page 46

5K 246 16
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )

















Page4⃣6⃣







*KI SADA ZUMUNCI DOMIN YANA ƘARA NISAN KWANA KUMA YANA ƘARA ARZIƘI, YANKE ZUMUNTA YANA SHAFE ALBARKAR RAYUWA DA JAWO MATSALOLI DA MASIFU IRI IRI, ALLAH KABAMU IKON SADA ZUMUNCI.......*
QUEENBK.








Shiru ne ya wanzu na tsawon daƙiƙu goma, a hankali Asmah ta ɗaga kanta ta kai dubanta gurin ya Abdallah, gani tai ya kama kai alamar kan nashi yana masa ciwo sosai, a ranta tace "ohhh ni Asmah me ya kamata inyi?" wata zuciyar tace "kice masa sannu ya Abdallah, a'a kije ki ɗauko masa magani yasha, a'a a irin wannan ranar ai shi ya kamata ya fara magana, to ai kuma baida lafiya, to ya zanyi?".





Kamar Abdallah yasan
me take tattaunawa da zuciyarta, a hankali ya sauke kansa da idanunsa kan Asmah, sai kuma ya taso a hankali yake takawa har ya isa kujerar da take zaune, hanunsa yasa ya zame gyalan kanta, da hannu ya ɗago haɓarta hakan yasa ta ɗago idanunta suka ko haɗa ido, wani kallo Abdallah yake mata kamar yana so ya haddace fuskarta, ita ma Asmah yau ɗaya taji bata da ɗar kallon ya Abdallah domin yau halalinta ne, sun daɗe suna aika ma juna saƙonni kala kala, can kuma Abdallah ya saketa yana buga kai kamar yana son ya tuna wani abu can kuma yace,





"Baby na zo muje muci abinci" ya faɗa tare da zuwa gurin da su Mahmud suka aje ledojin ya shiga buɗawa, Asmah ta tashi ta yaye mayafin dake jikinta tace,

"Ya Abdallah bari na ɗauko plate" wani kallo ya bita dashi tunda daga kanta har ƙafafuwanta ya saki baki, yadda taga yana kallonta abun har ya bata tsoro tasan dai kayan jikinta sun mata kyau amman batai tunanin zasu ruɗa Abdallah haka ba, ta ƙara cewa "bari in ɗauko",


Sai dai taku ɗaya biyu taji an rike mata hannu an jiyo da ita, da sauri ya Abdallah ya haɗe jikin su waje ɗaya yana sakin wata ajiyar zuciya.





Abun ya bata mamaki yadda har ya bar inda yake zaune ya iso inda take cikin abunda bai fi sakwanni ba, haka ya rungumeta tana jin yadda zuciyar shi ke bugawa da sauri, haka ya matseta kamar wani na shirin ƙwacemasa ita can kamar sabbatu taji yana faɗin,



"Baby na me ke faruwa dani? zuciyata tana bugawa da ƙarfi kamar zata fito daga ƙirjina, ina kuma jin wani daɗi marar misaluwa wanda na rasa dalilinsa, kuma wai munyi aure kin zama matata ko? sai naga abun kamar walƙiya dan Allah baby na kar ki taɓa bari na koman rintsi ban iya rayuwa sai dake" ya faɗa yana ƙara duƙunƙunata.




Asmah ko jikinta kamar an zare mata lakka da ƙyar ta gano muryar ta tace "Ya Abdallah bazan taɓa barin kaba koman rintsi, kuma zuciyarka ta dena bugawa ka kwantar da hankalinka ni matar kace bazan gudu in barka ba".


"Dagaske baza ki taɓa guduwa ki barni ba?".

"Ay bazan taɓa ba, yanzu to sakeni naje na ɗauko mana plate ɗin".


Shiru taji yayi bai ma da alamar sakinta, haka suka tsaya can kuma taji jikinshi ya ƙara mata nauyi a jikinta gashi yana fitar da wani huci mai zafi, dukkan jikin shi ya ɗau zafi da ƙyar ta iya ɗago kanshi gani tayi jijiyotin kanshi sun fito raɗa raɗa ga idanunshi sunyi jajir cikin firgice tace "ya Abdallah me ya same ka?"




ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now