*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA**🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}**Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
175to180
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*Duk wannan abunda akeyi indo bata sani ba, balle shi A majeed din,bayan Dad ya dawo Gida yasa Mum ta kira mishi indo din, bayan tazo ta gaida mum ta zauna tare da dan takurewa Mum tausayinta take dan Tana ganin kaman bata san auren ta daiyi ne kawai danta faranta musu, duk ta rame, Dad ne ya katse Mum daka tunanin data fada yace aysha yau aka daura aurenki keda abdulmajeed, Dam taji gabanta ya fadi dan batayi zaton za'ayi auren a wannan lokacin ba, toh amma mai yasa aka Mata haka? Hawaye taji yana son zubo mata tayi saurin goge idon dan karya zubo, wayan Dad ne yayi kara ya dauka tare da fadin shigo mana yusuf, bayan Yusuf ya shigo ya gaida Mum itama indo gaidashi tayi ya amsa ,bayan ya zauna ya dauko kudi tare da fadin Aysha ga sadakin ki nan tashi yayi ya mika mata, tace a'a yaya yusuf ka barshi a wajanka, yace a'a wannan ba Hakki na bane naki ne, amsa tayi tare da zubar da hawayen da take makalewa, yusuf murmushi yayi tare da yima su Dad sallama, Dad yace a'a ya tsaya suci abinci, yace Alhmdlh yana So yaje yaga abbanshi ne, sallama yayi musu ya fita, indo tashi tayi tabi bayanshi itama, har wajan motarshi, tsayawa sukayi a gefe, ya kalleta fuskan duk ta cabe da hawaye, sunanta ya kira da fadin aysha kin san zaman aure hakuri ne, basai na fada miki miye hakuri ba ke zaki fadama wani ma miye hakuri idan kin tuna rayuwanki a baya, So inaso ki kara akan nada, dan Allah sis karki bani kunya mutanan Da alkhairi suke sanki ki duba yanda suka rikeki kaman yarsu ta cikin su, dan Allah a wannan karan kema ki nuna yar halak ce ta hanyar Hakuri da kawar da zuciya nesa, sannan nasa ayi oder din kayan dakinki duk da dady yace a barshi amma nafi son a kawo miki yace yasa komai a gidan dan wani saban gidanshi ne daya gina zaki zauna keda mijin naki, kayan idan an Kawo za'a ajiye miki a wani waje, Allah ya bada zaman lafiya, kuka yaci karfinta ta kasa magana ganin tana son karyan mai da zuciya yasa ya shige mota ya wuce yana tausaya mata, saida ta goge fuskanta sannan ta shiga Gida, a falo ta tarar da mum, har zata wuce Mum ta kira sunanta ta amsa Mum tace kizo kici abinci, kaman zata ce ta koshi komai ta tuna kuma ta nufi dinning ta zuba abinci kadan taci, baifi 3spoon taci ba ta tashi ta wuce dakinta Mum duk tana kllonta amma bata ce mata komai ba, koda ta shiga daki babu abunda take sai kuka domin tana ganin kaman da wani manufa Ya aureta lallai hakan nema maganan da yazeed ya fada mata, dafarko ya nuna baya sonta yanzu kuma mai zaiyi da ita, shida yake da kaman Zainab a Gida mai zaiyi da ita, haka taita tunani tana kuka.
Karfe biyar dai2 jirgin su A Majeed ya sauka a airport, mutane suka fara fita ciki harda A Majeed kallo daya zaka masa kasan ya rame ya kara haske da kyau, kaman balaraban kasar dubai, direct wajan motarshi ya nufa dan yama driver magana akan yazo Ya daukeshi, baya ya zauna security din dady na gaba, kai tsaye gidansa yace a wuce dashi, bayan sun karasa ya shiga cikin falon duk yayi kura, dan tsaki yayi dan baya son kazanta ko kadan, fita yayi ya shiga mota yace a kaishi gidan Mum din nashi, kai tsaye gidan suka nufa, wayanshi dake kashe a hannunshi ya kunna message suka fara shigowa har zai share sai yaga na Abdul dan haka ya bude, *man ya zaka tafi baka kirani ba har yanzu kasan bani da number dinka na can, To congratulation aysha an daura muku aure yau* da sauri ya kara karanta message din yana mamaki dan yasan basa irin wannan wasan da abdul, fita yayi daka motar tare da doka ma Abdul kira inda yaji line busy, tsaki yayi tare da kara duba message din da aka turomai duk na congratulations ne akan auren nashi, da sauri ya shige cikin gidan nasu dan yasan duk amsan da yake nema zai samu a ciki, babu kowa a falon dan haka ya haura sama direct dakin Mum ya nufa, mum na zaune akan gado tana waya, taga mutum ya shigo Da sauri ta kashe wayan tare da tashi tana fadin son, sai kuma tayi shuru tana dariya da sauri ta nufeshi tayi hugging dan nata tana fadin mai yasa baka kiramu ba son? Dan sakinshi tayi tana kare mai kallo tace son ka warke kuwa? Dan murmushi yayi tare da fadin da sauki Mum, ina Dad? Tace yana dakinsa muje hannunshi rike da nata suka nufi dakin mahaifin nashi, inda suka sameshi yana danna system, shima ganin dan nashi yasa ya tashi yana yar dariya irin ta murna, yace son ya jikin naka? Yace Dad bana tunanin zan warke har sai abunda naji ya tabbata, Dad Da Mum suka Kalli juna lokaci daya kuma suka kalli dan nasu, Mum tace mai kaji, babu kunya ko tsoro yace Mum aysha wai da gaske an daura...... Shuru kuma yayi tare da sosa kai, Mum ta sakar mai harara Dad yayi gyaran murya tare da fadin zauna son, gabanshi yaji ya fadi bayan ya zauna Dad yace son hakane yau aka mayar Da aurenku kaida aysha, wani irin ajiyan zuciya yayi har iyayen nashi naji, Dad yaci gaba Da fadin son inaso kaji tsoran Allah kayi adalci a tsakanin matanka, ka daiga abunda ya faru baya, da irin abubuwan da suka faru yanzu, aure ba abun wasa bane..... Dad dai yayi mishi nasiha sosai mai ratsa jiki, inda Mum ta amshe tare da fadin ka dai san bazan yarda a wulakanta min yaba koh, wlh idan naji wani abu saina saba maka, itama ta daura da nata nasihan, inda Dad ya bashi keys din gidan da zasu zauna, ya amsa yayi godiya mum tace tarewa kuma sai nan Da sati biyu, wani iri yaji danshi harga Allah yanzu yaso a bashi matarshi, anya zan iya jira har sati biyu kuwa, Dad ne ya katse shi da fadin naji ance kana gina asibiti? Kai ya dan sosa tare da fadin eh Dad na aysha ne bana So tana aiki a karkashin wani, Dad yayi dariya irin tasu ta manya yace hakane hakan yana dakyau, tashi yayi dan yaje ya huta Mum tace Gida Zaka tafi? Yace No Mum ina nan zanje in huta ne, tace badai a gida naba koh? Yace Mum can gidan yayi kura kin san babu kowa a ciki, Mum tace matar taka har yanzu bata dawo ba? Kai ya daga alaman eh dan baya so ayi mishi maganan Zainab din dan yana ciki da ita sosai tunda ta kirashi sau daya bata kara kiranshi bah, shima haka bai nemeta ba, fita yayi daka dakin Mum ta girgiza kai tare da fadin Allah dai ya kyauta Dad yace da akayi me? Tace ina mamakin irin wannan auren Na abdulmajeed, na rasa wani irin So yake ma Zainab da baya ganin laifinta baya iya kwaba mata idan tayi ba dai2 ba, Dad yayi murmushi tare da fadin ki kawar da idanki a kansu ki masa addu'a kawai, Mum tace toh Allah yasa mu dace, Dad yace ameen.
Koda A Majeed ya shiga daki murna yaitayi wai yau shida aysha suna matsayin mata Da miji, ikon Allah, wayanshi ya dauka ya kara kiran Abdul ringing daya ya dauka, abdul yace angon aysha yaushe ka dawo? A Majeed yace yau wlh Kana ina? Abduk yace ina gidana, A Majeed yace ya kamata kazo kasa ta fito in ganta, Abdul dariya yayi sosai tare da fadin kaida matarka, A Majeed yace plz ka bari ni nasan halin kayana sai an lallaba, nasan har yanzu bata sauko ba wai ya abun ya kasance ne ma wlh mamaki nakeyi, nan Abdul ya bashi labari, A Majeed wani irin nishadi yake ji tare da fadin Abdul wlh tunda naji an daura mana aure da aysha naji kirjina ya warke kaman an cire min wani dutse, Abdul dariya yayi sosai tare da fadin kace yau akwai cin amarci, dan tsaki A Majeed yayi tare da fadin Mum tace sai nan da sati biyu zata tare,ni yanzu kawai kazo ka daukeni muje inga gidan da Dad yaban in babu wani abu in kara dan yace yasa komai, abdul yace ok gani nan zuwa, yana kashe wayan aka kirashi da No din waje ko bai tambaya ba yasan ko wacece kaman bazai dauka ba ya dauka tare dasa wayan a speaker tace A Majeed wai labarin da naji gaskiya ne? Yace name? Tace dagaske wai ka Kara aure? Yace hakane Zainab amma inaso ki sani aure....... Ta katse shi da fadin wannan karan kayi babban kuskure wlh I will teach you a lesson da koda nan gaba akace maka ga Mace tsirara ba zaka kalla ba balle kayi tunanin aurenta, duk da nasan mamanka ce ta shirya wannan makircin itama........ Daka mata tsawa yayi tare da fadin keee Zainab u have to be very careful akan kalamanki akan mum dina, cikin fushi tace toh karya nayi ai itace ta shirya komai koda yake bani da tym din magana dakai gobe zan dawo dan haka ka shirya domin zan baka babban kyauta kaida amarya tana fadin haka ta kashe wayan..
Taku Maryam obam😘

YOU ARE READING
TAMBARIN TALAKA
Short Storylabari ne akan wata yarinya marainiya da tasha wahalan rayuwa da yanda dan uwanka zaiki yaron dan uwansa sai nasa.