*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA**🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
170to175
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*Har cikin babban falon gidan ta kaisu, nan masu aikin suka cika musu gaba da kayan ciye2, indo sama ta haura dan ta shaida ma mum sun shigo, bata karasa zuwa wajan dakin Mum dinba sai gata itada Dad sun fito, indo cikin jin kunya take gaida Dad, ya amsa tare da fadin sun shigo? Tace eh, nan suka koma tare, Yusuf yana ganin Dad ya tashi domin girmamawa Dad ya mika mai hannu suka gaisa sannan ya mika ma yazeed dake zaune yana kallonsu, Dad cikin sakin fuska yake fadin aysha koh ban tambaya ba wannan shine dan uwanki danga kama nan sai dai kin fishi fari, dariya duka sukayi sannan Dad yace ma yusuf ya zauna mana, bayan sun zauna yusuf ya fara yima Dad godiya akan rike mai yar uwa da sukayi, Dad yace haba2 ya isa haka ai babu zancen godiya tsakanin mu, sai dai fatan daurewan zumunci muke fata ya kasance na har abada, Mum tace hakane domin a gaskiya ban san rabuwa Da Aysha dan tana da hankali da nutsuwa, yusuf yaji dadin yaban da sukema kanwar tashi yanda ya fahimci su Mum mutanan arziki ne, nan Dad yace musu bismillah naga baku ci komai ba, Yusuf ya dauki drink Ya zuba a cup tare Da zubama yazeed shima, nan Dad yaita jan yusuf da fira Mum tace ya mai jego gobe suna koh?dad yace waye ya haiyu nan Mum tace matar yusuf Dad shima barka yamai, Dad saida yaga yusuf ya kammala sannan yayi gyaran Murya, a dai2 lokacin wayan yazeed yayi ringing ya dauka tare Da fita daka falon, Dad yace ina mai bada hakuri akan abubuwan daya faru a baya na rabuwan auren aysha da mijinta, wanda rashin fahimta ne yaja hakan, amma yanzu sun fahimci juna ina mai rokan a barta ta koma dakinta, yusuf dan shuru yayi tare da kallon indo wacce take ta kasa Da kanta ganin irin kallon da yake mata yasa tabar wajan da sauri, murmushi yayi wanda a dai2 lokacin yazeed ya dawo inda yusuf yake fadin cewa babu komai tunda sun yanke zata koma gidan mijinta Allah yasa hakan shine alkhairi ya basu zaman lafiya, nan mum ta amsa da Ameen, yazeed dai bai fahimci abunda ake nufi ba saida Dad yace banso a dauki abun da tsawo danshi yana London inda So samu nema a daura auren sai tabi mijinta yusuf yace duk yanda kuka tsara koh kuma ince yanda aysha din suka tsara gaban yazeed ne ya fadi tare da shiga cikin wani irin hali, bai kara tsinkewa bama saida yaji Mum tace aida an bari ya dawo sai ayi bikin koh? Dad yace a'a baza'ayi haka ba, nan Dad ya zaro kudi cikin aljihu yace mlm yusuf ga sadakin aysha nan,yusuf yace dady inaga da an bari dan abbana zan wakilta akai yace toh shikenan kayi tunani mai kyau Allah yayi albarka yusuf ya amsa da Ameen, yazeed gaba daya ya shiga damuwa mai yasa aysha ta amsa min bayan ta daidaita da mijinta? Wani iri yaji yana ji dan haka ya tashi yace ma yusuf inka fito ina mota, sannan yama su Mum sallama ya fice,dad yace zaizo wajan abban Yusuf din, shima yusuf din bai wani dadeba ya fito inda Mum ta kira aysha dan suyi sallama, a waje ta gansu yazeed Na cikin mota shiko yusuf na waje bayan ta fito Yusuf yace amarya bakya laifi, dan rufe fuska tayi tare Da fadin kai bros, dariya yayi tare da fadin dama naso muje taraba So yanzu sai mu bari bayan bikin ki koh gwara kije kina da aure nima ga ciwon abba bana son yin nesa dashi, tace toh yaya yusuf duk yanda kace hakan za'ayi, ya jikin abba din? Yace da sauki Alhmdlh tunda ya fara shan Magani yace ya rage jin zafin jikin, tace Alhmdlh bari ya gama sha muga yanayin jikin sai ku dinga Kawo shi gashin kafa duk sati din, Yusuf yace insha Allah, yazeed dake mota gaba daya ji yayi kaman yasa ihu dan takaici, sallama sukayi da dan uwan nata sannan ta leka cikin motar tace yaya yazeed sai anjima kai kawai ya daga mata, sannan yusuf ya shiga yaja suka wuce, ta shiga Gida jiki a sanyaye su Mum na falo ita da dad, Mum tace aysha ko kina da wani abun da zakiyi na bikin naku? Tace a'a Mum duk yanda kuka yanke nima yamin, Mum taji dadi sosai indo dakinta ta wuce Tana tunani kala2 wayanta ne yayi kara alaman shigowan message, budewa tayi ganin yazeed ne ta fara karantawa *haba aysha mai yasa kikamin haka? Ko kin san yanda naji a lokacin da ake maganan za kiyi aure a gabana bayan kin amince min, dama zaki iya yaudara na aysha namiji bashi da tabbas duk da ban san maiya hadaki Dashi ba har kuka rabu tun farko ba, komawa gidan nasa bakya tunanin zaiyi miki abunda ya faru baya, aysha mijinki da zaki aura bawai sonki yake ba inda yana sonki da tun farko bai rabu dake ba kiyi tunani akai karki lalata rayuwanki a banza* wani hawaye taji yana zubar mata akan fuska lallai maganan yaya yazeed gskya ne A Majeed bawai yana sonta bane tunda a baya ya gujeta bana tunanin yanzu zai soni sai dan wani manufa nashi, lokacin da nake indo na ya nuna yana jin kyamana tare da gudu Na saida yaga na zama wani abu zai nuna min So, anya banyi babban kuskure ba na komawa gidan nasa ba, kuka ta Saki mai sauti tunawa da tayi da sulaiman mai sonta tsakani da Allah tun bata wayewa yake sonta lallai Sulaiman kaine masoyina na gskiya duk da kaima ka juya min baya, amma har gobe ina jinka cikin raina, kiran yazeed dinne ya shigo waynta kashe wayan tayi gaba daya dan bata son damuwa dan shima Tana ganin bawai yana sonta bane inda Ya ganta a yanda take da tasan koh kallonta bazai yiba, kwanciya tayi tare dajin haushin yazeed din Da A Majeed wanda tafi tsana a yanzu, zazzabi ne ya rufeta ta kudun dune a bargo, Mum jinta shuru yasa ta shiga dakin taga halinda take ciki cikin tashin hankali take tambaynta lafiya kuwa ,indo tace Mum zazzabi nakeyi cikin rawan sanyi Mum tce bari muje hspt indo tace a'a zata sha paracetamol kawai Mum dauko mata tayi ta taimaka mata tasha, sannan ta koma ta kwanta, Mum ranan taita zirga zuwa dakin dan taga jikin indo din, babu laifi zazzabin ya saketa sai dai damuwa dake damunta domin tunda taga sakon yazeed taji bata san auren da zatayi duk da dama ta amsa ne badan tana so ba, anya bazan fadama Mum na fasa ba? Wata zuciyar tace karki kuskura ma ki kara wannan tunanin, ranan dai a daki ta wuni washe Gari dakyar ta shirya suka tafi sunan yayanta ita da mum, inda aka amshesu cikin mutunci Mum tayi ma baby siyayya da yawa,haka akaci suna yaron yaci sunan abban zaliha suna kiranshi Da irfan, indo jiki a Mace domin tunani taitayi Mum duk Tana lura da ita, amma ta bari sai sun koma Gida zata mata Magna indai auren ne bata so sai a fasa, koda suka dawo Gida mum ta sameta a daki ta zabga tagumi tace aysha bataji ba har saida ta tabata, tayi firgit, Mum tace aysha anya lafiya kuwa tun jiya da akayi maganan aurenki kika shiga wani hali dan Allah aysha idan bakya son wannan auren ki fadamin karkiji komai ko nauyi Na wlh bazanga laifinki ba duk hukuncin da kika yanke, aysha hawaye ne ya zubo mata tace Mum bazan taba kin jininki ba, koda kuwa ya yake mum kinmin abunda bazan taba mantawa Dashi ba a rayuwa bani da abunda zan saka miki Dashi Mum sai addua Mum tace ya isa haka,tare da rungume indo Tana sa mata albarka.
Yau alhamis kuma a ranan dady ya hadu da abban yusuf ashe sun ma san juna nan suka tattauna bayan saduwa inda dady yake tambayan abba maiya sameshi, abba yayi ajiyan zuciya tare Da fadin wlh jarabawa ne ya sameni na tura wajan rabi Da kwata na kudina a kawo min kaya har an shigo Da kayan costume suka rike wai an sami hodar iblis a ciki gashi driver din ya gudu, nida aka Kawo min motoci maiya hadani da wata hodar iblis, nan dady ya jajanta mishi tare Da fadin zaiyi wani abu a kai insha Allah, sannan Suka fata tattauna akan maganan daya Kawo su inda abokin dady Da sukaje tare ya bada sadaki abba yace gobe juma'a sai a daura auren, hakan koh akayi, Dad bayan ya koma Gida yake tambayan Mum sunyi waya Da A Majeed kuwa yakira? Tace wlh bai kira ba gashi babu number dinshi tacan Dad dan shuru yayi tare Da fadin gobe za'a daura auren nasu, Mum tace haba aida an bari an shirya, Dad yace No gwara a daura dan harna turama mutane Da txt kawai kiyi addu'a kawai Mum tace Allah ya sanya alkhairi yasa ayi a sa'a, Dad ya amsa Da ameen.
LONDON
A majeed bayan ya sauka direct asibiti ya wuce gado suka bashi ana kula Dashi, kwananshi uku ya dawo gidan da zai sauka tare Da Magani Da aka bashi, kwata2 baya son kiran koda iyayenshi dan So yake ya manta komai amma abun yaci tura dan kullum aysha Tana ranshi ganin kaman a nan din yafi tunanin nata yasa ya fara tunanin dawowa Gida, duk da yayi alkawarin yin nesa Da ita amma yaji bazai iya ba yadai yanke gobe zai dawo Gida ko zaiga ayshan shi yaji dadi.
Yau juma'a bayan an idar Da sallah juma'a aka daura auren A Majeed Da Aysha a central mosque dake abuja, daurin auren Da mutane da dama suka shaida ciki harda president dan shima Dad ya mishi bayani kuma ya hallara sai dai addu'a zaman lafiya.
Hmmmm muje zuwa
Taku Maryam obam😘

ESTÁS LEYENDO
TAMBARIN TALAKA
Historia Cortalabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.