page 17

3.8K 285 1
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎 *ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S📝(( Z.A.W))*
[ ~Gidan   zaman   lafiya   da   amana   insha   Allah~ 🤜 🤛 ]





Inayinki har birnin zuciyata, kece tawan banda makushinki, har abada ina sonki ubangiji Alllah ya had'amu har a gidan aljannar sa, kece dai *ZAINAB MUJITTABA WAISU,* wannan page d'in naki ne ked'ai ki wataya *QUEENBK* nayinki irin totaly😍❤💋








Page1⃣7⃣






Inason mu zauna dake cikin
mutunci da amana kamar
yadda muke zama da duk
wani da ya rab'e mu cikin lumana,
duk daga ganinki naga kina
da hankali da natsuwa inason
hakan ya zamo sai dai ki k'ara ba dai ki rage ba, sannan abubuwan da banaso
shine k'arya da k'azanta don
haka ki kiyaye, ki d'auke ni kamar
uwa ni kuma zan zame maki
d'aya, kar kiji shakun fad'amun
komai dake damun ki kinji,
ma'u tace " insha Allah zan kiyaye duk abun da ki ka gaya mun, kuma za ki sameni mai biyayya da yaddar Allah"

"yauwa haka nake son ji y'ar d'iya ta, yanxu tashi muje na nuna maki inda zakina kwana, alabashi daga baya zan gaya maki yadda zaki rink'a ma yayansu aikin"

Ma'u ta amsa da to, ta tashi ta bita tana jin d'ad'in
yanayin matar, bata da wani b'oye2.

Haj, amina ta tsinci kanta cikin
son yarinyar matuk'a, farat
d'aya daga ganinta taji ta kwanta
mata a rai, har tana mamakin
kallar son da taji tana matan,
(niko nace SO HALITTA NE, amman muje zuwa muji ko da akwai wata a k'asa)

Wani d'aki suka shiga d'an madaidaici mai kyau komai na d'akin pink ne, haj. ta juyo ta kalli ma'u tace " Nan d'akin auta tace ki zauna a nan dan nasan zatayi farinciki da hakan"

Ma'u ta k'araso ta aje kayanta tana k'are ma d'akin kallo tare da jero mata godiya, duk ta k'agara taga autannan da zatai farincikin zaman ta a d'akinta.
kuma abunda ta lura dashi
hajiyar bata da k'yamar talaka ko kad'an, bayan ta aje kayanta, haj, tace biyo
ni, wata k'ofa dake cikin d'akin ta bud'e toilet ne shima
komai na ciki pink ne, tace

" kin ga nan zakina wanka kuma ban san k'azanta, kamar yadda na fad'an maki, ki rink'a zabace kayan ki da jikin ki in kina so mushirya"

Ta nunnuna mata yadda ake
amfani da abubuwan toilet d'in kaf, sannan tace ma'u tayi ta gani, kamar yadda ta nuna mata haka ma'u tayi tsaf wanda hakan ya birge hajiya.

Suka koma cikin d'akin ta bata
wani sabon towel ta ce ta tub'e
ta d'aura shi, nan taga gashin
ta mai kyau da tsayi, gashi virgin hair, sai dae
baya samun kulawa dan wani
zane ne kan ma'u wanda daga
gani ya d'ad'e dan tsagar ma
ta shige ba'a ganinta gashi yasha uwar datti, ta d'auki
sabon brush ta matsa mata
macline ta gwada mata yadda
akeyi sannan tace in ta gama
tayi wanka ta kwance kanta
shima ta wanke shi tas tunda
duk ta nuna mata su shampoo
da liquid soup da dai sauransu
yadda ake amfani da su, sai
da ma'u ta fara sannan haj, ta tafi.

ma'u da tazo wanka shower
ta bud'e amman gannin bata
saba ba yasa ta kashe ta tara
ruwa ta cud'e jikinta da sabon soso da sabulun da
aka bata mai d'adad'an k'amshi,
bayan tagama fitowar ta yayi
dai2 da shigowar ammie,
ta k'araso ta duba kanta, sai
cewa tai "asma'u kanki bai fita ba
duk ga datti nan muje na kuma wanke maki" suka koma
haka ammie tai ta wankar kan ma'u amman datti be dena biyowa ba, da ta gaji sai tace bari su bar
shi haka in miemie zata je
saloon suna zuwa tare haka
har datti zai fita a hankali,
suka fita bayan ta d'auraye mata kanta da jikin nata,
wani k'aramin towel tasa ta tsane mata kan nata,
sannan tasa hand dryer ta busar mata da gashin ma'u ko har da y'ar k'wallanta wai zafi, tasa
ribon ta tufke mata shi tayi mata doughnut duk da haka sai data k'ara nannad'a mata gashin saboda tsawon sa, ba laifi gashin ya gyaru sosai
sai k'yallin mai da yake, bayan ma'u ta shafa mai,
tazo maida kayan da ta cire, ammie tace

" a'a asma'u d'auko wasu"

ganin da tayi kayan nata duk
tsummokarai ne gwanda ma
wanda ta sako d'in, yasa tace
to ta maida waennan kawai
kafin anjima ta nemo mata
kaya cikin na miemie kan a d'inka mata wasu sannan ta fita.

Bayan ma'u tagama sa kayan,
ta fito da k'yar ta kai kanta
kicin d'in, ta iske uwar talle
na ta aikinta, dan haka ta
kama mata da wanke2, ta wanke
su tas sannan ta tsane ruwan
da ta zudda ta goge sink d'in,
ba ammie kad'ai ba har uwar
talle tayi mamakin aikin nata
gashi tsab2 kuma cikin natsuwa,
Ammie tace " asmau kinyi k'ok'ari sosai, dama kin tab'a aiki ne a wani gida"

" a'a ammie ban tab'a ba aman na saba a gida kuma aunty nafy ta kuma koya mun"

" to madalla yayi kyau Asma'u zo muje"
Suka fito farfajiyar gidan bagaren gaban gidan nan suka shiga, ammie ta shiga da sallama, Alhaji Muhammad zayan na zaune akan wata kujera wadda bata d'aya daga cikin set d'in na falon, irin na hutun nan ne da za'a iya linke su ayi yawo da su ko ina, yana shan juice yana kallon t.v da remote a hanun shi, jin sallamar uwar gidan shi yasa shi murmushi tare da maida duban shi gare ta, sai da suka gaisa kamar yadda suka saba ta zauna kan kujera kusa dashi, sannan ta kira ma'u tace ta shigo mana, ta k'araso da sallamar ta, ta samu waje k'asa nesa da su ta rakub'e, ta gaishe dashi cikin girmamawa, ya amsa sannan ya maida duban shi ga ammie, itako tagane kallar kallon da yake mata wato yana sonjin k'arin bayani don haka ta koro mashi batu kamar yadda yake, yace

"to madallah ai abu yayi kyau, anma kina tunanin zata iya? dan naga k'arama ce"

ammie ta amsa da " ai abbansu indai wannan ce ba wata matsala insha Allah a yadda naga yanayin nata"

" to ai haka akeson ji, ai yanzu ma yayan nasu ya fita"

" to yazo ya kawo gaisuwa kenan ni yau ma be ma shigo mun gaisan ba" cewar ammie

"a'a ammiensu kar kice haka yanzu fa fitar shi kuka shigo, kun dai sha bambam"
ya k'ara maida duban shi ga ma'u sannan yace " amman amiensu wannan y'ar garin kuce ko?, naga tana kama da danginku shuwa"

" nima haka na gani wlh, ni da NANAn mu ma take mun kama"

" wlh ba shakka maganarki dutse"

Ammie tace "amman tace daga rugar nagge take"
 
Ita dai ma'u shiru tai ta sadda kanta tana ta wasa da y'an yatsunta,

Daganan suka canza ak'alar hirar tasu, daga bisani kuma suka fito suka shiga d'ayan bangaren me kama da na ammie, haj. shafa'atu cikin fara'a ta tare su, ta gaishe da ammie ta amsa da " lafiya k'alau auntyn yara, ya kwanan yaran"
ta amsa da "lafiya k'alau duk an tafi nakaranta"

Nan ma ammie ta gabatar mata da ma'u sannan suka fita, daga nesa ta nuna mata bangaren k'arshe tace " wancan ne b'angaren yayan nasu"  ma'u bata gaza fahimtar ZAMAN LAFIYA DA AMANAn dake wanzuwa a gidan ba, sai dai abu d'aya da ta sama alamar tambaya shine kallon da aunty (haj.Shafa) ta rink'a binta dashi lokacin da aka ce ita ce mai ma yaya abdallah aiki kuma ta rasa gane dalili.

suka koma part d'in ammie suka tarar uwar talle na ta cuccura sakwarar da ta daka a leda, da sauri ma'u ta wanke hannunta ta kama mata, bayan sun gama suka had'a miyar agushi da taji naman kaza zak'ok'o sai kunnun ayan da sukai, itako ma'u taimaka mata kawai take   tana kuma kokkoya dan bata tab'a ganin girki kallar wannan ba, bayan sun gama uwar talle ta d'an nunnu namata abubuwa da yawa da yadda ake serving yaya abinci, daga nan aka bata basket d'in da aka jera komai da aka dafa a ciki akace ta kaima shi part d'insa,


Makaranta kuyi hak'uri jina shiru kwana biyu mun d'anyi sha'ani ne, kuma na muku typing jiya amman ya goge har sau biyu😭,  muje zuwa QUEENBK nayinku ina matuk'ar jin d'ad'in comments d'inku suna k'ara mun k'arfin gwiwa, da kuma kulawa da kuke bani ku ci gaba kuna sani farin ciki 😍😘

A HARDENED HEART WON'T PROTECT YOU FROM HEARTBREAK, IT'LL PROTECT YOU FROM LIVING.


👸🏼QUEEN BK👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now