa za subi, A Majeed yace wlh idan kika kara wani abu I will teach you a lesson, tace kai waye baka isa kayi min komai ba kuma wlh sai sunci ubanta yau, indo zagin da ake mata ranta ya baci sosai dan idan da ta tsaya ana zaginta yanzu ba zata bari ba, nufan Zainab tayi tare da fadin ki kwantar da hankalinki indai mijinki ne gashi nan dan baya gabana tana fadin haka tabar wajan A Majeed kam ranshi ne ya baci dajin kalaman indo din, Zainab kam shewa ta Saki tare da fadin toh kaifa kaji saika sallameta ashe yar Nigeria cema shegia zabiya, A Majeed Da ranshi ya baci sosai baibi ta kanta ba ya wuce ciki, itama binshi tayi tana fadin ai wlh sai ka koro shegiyar tabar gidan nan, zama yayi a falo ranshi a bace, yama rasa abunyi gaba daya ga ranshi dake a mugun bace, tace kafa tashi kaje ka koro wannan shegiyar, indo ce ta fito ta yafa Gyale a kanta Zainab tace Yar Iska sai kinyi dana sanin auren min miji, sadaka yalla, indo ranta ya gama baci hakurinta ya kare abunda tai niyan yi saita tsinta kanta da fasawa, tace dafarko naga dai baki ganeni ba bari kiji nice dai kishiyar ki wacce aka miki tun farko yanzu kuma gani a gidanki a karo na biyu, Zainab kallon Indo take tayi tabbas sai yanzu taga kaman wani uban ashar ta saki tare da fadin dama na dade ina neman irin wannan daman da Allah zai hadani dake yanzu kam gani ga ki, cakuman indo tayi da nufin dukanta indo ta tureta da karfi tare da fadin karki kuskura yanzu bada bane sannan inaso ki sani ni aysha zan zauna a matsayin kishiyarki indai hakan kike so in kuma kin canza zan zauna a matsayin yar uwarki, Zainab tace yar uwar uwarki A Majeed tashi yayi yaja hannun Zainab yayi hanyar waje da ita ta fara kokarin kwacewa tare da fadin ka sake min hannu, saida ya kaita waje ya rufe kofar sannan ya dawo yace ma sodojin subar mai Gida fita sukayi tana ganin an bude gate din ta kara shigowa Da gudu tayi hanyar falon shima rufa mata baya yayi yana shiga yaga suna kokowa ranshi ya kuma baci ya fizge Zainab din tare da wanketa da mari har biyu wani uban ihu ta Saki tare da fadin akan wannan yar matsiyatan ka mareni abdul-majeed wlh ka mari Bala'i ke kuma ki jira dawowa Na, fita tayi fuuuuu tabar parlour shima rufa mata baya yayi tana fita ya kalli mai gadin yace karya kara barin kowa ya shigo mai Gida, yace ok sir ciki ya koma koda ya koma baiga indo ba bai bi ta kanta ba dan yana fushi da ita itama dan maganan data fada yafi mishi ciwo akan abunda Zainab tayi ni mijinki baya gabana, kwanciya yayi akan gado tare da lumshe ido yana mai jin zafin abun,  itama ta gefenta kuka take tayi tare dajin haushin shi domin tana ganin duk shine yaja komai tunda ya nace saiya aureta gashi abunda take gudu ta fara gani, wata zuciyar tace kai karki ce haka yana sonki dagaske baki ga yau harda marin Zainab yayi saboda ke ba, ya kamata ki sallama kema ki soshi domin son tsakani da Allah yake miki, lallai hakane tunawa ta farayi da abubuwan da suka faru Baya duk abunda Zainab tace baya iya ce mata No, tuna abunda inna Maryam ta fada mata tayi tace kinga yanda zaki kwace mijinki inma kina tunanin wai yana son matarshi fiye dake, ki dinga mishi abubuwan da kika san bata mishi......  Misali kaman wajan kwanciyan aure duk wani abu da kika san yana so ki dinga mishi karki ji kunya ki zama karuwa number daya sannan kisan yanda zaki dinga magana da miji kar kice waike ranki ya baci bari ki fada mishi komai ko kice bari in tura mishi txt din rashin mutunci karki kuskura namiji baya mantuwa koda kuwa kun shirya zai dinga kallanki da abun wata rana koda kun samu rashin fahimta sai kiji yana fadin ina jiran sakon cin mutunci dama Kin saba kinga mutuncin ki ya ragu, sannan keda kike da kishiya idan kika lura ranshi a bace yake kisan hanyar da za kibi danki faranta mishi rai May be itace ma ta bata mishi ran kinga idan kina sashi cikin farin ciki koda baya gidanki zaiyi ta Alla2 Ya dawo gareki sannan kullum kina cikin ranshi, sannan koda shine ya miki laifi bishi ki bashi hakuri shida kanshi zaiji kunya gobe zai rage abunda ya miki sannan karki Bari mijinki ya kwanta cikin fushi kice aishi ya sani babu ruwana yar uwa kinyi babban kuskure a duk sanda kikaga mijinki na fushi bishi ki rarrashe shi har kiga Ya sauko irin haka zaisa miji ya kara manne miki dan yana samun nutsuwa wajanki.... Ajiyan zuciya indo ta sauke tare da tashi ta shiga toilet tayi wanka zama tayi tasa wata night gown gaba daya jikinta ana gani ga wani irin rikitaccen kamshi da takeyi saida ta gama ta bude kofa zata fita saita tsinci kanta dajin Kunyan zuwa wajanshi komawa tayi ta zauna dan bataji zata iya, tashi ta karayi ta dauko hijab tasa sannan ta nufi dakin nashi budewa tayi a hankali kofar ta bude akan gadon dakin ta ganshi yayi rub da ciki, jikinta a sanyaye ta karasa inda yake a hankali tace in Kawo maka abinci?  Bai bata amsa ba sannan kuma bai dago ba, kara nanatawa tayi in Kawo maka abinci? Dagowa yayi idanshi yayi ja yace aysha mai yasa bakya sona? Aysha bani da abunda kike bugata gana mijin da kike burin aure ne? Mai yasa kika tsaneni haka? Aysha dan Allah ki fadamin miye bani dashi wanda bakya sona? Shuru yayi tare da kifa kanshi a kasa, jikinta taji ya mata sanyi ta kasa furta komai sai zuciyarta dake faman buga mata, a hankali yace aysha nine bakya so right? Plz kiban amsa yau inaso in kawo karshen komai koda kuwa Kin yanke hukuncin rabuwa dani ne, ni na yarda sonki ya kashe ni zan miki abunda kike so indai zaki farin Cik....... Karan kukanta ne yasa yayi shuru tare da kallonta ganin tana kuka sosai gashi baya son jin kukan nata domin jinshi yake har cikin zuciyarshi tashi yayi ya janyota jikinshi tare da rungumeta yana shafa mata baya cikin murya irin namai rada yace plz stop it bana son kukan ki, ki fadamin abunda kike bukata and I promise zanyi miki duk abunda kike So cikin daren nan, kukan ta kara saki mai karfi saketa yayi tare da dago mata kanta bakinshi yasa cikin nata ya fara kissing dinta sosai gaba daya jikinta yayi weak kafanta ya kasa riketa lokaci daya sukai kasa tare saida ya bari ta fada sosai kafin ya saketa dan dama yana bukatan nutsuwarta ne, a cikin kunnanta ya furta do you love me? Shuru tayi tana mai sauke ajiyan zuciya a cikin kunnenta ya kara furta tell me plz, ki fadamin miye bakyaso a tare dani, idanta na rufe ta kasa furta komai sai tunani takeyi harga Allah a yanzu dai bata jin zata iya cewa tana sonshi ko kuma tace bata sonshi ba dan zuciyarta gaba daya ta kasa gaya mata mai takeji akanshi, katse mata tunani yayi da fadin tel me plz, a hankali tace kana Da duk wani abu dana miji akeso a ganshi a tare Dashi duk abunda nake son in samu a wajan namiji kana dashi sai dai abu daya na rasa shine kai baka sona...... Bakinta ya rufe da hannunshi yace mai zan miki ki tabbar ina sonki?  A hankali tace kayi nesa dani  cikin wani irin murya yace ban gane ba, tace inaso kayi nesa dani na wani lokaci, yace ok tunda haka kikeso zanyi miki indai zaki farin ciki, saketa yayi ya tashi tare da bude wardrobe din dakin ya fara diban kayan da yake bukata yana sawa a karamin akwatin shi, tana kwance harya gama ya kalleta yace ga ATM dina tare da fada mata pin din yace duk abunda kike bukata ki dauka sannan inaso kiji tsoran Allah dan zaki cutar dani, yana fadin haka ya kama hanyar fita.









Taku Maryam obam😘

TAMBARIN TALAKADonde viven las historias. Descúbrelo ahora