page 4

5.1K 402 3
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨



💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
*((QUEEN BK))*



🚩ZAMAN AMANA WRITTER'S ((Z.A.W)) ASSOCIATION (( Gidan zaman lafiya da amana insha Allah))



Page0⃣4⃣

Karfe biyu dai dai aka tashe su,
a hanyar su ta dawowa suka biya gidan su lamunde kamar yadda suka saba, kullum suka tashi
islamiyya za su biya su ansa maganin da inna lamunde ke basu, su a cewar su magani ne tunda
tun suna k'anana take basu, wani in sun sha suji zak'i wani kuma suji d'aci ko bauri, hakan ne ma yasa suke cewa magani ne,

innar lamunde mutum ce mai dattako da sanin ya kamata kuma cikakkiyar mace, ya kasance mamarta ta na bayar da maganin gargajiya duk fad'in rugar tasu da kewaye tayi suna, don haka tun tana k'arama mamarta ke tsumata kasancewar taji dad'in abun, yasa itama take tsuma d'iyar ta sae ta ke basu tare da ma'u tun suna k'anana,
don jininsu ya hadu sosai dana ma'u, shiyasa ma take taemakonta sosai tunda tasan halin hanne (gwggo),
wata sa'in tana kiranta taci abinci a gidansu duk da suma ba wani haline da su ba,

suna isa gidansu lamunde suka gaishe da inna, bayan d'an barkwanci tsakanin ma'u  da inna kamar yadda suka saba ta basu tsumin suka sha, sannan ta zuba masu alalan da tayi suka ci.

Ma'u tunda ta iso gida taga taguwar baffah a zaure da murna ta k'arasa ciki,
yana ganinta ya washe baki
itama baki a yak'e ta k'arasa inda yake zaune, ta zauna kusa da k'afafunshi
cikin harshen fullanci ta gaeda shi,
Ya amsa tare da tambayarta ya makaranta
tace,
"lafiya lau baffah, yau ma aka maeda mu babban aji"

Yace " masha Allahu, ajin y'an sauka kenan ko"

Ta gyada kai

Yacigaba, " to yanxu saura izu nawa kenan ki had'a"

ta amsa da, "sauran mu biyar baffah"

Yace, " Alhmdullilah batun muraji'a dana baki kafin in tafi fa"

Tace " na gama"

yace "Duka rubhi'i biyar din?"

tak'ara amsawa da "ay"
yace
" to sae da daddare zan karb'a, tashi kije kicire kayan naki kixo ki ci abinci, ki huta dan yau tare xamuje kiwo".

Tana murna ta nufi daki don tana san zuwa kiwo da baffah don xusuyi wasa da dariya, ya mata busa ya bata labarai masu dad'i, da labarin birni wanda yafi k'ayatar da ita, dan sunfi sakewa a gun kiwo ma akan gida.

Da wannan murnar ta tafi cire kayan makarantarta, ita ko gwggo dake gefe tana tankad'e sae yatsina take, tana watso masu harara k'asa2.
ba ta k'ara tsinkewa ba ma,
sae da taji baffa na kiran ma'u, wai tazo ta karb'a, kuma taga ya dauko d'aya daga cikin ledojin da ya shigo dasu, wanda tunda ya shigo ya aje su bai waiwayesu ba, ita dama Alla2 take ya fita masalacci ta bud'e taga meye aciki dan bae saba dawowa da leda ba.

Ma'u ta iso wajen baffa, ya mik'o mata leda yace " karb'i wannan naki ne, na gansu ne ana siyarwa nace bari na siyo maki dan na lura kayan ki duk sun d'age maki"

ma'u tace " ayyah baffah na ko gode sosai"

gwggo ko sae xunguro k'eya take ta na so taga meye acikin ledar,
Ma'u kamar ta san abun da ke ran gwggo ta b'ude ledar
kayan fulanine masu kyau na bak'in sak'i set 1,
da sark'arsu da abun hannu dana kai,
ma'u har da tsallen ta, tana ma baffa godiya.

yace, " in ban maki ba wazan mawa ma'u"
sanan ya mik'o ma gwoggo d'ayar leda biredi ne sink'i biyu, duk da tana san biredi sosai hakan sae taji kyautar batayi mata dadi ba dan haka a wulak'ance ta ajiye ledar gefe guda.
Shiko
baffah ko ta kanta bae biba ya nufi masallaci dan dama yasan ba godiya zata mae ba kuma dama baya jiran godiyarta,
itako ma'u har taje daki ta gwada sae tsalle take da murna ganin ya mata kyau, dama tana son bak'in sak'i kuma gashi yanxu ta samu don haka take ta gode ma Allah,

Washe gari su ma'u, tun kan su isa wajen xaman su, suka hango jauro na jira, lamunde ta zunguro ma'u
tana mata alama da ido, ma'u
tace na ganshi kyale shi kawai, suna k'arasawa suka karkade wajen xaman su,
suka zauna tare da kwance kwarerayinsu,
shiko jauro bae damu da halin ko in kulan da ma'u tae mashi ba, dan yasa ya tok'olota ne, dan haka yayi gyaran murya ya matsa
kusa da lamunde yace

"ah'ah lamunde ya naganki ke daya yau ba k'awar taki fatan dae lafiya"

lamunde ta karb'e da cewa

"wace k'awar kuma banda ma'u?"

yace, "itakuwa nake tambaya"

Ma'u ko ta k'ara had'e rae tare da kawar da kai gefe tacigaba da damun furar da takema wani da yaxo siya,

Lamunde tace " duk fad'in rugar mu akwai wata ma'u ce banda wannan?"

ta fad'a tare da tab'o mau'n

Yace " ay to, naga wannan suna kama da mau'nah saedae ni ma'unah kullum fuskarta a sake take, tana cikin dariya a koda yaushe sae dae kash naga d'aurewar ma ta fi mata kyau amman dae in tayi dariya
tafi kyau"

ma'u ta d'an saci kallonshi shi kuma ya sakar mata wani lallausan murmushi
dae2 lokacin yace haba ma'un jauro, tanasan sunan
don haka bata san sadda
ta saki wani k'ayataccen murmushiba,
wanda har dimple dinta sae da ya lotsa shiko ganin haka ya bashi damar
fada mata uxurin da yasa bai
zoba, danda nan suka manta
da zancen suka koma hira,
labari ya ke basu ita da lamunde
sukuma suna ta kyal kyala dariya,
a haka dae har ya shafura sannan ya wuce aikin shi.

Da daddare wajen k'arfe takwas ma'u ce ke ta cab'a adonta
tana shirin zuwa dandali,
tagama kintsawa tsab
lamunde
kawai take jira ta biyo mata
dan baffah baya bari ta tafi
ita d'aya, kuma tara nayi zata
dawo gida acewar shi ba xa'a hana yaro wasa ba amman
in yawuce tara ai yayi dare
da yawa, shi dan an ma saba
sun taso tun iyaye da kakanni
haka suke fita wannan dandali
ai da ya soke shi, dan shi baya
cika san wannan wasan daren
ba to bai so ne ya tauye ma
ma'u wani farin cikin ne, dan ya san tana son zuwa dandali,
to gudun kar ya ci amana
Shiyasa yake barinta tunda yasan ba wae tana samun gatan da ya kamata bane.

Sae kai komo take tana son taji sallamar lamunde,
kamar ko had'in baki tajiyo muryar k'awar ta ta, ta kwad'a sallama tare da fadin ma'u taho mu tae
wasa dama haka ta keyi bata shigowa saboda gwggo, ai tun kafin lamunde tagama sallama ma'u ta zari takalminta ta kwasa a guje
dama baffah na waje shida abokinsa, suna tattaunawa,
Nan suka gaishe su tare da yi masu sallama sannan suka d'au hanya,
suna
tafe suna hira ma'u ta b'ige
da kallan sama ga yadda gari yayi shiru, yara duk antafi
dandali, gawata ni'imantacciyar iska da take kad'awa ga wani sanyi2
Ni'imar Allah dake busa su,
ma'u ta maida duban ta ga
lamunde dake ta gartsar gorubarta,
tace

"gaskiya Allah yayi ma dare ni'imomi da yawa jiba kiga yadda yanayin
shi yake, wlh ji nake kamar in kwanta in ta kallon taurarin da watan nan da Allah ya k'awata sama
dasu, in ta kallonsu har in gushe a haka,
hak'ik'a Allah mai girmane, lamunde ko da ba wani abun da taji sosai
hakalinta nacan kan gorubarta, kawai ta amsa mata da
" maganar ki dutse ma'u, ke dai kina san yanayin dare ya miki"

ma'u tace "sosaima!"

Ta cigaba da jujjuyawa a hankali iska na shi ganta ta ko ina, tana kallan sama tana santin ni'imar Allah.




A/N

Helloh beautiful readers!

Hope you guys got a rough idea about the characters?

if you like the page do vote and comment!



*QUEENBK*

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now